Sashe 3
Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amina cike da matsar hawaye ta nufo hanyar gidan yayin da ita kuma najwa ta tabe baki ta koma wajen sana'arta.
Bayan ya kare ne ta tattaro kwanikan ta taho gida, abinda ya bata mamaki tin daga kofat layinsu ta hango mutane cike kamar ana wani abun.
Cike da mamaki ta taho tana kallon mutanen wajen, yayin da ita ma su din taje kalla, karasowarta kofar gida ne yasa salame fizgota tace"shegiya munafuka mai suffar... Bata karasa ba amina ta fashe da kuka.
Kwanikan hannunta ne suka fadi, cike da mamaki ta kalli amina tace"amma amina kedai anyi munafuka, yanzu ni na watsa miki ruwan mai ko kuma tukuru, haba amina yanzu sharrin da zakimin kenna.
Jin wasu tagwayen maruka taji ya sauka a fuskar ta, batayi koakrin juyawa ba domin tasan marin ko daga ina yake, ba kowa bace zainabu ce mahaifiyarta.
Cikin masifa tace"amma kedai najwa anyi mara mutunci, wallahi wallahi najwa kin kusa kaini inda zan tsine miki ma uban kowa ya huta, cike da faduwar gaba tace"umma kiyi hakuri dan allah wallahi dik abinda suka fada, bata karasa ba umma ta gwabe mata baki take ya hau jini.
Kuka take wiwi da idanunta, wajen su nusaiba taje tace"dan allah nusaiba ba kina a tsaye ba tukuru yazo ya watsa mata mai a fuska, tsaki nusaiba taja tace"malama ba wani tukuru ke kika watsa mata kuma wallahi yanzu haka ma 'yan sanda suna zuwa ki shirya kwatat kanki.
Baya da kamar awa 1,zainabu ta mikawa salame kudi hadi da bata hakuri, nan fa mutane suka taya ta ta basu hakuri, da kyar ta hakura ta mike suka bar wajen sai banbami take.
Bayan da kowa ya fara watsewa tashi tayi daga zaman dirjan din tayi ta goge hawayen ta, jin kanta ne ya mata nauyi yasata dafa katanga ta shiga gidan tana yi tana layi, bata ankara ba taji saukar wata shafdediyar dorina tayi, wata kara ce ta fito ita kanta ma zaka gane cewa a wahale take take ta zube a kasa ba numfashi.
Zainabu dukanta takeyi amma shiru hakan ne yasa ta zuwa ta debo ruwan sama mai sanyi ta watsa mata, a galabaice ta furta, tanayi tana fadin "bani bace na watsa mata mai ba, ba tare da ta saurareta ba ta kara sakar mata wata bulalar, anan ne fa fahad ya shigo,turus yayi ganin najwa bata motsi ita kuma sai dukanta take, da gudu fahad ya taho, cike da bacin rai zainabu tace" kana tako kafarka nan wallahi sai na tsine maka.
MAHAIFIN MU NE SILA
BY
_QUEEN WALEEDAH_
_❤️Official Ashkiey ❤️_
*TAURARIN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION*
From The Team Of
*HAZIK'AI WRITERS*
This Page dedicated to best and end love, sayyada ta tabbas kina rohy na.
*_DEDICATED TO MY FAMILY_*
*PAGE 4*
K'amewa yayi a wajen kamar an sassaka sa, wullar da dorinar tayi sannan ta juya ta huce zuwa dakin ta, zama tayi tana fashewa da kuka ita kadai batare da wani a dakin ba.
A bangaren fahad tana tafiya ya matso kusa da najwa ya fara jijjigata amma shiru, da saurinsa ya debo ruwa ya zuba a hankali ta furzar ds wata nauyayyiyar ajiyar zuciyah,fahad ne ya mikar da ita yana mata sannu, kasa magana tayi ganin haka naga ya saketa ya fice waje.
Bai dade da fita ba ya dawo kamar daga sama yaji ance"FAHAD gabansa ne ya fad'i a fili ya furta "ya ilahyy allah ka tsareni kasa naji alkhairi, ansawa yayi ya nufi dakin da ake kiran sa yasan umma ce.
A zaune ya tarar da ita a hankali tace" fahad ka dauki najwa ka kaita asibiti, kudi ta basa sannan tace yaje, cike da mamaki fahad ya taho ya taso ta ya fita dama ya riga daya samo mai nafef, shiga sukayi, fahad tambaya ce fall ransa amma yasan bashi ds wata amsa, taya akai umma takewa najwa wannan abin amma kuma tana kuka bayan tayi, jin maganar mai nafef ce yasa shi saurin dawowa daga dogon tinanin daya tafi.
Tare suka shiga asibitin, kwantar da ita akayi bayan anyi mata allurai da karin ruwa, wata takadar nurse ta mika masa sannan tace"kaje ka siyo wadan nan magungunan, da toh ya amsa ya fice, gida ya dawo lokacin nabila tana zaue tana fadin"umma wai lafiya naganki dik wani iri batayi mata magana ba ta kyaleta.
Fahad ne ya shigo yace"umma sai kin kara 2000 sun rubuta mata magunguna, batare da tayi magana ba ta mika masa magungunan suka sanan ya fice.
Nabila ce ta ta6e baki tace"wai dama umma waccen banzar kika siyawa magunguna, ashe saboda ita kika zauna kikai shiru, zainabu ce tace"ya isheki haka nabila, kina sassautawa najwa mana, karki manta ita din yayarki ce uwa daya uba daya dan haka ki iya bakinki.
