← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 31

Sashe 25

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ce tai murmushi tace"to allah ya amince abbah allah ya kara sutura,murmushi abbah yayi yace'muje kici abinci.
*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 43

Tsaye take a gaban tarin daliban da tsayawa kirgisu ma bata lokaci ne a kalla zasu kai 150 ko ma sufi haka, najwa ce tsaye yayin da cameras suka fara kokarin daukarta,kowa burinsa ya dauketa, najwa cikin wata cool voice ta furta.

Peace be upon you all, and may Allah's blessings be with you.

All praise is due to Almighty Allah who granted us the privilege to gather here today in peace and well-being, at this esteemed institution — a center of learning, discipline, and future leadership. I am deeply honored to speak before this remarkable audience at the prestigious Faculty of Law, a faculty that molds defenders of justice and truth.

I wish to extend my sincere appreciation to the school authorities, the Dean and leadership of this faculty, the respected lecturers, and most importantly, you — the vibrant students with great vision — for inviting me here and for your warm reception.

To be a lawyer is not just a profession; it is a position of trust.
As students of law, you have chosen a noble path — one that demands brilliance, integrity, and above all, the fear of God. Being a lawyer goes far beyond standing in court; it is about impacting lives, protecting the rights of the voiceless, and building a society founded on justice and truth.

Learn with purpose, stand for truth, and speak for the voiceless.
Every law student holds a responsibility to study not just to earn a degree, but to become a tool for societal transformation. Do not turn this profession into a means for selfish gain or injustice. Be courageous defenders of truth — no matter the cost.

There are thousands of people in our country — the poor, the oppressed, the abused — who are waiting for lawyers like you to stand up for them. You are their hope. Your words, your wisdom, your integrity — may be the only thing standing between them and injustice.

So, I urge you today: study with the aim to build legacy.
Be role models. Be leaders. Be listeners with empathy. This profession demands seriousness, not recklessness — because justice is the foundation of peace and national development.

I pray that Allah grants you wisdom, understanding, and honor.
Live with discipline and purpose. Avoid any action that could tarnish your name — because the world is watching you, with high expectations.

Finally, let me congratulate you on your admission and your decision to join the Faculty of Law. You have stepped into a path of great honor and responsibility. Keep pushing forward until you become stars that shine across this nation and beyond.

Thank you for your time. May Allah bless this institution, elevate the Faculty of Law, and grant you success in this life and the hereafter.
Wassalam Alaikum Warahmatullah.
Najwa Suraj Muhammad

Gaba daya wajen taron tafi ne ya krade ko ina, yayin da kowa ke furta yau an fayyace me kalmar lauya take nufi a, wani zakukurin lecturer je ya tashi yana magana cikin harshen hausa,tabbas abinda najwa ta fada haka yake, muna fatan zakuyi aiki da shi kuma zakuyi aiki da basira,a yau dani da sauran malamai, muna muku addu'ar fatan samun nasara a jarabawarku,fatan ubangiji ya baku nasara,daga nan kuma aka rufe taro da addu'a.

Gaba daya fitowa sukayi daga hall din yayin da suka zagaye najwa suna kara gaisawa tare da jinjina mata,wani dalibi ne ya doso wajenta yace"najwa kije inji dean,kallonsa tayi tace"dean kuma wata kawarta ta kalla tace"deejah zo ki rakani, daganan suka fito suka nufi office din.

Knocking take tafi minti 1 sannan yace"shigo tare da deejah suka shiga, kallonta yayi sai kuma ya kauda kai yace"gaskia najwa suraj Muhammad kin burgeni kedin 'yar gidam malam suraj Muhammad ne dayake unguwar rigasa,najwa ce ta gyada kai tace"ea ni ce,wani list ya mika mata yace"daga yau zuwa gobe dik wanda bai baki ba ki masa cancelled, najwa ce tace"toh sir insha allahu daga nan suka tashi yana me kallonta yana murmushi.

Tana fitowa suka rabu da deejah ta koma can parking space, wayarta ce ke kara zaro ta tayi tana kallon screen din wayar,picking tayi tace"gloria yadai,banji mai gloria ta fada ba kawai naji ta katse ta shiga motar, wasu yammata ne suka taho suna kwala mata kira dole ta tsaya tana sauraren zuwansu.

Daya daga cikinsu ce ta karaso,kallonta tayi ta kalli ta kusa da ita tace"ke ku kawo paper dinku ta gani ta muku tick idan ba haka ba kuwa kunsan halin wannan mutumin, wata dariya dayar ta babbaka tace"ohhh wai ita ga me kokari ko,to ni bazan bada ba dik abinda zaiyi sai dai yayi amma bazan bawa mai kan kwakwa paper ta ba,najwa murmushi tayi ta kar6i na wadda suka miko mata ta juya ta shiga motarta tana kokarin tada ta,daga nan ta fice ta barsu ta bar school din.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 44

Motoci 4 ne sukai parking a parking space din dayake tsakar gidan,wani kamshin turare ne ya ziyarce ni a lokacin da aka bude murfin motar,tsayawa nayi ina karewa halittar wajen kallo,wani saurayi ne ya fito sanye yake da suit ash wadda ta karbi jikinsa, sai shoes black wand ayake daukar idon mutane.

