← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nabila ce tace"aunty najwa me kika gani,oh wai dan talaucin da muke fama dashi,yanzu bamu da kudi kuma umma tin bayan tafiyarki ta daina dorawa kowa tallah,yanzu haka ina ss1 ne a makarantar secondary ta bayan gari.

Aunty najwa yanzu haka bashi ake bin umma a gidan maigari, amma allah yasa ma ta bata kindirmon,najwa ce tace"nawane kudin.

Nabilace tace"dubu biyar,handbag din ta ta dago ta zaro dubu biyar ta mika mata tace"nabila ki bata idan munje kice inji umma,nabila tsayawa tayi yayin da hawaye ke faman yoyo a kumatunta.

Aunty najwa kece kika koma haka,aunty najwa kalli rigarki inda a film nake ganin ta,sai kuma ta kalli jikinta tace"aunty nabila miyi sauri ko an kusa sallah, yayin da al'ummar wannan gari ke kallon najwa, dayawa suna tarar ta suna cewa wacece wannan amma nabila sai tace musu 'yayarta ce tazo daga birni,kuma cikinsu ba wanda ya kawo najwa ce.

BAYAN AWA 4 (After Four Hour)

Zainabu ce tace"aminatu nagode nagode sosai allah ubangiji ya biyaku da gidan aljannar firdausi,abbah muna godiya tabbas kun ceci rayuwar najwa kuma indai ni ce kuje na bar muku najwa ku zaba mata dik abinda kukaga ya dace da ita,kuka zainabu take yayin da umma ita ma ke kukan tana kara bata hakuri.

Zainabu ce tace"a rayuwa gambo ya cuceni amma komai ya faru yana da dalili gashi har kun karya sihirin dayake jikin ta,nagode kwarai da gaske allah ya saka muku da alkhairi, abbah ne yace"ki daina kuka kallon najwa yayi yace"tashi kuje,ai da sauri taja hannun nabila suka mike, yayin da safwaan shima ya bi bayansu.

A kofar gida suka tsaya,najwa ce tace"nabila ina ne wajen aikin fahad,nabila ce tace"ba anan bane ciki ne sosai kuma da tazara gaskia sai an huce kauyen nan,kallon safwaan tayi wanda wasu samari suka tsaya kusa dashi suna masa hira,ganin sun juya zasu shiga gari yasata fadin"yah safwaan,juyowa yayi yana kallonta yace"menene.

Dan turo baki tayi tace"dan allah ka bani key zanje wajen yayana kuma ba a kauyen yake ba,safwaan ne ya kalleta yace"najwa ki kula kinji,dan allah banda tukin ganganci kinsan ina sonki ko,saurin kau da kai tayi tana kallon nabila wadda take dariya.

Ganin haka yasa shi fadin"kunga kunsan menene ku jirani,wajen nabila yaje yace"kinga yanzu dai ki kula da ita kinji dan nasan kin fita sanin kauyen nan ya yake,dariya nabila tayi tace"to ya safwaan insha allahu.

Key din ta karba sai da shigar da nabila sannan nabila tace"wai yanzu aunty wannan katuwar motar zaki tuka,aunty a ina kika iya tuki,najwa murmushi tayi kawai taiwa motar key,harzasu fice safwaan yace"tsaya budewa yayi ya shiga uace"kafata kafarku dan baza kijamin fada wajen abbah ba.

Tafiya suke nabila sai surutu take zuba musu kamar an kunna radio,yayin da safwaan ya bide baki yana ta dariya,najwa ce tace"ohh kallesa kamar ba shi bane dazu ya hade rai.
*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 49

Zainabu ce tace"a yanzu haka mahaifin najwa yana kano.

Abbah ne yace"nan nan kano, umma ce tace"eh ni da zaka bi tatawa wallahi da an kyalesa da magnaar nan,baisan shanta ba, cinta, suturar ta,har yayi kokarin maida ta rabi dabba rabi mutum, to kuwa meye amfanin zuwa wajen sa yanzu.

Umma ce ta dafa ta tace"kiyi hakuri mana zainabu komai yayi zafi maganinsa allah kuma kamar yadda abbah ya fada za aje wajen sa a nemarwa safwaan auren najwa,saboda bata da kamar shi, sannann karki la'akari da wadan nan abubuwan,dan adam baya hucewa kaddarar sa zainabu.

Zainabu ce tace"to shikenan allah ubangiji ya taimaka kuma ya kaimu lokacin biki lafiya,umma ce tace"ameen hadi da abbah.

Umma ce ta mike tace"ga magariba nayi bara muje wajen mai gari na gabatar daku sai ya baku gida ko,daki ta shiga dakko hijabi, yayin da aminatu ta gyara mayafun kanta tana fadin"abbah muje to,sai muyiwa mai gari bayani shima.

Tin daga nesa najwa ta hangosa a sama yana kwaba kasa yana zubawa akan wani rufin kwano,masha allah ya girma tinda gashi ya zama saurayi, ga wani tsawo da yayi amma sai dai har yanzu kyansa yana nan bai disashe ba.

Nabila ce ta karasa wajen sa yayin da yayi tsalle ya sakko daga cikin motar yana fadin"nabila waya kawo ki nan,nabila murmushi tayi tace"yah fahad kalla kaga wacece tazo.

Maimakon ta kyalesa jan hannunsa tayi suka fara tafiya,dab da najwa ya tsaya yana kare mata kallo,a wannan lokacin kwakwalarsa na gaya masa najwa ce,yayin da zuciyar sa ke wasiwasi akan hakan,bai tsinkaye da ita ba har sai da ta furfa fahad yayin da hawaye ke kokarin fita daga idanunta.

