← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 31

Sashe 15

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu ya shawo kan motar yana danna horn, mai gadi da sauri ya bude masa yana masa barka da zuwa amma bai samu ya amsa ba,cikin gidan ya shiga, habiba ya fara gani a falo, amma bai mata magana ba yaci gaba da hawa step na dakin aminatu,a falonta ya ganta tana rike da hoton safwan ta zabga tagumi.

Abba ne ya karasa bayan ya dauje mata hoton ne ya kalleta, sanann ya yajata ya zuwa dakin ta, bayan ya sawa kofar key yace"albishirinki, ganin fuskarsa wasai yasata fadin"goro abban samaiha,murmushi yayi sai da ya kalli ko ina sannanyace"kinsan da cewa safwaan ya kubuta, da sauri ta kalles tace"kamar ya abbah, kana nufin ya fita daga bala'in muttaka.

Abba ne yayi murmushi yace"tabbas domin indai ya dawo ba tare da sanin wani ba, maganin dana hada masa, indai yayi amfani da shi yadda akeyi, to insha allahu rabby allah zai karesa,kuma ba abinds muttaka ya isa yayi masa,umma kasa tayi take wani zazzafan kuka ya kwace mata, cikin kukan takewa allah godiya hadi da kirari,domin tabbas tasan ikon allah ne ya sa shi ku6uta, bayan muttaka yace"bazai ta6a ku6uta ba.

Abba da kyar ya lallasheta, nan fabtace"sai ankira saa, abba ne ya kalleta yace"karki damu nan ya bata labarin yadda sukayi dashi,sanann abba ya kalleta yace"sai ko eufe bakinki kar wanda yaji wannan maganar har sai ya gama amfani da maganin, sanann ba wanda zai san ya dawo, umma ce tace"insha allah ba wanda zai sani, dagani sai kai abba, daga haka ya bude kofar dakin nata.

Turus yayi ganin habiba tana kokarin zama,kallonsa tayi shima ya juya ya kalli aminatu da take zaune, saurin kullo kofar yayi yace"me ya shigo dake wannan falon, shiru tayi tana kallonsa, can kuma tace"wallahi sam alhaji ka bani kunya, ashe dama a ranar kwana na wajen aminatu kake zuwa, kana cin amana ta, amma sam baka min adalci ba, tsayawa yayi yana mai kara kallona.

Abba bai biye mata ba ya huce yabar falon, domin sai yanzu hankalinsa ya kwanta da bataji me yaje ya gayawa aminatu ba,a ransa ya furta"lalle habibah baki da hankali,ke abinds ya dameki kenan, dakinsa ya shiga yana kallon dakin sai kuma ya samu wata kujera 1 sitter ya zauna yana mai jan numfashi.

Habiba ce ta kutso kai ta kallesa tace"wallahi surajo gidan mu zan tafi na barku kai da waccen shashashar da kakeso, bai kalleta ba, bare tasa ran samun amsa daga wajen sa,juyawa tayi a fusace ta bar wajen tana kuka wiwi,mayafinta ta zara ta bar gidan, yayin da shi kuma bai hanata ba, domin shidai rigimar habiba ta ishesa.

Tana fita ya furzar da iska yace"sai kin dawo allah ya rakataki gona, daga nan ya juya ya kalli Agogon wayarsa, saurin mikewa yayi yana kallon lokaci domin ya tina zaije masalaci tafsiri, daga nan ya shige toilet.

💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮

Nabila ce ta kawarta 'yar mai gari suke tafiya kowacce da bokiti a hannunta,kulu ce tace"ohh ni nabila kinga wasa wasa har anyi sati daya da tafiyar najwa yayarki ko,nabila ce ta kalleta tace"to ya za ayi ko wane bawa yana da kalar tasa kaddarar mu kuma tamu kaddarar kenan.

Da haka suka tafi har rafi,ruwan suka debo suka taho suna tafe suna hira sannu a hankali har suka iso mararraba daga nan kowacce ta kama hanyar gidansu,nabila tafiya take tana tinanin najwa da irin abinda tayi mata,da sallama ta shiga gidan umma ce zaune tana jan carbi da alama salla ta idar.

Tana ajiye ruwan ta kalli umma, umma ce tace"yawwa zoki kar6a kije wajen mamman ki amso mana shinkafa sai mu dafa tinda fahad baya nan yaje kasuwa,nabilace tace"tohm umma haka ta kar6a ta tafi.

💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮

Sakina ce ta fito daga kitchen, gidan shiru ba kowa, wayarta ce ke ruri hakan yasa ta dagawa tana kallon screen din ganin an saka labiba ne yasata saurin dagawa tana fadin ai kin kyauta, yqnzu labiba sati nawa da auren nan amma sai yau zaki kirani, dama ai jira nake naga randa zaki kirani, banji mai labiba tace ba sai ji nayi sakina tace"dan allah ai kkuwa bara baby ya dawo domin ayau sai naje nayi register, kinsan yadda nake addu'ah kuwa.

Ranann munje dubawa ba a kafe ba, amma bara na duba whatsapp group yanzunn nan kuwa ba tare da 6ata lokaci ba, sallama sukayi tana katsewa ta shiga whatsapp nan taga Sakamakon exam din ta wtih upper class, wani tsalle tayi bata san lokacin data mike ta fara rawa ba har da juyi.