Sannu a hankali yake tafiya da sauri nasha gabansa,yayin da sumar kansa wadda ba dayawa bace ta gama taruwa a kan nasa,sai kuma wata kasumba wadda bai riga daya gama aske ta ba ya barta ta kwamta luff a kan kumatunsa.

Falon ya shiga da sallama a bakinsa yana yi yana karewa falon kallo, daya daga kujerun falon ya samu waje ya zauna jin fakon shiru,zaune yake har yanzu falon shiru shi kuma yaki mikewa daga zaunen da yake,najwa ce ta shigo da waya a kunnenta tana fadin"ohh kana bakin gate, ok to ka shigo yanzu zan fito,katsewa tayi sam hankalinta ya kada ta tafi upstairs ta haye ta fara taka matattakalar bene.

Yayin da safwaan sai da ya bari ta huce yabi bayanta, dakinsa ya shiga ya barta direct bedroom yayi a cikin shekaru 2 an chanja komai na dakin daga marron zuwa blue and white wanda yayi matukar yiwa dakin kyau, shi kansa dakin ya burgesa,bai kalli toilet ba ya dauki kujera ya dasa bakin windown dakinsa yana kallon yadda zai ga ita kanta najwa.

Yana nan zaune harta shiga ta fito,kallonta yake yayin daya shiga motarta ta tada ta fice daga gidan,a ransa yace"lallae wannan yarinyar ta cika yawo amma zanyi maganinta, dsn naga idan har ba auren aka daura ba bazata barni na huta da cecekuce ba.

Bayan awa 2

Kowa zaune yake a falon, sakina safna umma da samaiha dikansu da mazajensu, yayin da aka saka safwaan a tsakiya ana zolayarsa, ko kallonsu bai ba,najwa ce ta shigo da sallama, gaba daya hankalinta yana kan dining area,ganin ba abinda aka shirya yasa ta furta"ohhh umma kin kyauta da baki jera komai ba, naje wajen Gloria kar6ar aikin da mukayi dazu kafin na tafi speech, batare data juyo ba,safna ce tace"najwa ya akai na ganki a social media,cigaba tayi da gyarawa tace"oh aunty safna ba dole ki ganni ba,ni ai bansan zaki dauki hoto ba da bazan je ba.

Umma wai ina yah safwaan ko bai dawo bane,rayyan ne yace"wane safwaan kuma, abdallah ne yace"safwaan har nawa kuma bayan gashi a zaunr yana kallonki,najwa ce ta murmushi tace"aa yaya abdallah kaima ka cika abin dariya ya safwaan ne zai dawo bani da labari,wayarta ce ta fara ruri,shiryawa take a haka dauki wayar tana fadin ka shigo ina aiki ne,jin wata kakkausar muryar da bazata ta6a mantawa ba taji yace"ba inda zakije har maza nawa zaki gayyato mana gida stupid.

Take hanjin cikinta ya kada, hankali ta juyo tana kallon sa ganin kallon da yake aika mata ne yasata sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta,mikewa yayi yazo dab da ita yayin da umma ta mike ta bar wajen tana murmushi a ranta,najwa jiki na tsuma ta fara ja da baya, har sai da ta tokare bayanta a jikin dining din.

Safwaan ke kallonta yayin daya shagala da karewa halittarta kallo,kallonta yake wanda a cikin shekaru 2 ta zama wata beautiful, wadda bai zata ba, gata ta zama cikakkiyar budurwa, wadda take fitar da wani sihirtacen kamshi a jikinta, najwa ce ta durkushe yayin da wayar ta fara ruri, tana shirin dauka ya kar6e wayar, a handsfree ya sakata yayin da mai magana yace"class captain na iso,wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yace" kije ki kar6i abinds zaki kar6a.

Ai da sauri ta mike har tana tuntube,yayin daya juyo ransa a hade yana kallonsu, dik da sunso yi masa tsiya amma haka ya huce yabi bayan umma zuwa dakinta,sai da suka tabbatar da cewa ya tafi sannan suka fashe da dariya kasancewar sun san halinsa bayasan dariya.

Najwa a ranta tafiya tati cike da tsoro domin ita bata ta6a jin tsoron yah safwaan ba sai yau , domin kuwa ya mata wani kwarjini wanda ita kadai ne ta gani ko su safna sun gani ne ko basu gani ba ita dai ta gani.
Chapter 25 · 0% Book details