Da gudu ta karasa ta fada jikinsa yayin d shima kukan yake,nabila ma kusa dasu taje ta tsaya tana kuka ita ma,safwaan kam tsayawa yayi yana kara kallon yaran,kamar fahad ace yanzu yana wannan aikin shi da ya dace ace yana makarantar gaba da secondary, tabbas mahaifin su ya cuce su.

*************

Zainabu ce ta gabatar da su wajen mai gari,mai gari kuwa ganin za a samu abin arziki ne yasa shi sakin baki hadi da yi masa surutu,sunan nan zaune motarsu safwaan ta karaso wajen mai gari kasancewar sunje can ance tayo nan.

Gaba daya fitowa sukayi kallo daya zakawa face din su kasan sunsha kuka abinsu,safwaan najwa har gaban mai gari suka zo suka tsugunna hadi da gaishe sa,mai gari ya dubesa yace"oh to to kune yaran su alhaji kenan,to masha allah haka akeso.

Safwaan ne ya dubi abba sai kuma ya dubi mai gari yace"ranka ya dade karkace baka gane wannan din ba,mai gari ne yace"tayaya zan ganeta,ni da na dauka tare kuka zo.

Safwaan ne yace"tare muka zo amma kuma da ai anan take.

Maigari ne ya kalli naiwa ya jinjina kai yace"yaro ban ganeta ba kayi min bayani dallah dallah.

Safwaan zaiyi magana najwa ce tace"ranka ya dade najwa ce,a lokacin kowa ya bude yana kara kallonta wanda bai kalleta da kyau ba ya kara kallonta.

Maigari ne yace"najwa, najwa dai wadda ta zama kura,ashe dama. Baki mutu ba yarinya,to kuma har yanzu kina zama kurar ko kuwa yanzu kin daina.

Najwa ce tace"na daina yanzu allah ubangiji ya bani lafiya kuma alhamdulillah ta sanadin abbah da umma da kuma yaya safwaan na samu lafiya.

Mai gari ne ya kalli najwa ya kalli liman yace"mai liman ina galadima gaskiyarku wallahi,da kukace mu kyale zainabu karmu koreta dik daran dadewa zata dawo,gashi kuwa ta dawo,kai allah abin godiya.

Nan fa labari ya cika gari wai najwa ta dawo ta kuma samu lafiya kacin ka ankara tini mutane sun cika bakin fada kowa ka gani najwa yake kallo wadda ta sunkuyar da kanta tana wasa da wayarta kirar iPhone.

Bayan sallar isha'i
Umma da abba ne zaune gidan da aka basu su kwana, sai safwaan wanda yana daya dakin, dakin da gado da kuma fanka tanayi.

Umma ce tace"gaskia na tausayawa zainabu abbah,da sauran yaran kallo daya ya isa ka gane cewa suna cikin talauci,abbah ne yace"eaa ai sai dai mugode allah kuma ya kara masa budina alkhairri.

Najwa ce jikin umma yayin da umma sai nan da nan take da najwa,ga wata sabuwar hira da suka dora tana kara basu labarin wahalar da tasha a lokacin da tana kura,fahad nabila kuwa baki yaki rufuwa yayin da fahad din ke cin danwaken da umma tayi musu bayan dawowa daga fadar mai gari.

Nabila ce tace"umma na manta aunty najwa fa ta biya miki bashin gidan mai gari,zainabu ce tace"najwa ina kika samu kudi haka,murmushi tayi tace"umma ina kasuwanci ne shisa,umma adduva ta fara zuba mata ita da su abbah.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮
🌼🌼🌼LAST CHAPTER
💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 50

Washe gari karfe 11abbah umma da kuma safwaan suka dauki hanyar komawa kaduna, inda abbah yace"najwa bazata dawo ba har sai an daura aurenta sannan zata dawo,dik da auren bazai huce sati 3 ba tinda dama can an tsayar da magana, ga kuma kayan lefe.

Nabilace ta fito daga wanka wata tattararriyar atamfarta ta dakko zata saka,najwa ce tace"ki ajiye wannan bara na baki wata ataamfa,najwa akwatinta ta bude,wata atamfa ce fara sai ratsin marron, doguwar riga dinkin umbrella ta bata tace saka muga,tana sakawa rigar tayi mata daidai sai dai kasan na sharar kasa,najwa ce tace"kai nabila wai ina tsawon nan dana sanki dashi,murmushi kawai nabila tayi tana tattare rigar.

Umma ce ta fito tace"yawwa nabila zo kije ki amso min taliya sai mu dafa,wayar najwa ce tai kara hakan yasata dagawa ganin sunan Gloria.

Bata dade ba ta kashe wayar tana fadin umma bara muje sai mu amso,umma ce ta dubi atamfar jikin nabila tace"masha allah aikuwa gaki nan atamfaar ta miki kyau,murmushi nabila tayi,tana koakrin kar6ar kudin,najwa ce tace"karki kar6a mana da kudi a wajena.

Fitowa sukai yayin da kowa ya ganta manya da yara zaka ga suna daga mata hannu suna kiran najwa,haka har suka karasa shagon provision, najwa siyayya tayi musu sosai sanann tace"akai musu gida, daga nan ta dubi nabila tace.

"nabila nikam ina kulu.

Nabila ce tace" aunty tayi aure baiwar allah, a wajen haihuwa alah ya dauki ranta,kasancewar ba asibiti a kusa kuma ga hanyar bata da kyau,ai aunty nayi alkawari dik irin wahalar da zansha insha allahu sai na zama likita, domin mutuwar kulu ta tabani.

Cike da jimami najwa tace"nabila ina tare dake wajen cika wannan burin naki, kuma. Insha allahu zan tsaya miki, daga nan suka juya suka shiga gari.

****************
Chapter 28 · 0% Book details