Nabila ce tace"umma tayaya bayan kema baki raga mata ba, cike da kufula tace"wai nabila ni sa'arki ce ina fada kina maimaitawa, kinsan dalilin daya sa nake mata haka, baki sani ba, kuma ki ina son najwa kamar yadda nakesonki kuma ki daina mata abinda kike mata.
Mikewa tayi ta shiga daki bata dade ba ta fito da mayafi sannan tace"ki tashi ki tafi asibitin nan nafada miki, nabilq bata musa ba saboda taga ran umman nasu ya 6aci haka ta mike ta fice bayan ta amshi mayafin hannun umman.
Sallamar da ake ne yasa umma jan hijabi ta nufi kofar gidan, ba kowa bane tukuru ne ya taho shi da wani abokinsa, tana fitowa taji warin giya ya bugi hancintaa,a hankali tace"malam lafiya, cike da gadar yace"ba wajenki muka zo ba wajen 'yarki mukazo, zainabu tace"bata nan na aiketa, tsaki yaja yace"ke dallah karki rainamin hankali yarinyar da baki sonta, baki damu da ita ba, dan haka idan bazaki turo min ita ba ki matsa ni nake na gani nasan idan har tasan nazo to tabbas zakiga abin mamaki.
Runtse idanu tayi tare da zubar da hawaye tace"idan har baka bar kofar gidan nan sai na kira maka hukuma, in ta ambaci hukuma ne yasa shi saduda daga abinda yaso yi na tata iskacinsa.
Gida ta koma ta zauna tana goge hawayen fuskarta, a fili ta furta ya ilahy kasan meke faruwa a kulkun ina rokanka, allah ka yaye min damuwar da take damun najwa da kuma ni kaina, allah ina rokanka ka kawowa najwa miji na gari nasan kaine mai badawa, sannan kuma kaine mai hanawa allah ka kawo min dauki.
Kowa nacewa banason najwa amma ba wanda yasan dalili na na hakan, ba wanda yasa meye a kasa allah ka taimakeni daga haka ta mike tai hanyar dakinta.
A can asibiti kiwa najwa bacci take, yayin da ruwa ke shiga jikinta a hankali, fahad ne zaune yana danna wayarsa, ganin nabila yayi ta shigo tana gyara mayafi, zama tayi sanann tace"sannu yaya fahad ya mai jikin"a hankali yace "alhamdulillah, nabila ce ta kalli najwa take ta bata tausayi, kallon fahad tayi tace" yaya fahad wai meyasa ummah sai tayiwa najwa wani abun sai kaga wataran har kuka takeyi wataran kuma ka ganta ranta dik ba dadi, abya kuwa yaya bada wani abin a kasa ba, kallonta yayi yace"idan ma akwai to ni bansani ba nabila, daga haka sukai shiru suka bar zancen.
Tin shigowar nabila najwa ta tashi amma bata motsa, dik hirar da suke tana jinsu, cike da mamaki take kara jinjina maganar nabila, a ranta tace"ashe dama umma tanajin badadi, to ni me yake damuna haka.
Wani gagarumin hadiri ne ya taso, dole zainabu ta mike ta rufe gidan sannan ta huce, abin mamaki asibitin naga ta nufa dsga can nesa da dakin ta zauna tana hango najwa nacun abinci tana murmushi cikin 'yan uwanta suna dariya cike da farinciki.
Ruwa ne aka fara sa, tinda a daren bai tsaya ba sai wajen 4 na asuba sannan ruwan ya tsaya, yana tsayawa zainabu ta samu ta taho gida, koda ta dawo sallah tayi taje ta mika markade, kafin gari yasha harta fara suyar wainar.
A can asibiti kuwa, likita ne ya shigo bayan ya duba lafiyar ta ne nan ya basu sallama hadi da kuma magunguna da zata na sha bayan wanda fahad ya siyo, karfe 9 suka dawo gida a lokacin zainabu ta rafka tagumi tana jira taga ta inda su najwa zasu bullo mata, kamar daga sama ta ji sallama, daga kanta tayi ta amsa sallamar idsnunta yana kan najwa.
A zuci ta furta ya ilahu, ganin face din ta da tayi fari fat, gashi ta rame, dik haskenta amma wai nabila ta fita haske, saurin amsawa tayi tace"alaikussalam, sannunku da yawwa suka amsa, najwa ce tace"umma ya gida, alhamdulillah ya jikin, a hankali tace"alhamdulillah da sauki umma, daga nan bata kara magana ba, tashi tayi ta nufi dakinta, magungunan ta ajiye tazo zatayi wanke wanke taga anyi, a takaice dai aikin gidan anyi angama sa, zuwa tayi ta tsugunna tace"umma zsnje wajen mai provisions na karbo kayan ki bada kudin jiya, umma ce ta kalleta, cike da tausyi tace"aa kibarshi sai gobe tinda jikin naki ba kwari, kwano ta mika mata tace"gashi nan zauna kici, ke kuma nabila ki maza ki gama ki zo zan aikeki, da to ta amsa, sannan umma ta tashi, cike da mamaki najwa take kallon umman nata.
*MAHAIFIN MU NW SILA*
*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_
QUEEN WALEEDAH
_HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*
✨✨✨✨✨
💪😊
*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*
✨✨✨✨✨
💪😊
https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F
Whatsapp Channel
https://chat.whatsapp.com/ENm6Og7XEUB2iUFDEeu54n
Whatsapp Group
*PAGE 5*