Lokaci guda take son kiran safna, zama tayi ta danna mata kira,sai da ta kusa katsewa sanann ta daga, murya can kasa tace"hello sakina, turus tayi tace"safna lafiya kike ne,safna cike da tsiwa tace"lafiya da ba lafiya ba ai bazan daga wayarba, kuma ke tsaya ina ruwanki dani har kike tambayar lafiya, aikin banza aikin wofi kiji da kanki na, banza kawai, kittt ta kashe wayar yayin da sakina tai murmushi tace"ohhh safna har yanzu bazakiyi dana sani ba, har yanzu abin naki ma bai chanja ba.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 26

Karfe 5:30 na yamma motarsu ta saukaa tasha a cikin garin kano, nafef ya tare suka shiga, yadanyi tafiya mai nisa daidai wani dan karamin gida suka tsaya, sallamar me nafef din yayi sanann ya juya ya sallami mai nafef din,
Kallon sa najwa tayi tace"safwaaan yadai ina ne nan kuma,safwaan ne yayi murmushi yace"gidanmu ne gidan abbah ne,wani karamin gida ya kalla yace"najwa shiga kice ana sallama da mai gidan,kallonsa tayi ta kalli kanta sai a lokacin taji kunyar kanta.

Murmushi safwaan yayi kawai ya karasa bakin kofar gidan ya fara knocking,shiru can kuma sai yaji ance ana zuwa, wani dattijo ne ya fito yana kallon yaron, da kyar tsohon ya dubesa yace"aa karka ce min dai Muhammadu ne, safwaan ne yayi murmushi yace"eaa wallahi baba bala,baba bala ne yace"aa to kace yau ka leko gidan naku, bara to na miko maka mukullin,shiga yayi bai dade ba ya fito yana mika masa mukullin, safwaan cike da farimciki ya kar6a yana bashi wasu kudade.

Baba bala addu'ah yayi ta zubawa safwaan daga nan kuma ya koma,safwaan ne ya kalli najwa yace"ke sai yanzu zakiji kunyar kanki, zatayi magana ta fara jin canji a jikinta, cikin sauri tace"safwaan kai sauri ka bude,duhu ya fara yi,kokarin budewa yake, sai da ya bude suka shiga sanann ya rufe, kallonta yayi yana fadin"lafiya kike najwa, kokarin matsowa yakeyi amma najwa ta dakatar dashi, wani irin kaikaiyi takeji, a lokacin ta fara soshe soshe,wani kara ta saki a lokaci guda ta rikide ta koma bakar kura.

Safwaan zabura yayi yana kara kallon ta, cikin yanayi mara dadi ya kalli kurar,yayin da kurar take fitar da wani gurnani mara dadin saurare,safwaan ne ya karasa ya bude gidan, yana dari dari da wannan kurar data bayyana a bayansa,yana budewa yazo ya shiga,kurar ce ta biyosa tana fitar da wani gurnani mara dadin saurare,shiga tayi har lokacin a tsorace yake, zama yayi yana kallon kurar,kurar ce ta matso kusa da shi tana fitar da gurnani, matsowa tayi tana kara kallon sa, ganin a tsorace yake yasata koma can bayan wata kujera ta zauna.

Sun dau tsawon mintuna a haka sannan ya lura da kurar ta rufe ido, a hankali ya tashi ya shiga wani bedroom tare da saka masa key,yana shiga ya zauna yana jimamin yadda najwa kyakkyawa ta chanja daga ita zuwa kura,sai kuma ya tashi ya tafi bandaki.

💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮

Aminatu ce ta fito daga dakin ta, jin dakin shiru hakan yasa ta kara fitowa, ba kowa dan haka ta zauna tana kallon television fuskar nan dauke da farin ciki,jin ana kiraye kirayen sallar maagariba yasa ta mikewa ta huce zuwa dakin nata.

Tana idar da sallar magariban ta fito dakin safwaan ta shiga,nan ta fara gyarawa tana kara goge wa,kallon hotunan da yake zanawa tayi, zama tayi tana kara kallon hoton, lokaci guda ta tsinci kanta da kallon zanen hadi da murmushi, ta jima a dakin sannan ta fito ta shiga kitchen domin hadawa abbah tea din sa.

Tana fitowa ta shiga dakin abba,a zaune ta gansa a kan sallaya yana karatun alkur'ani mai girma, ajiye wa tayi ta koma gefe ta zauna, tana hangen hangen habiba ko zata ganta amma shiru, sai da ya kai ayar karshe sanann ya ajiye alkur'anin ya dubeta yace"ameenatuh, murmushi tayi tace"naaam abbah,flask din shayin ta dakko tana mai tsiyaya masa ruwan shayin, dayake fitar da wani irin kamshi.

Abba ne ya kalli Agogon hannunsa yace"nikam kinga yaron nan shiru, Ameenatu ce tace"ea wallahi nima tinaninsa nake,sai kuma ya kalli wayar sa yace"bara na kira numbern daya kirani dazu, ya dauki wayan yana kokarjn kiran nasa.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️🍀☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

Gaba daya wani katon falo ne, kowa zaka ganshi zaune, yqyin da kowa sanye yake da kaya mabanbanta,can gefe daya idanu na suka sauka akan alhaji gambo ya harde a kujerun dakin.

Wani mai kaya bakake ne ya mike yace"za a gabatar da shugaban kungiya a yau, sannan kuma za a yi nadin shugabancin sa wani satin, akwai sharuda da ka'idoji kamar yadda wannan kungiya tamu ta tana da, alhaji gambo ka sani kaine shigaba kaine wanda zaka jagorance mu, amma kafin nan bara mu fadi, kaidoji kamar yadda suke a littafin mu na shugabanci,wani katon littafi ne ya bayyana a gaban mai bakaken kayan.
Chapter 15 · 0% Book details