← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 31

Sashe 26

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cinyar umma ya zauna yana karewa wayar kallo,gaba daya wayar iya whatsapp ne sai Instagram wanda dika ba wamda ya shiga,umma ya kalla yace"umma dan allah ayi a tsayar da magana tinda na dawo,umma ce tace"haba safwaan kasan hakan bazai ta6a yiwuwa ba, dole sai anje anga iyayen ta,an tambayesu idan su zsu yadda,karka manta lokacin da aka hada auren nan ba wani nata a kusa, dan haka ya zuwa yanzu sai dai mu je zuwa kauyen su.

Safwaan ne yace"umma yaushe zamuje dan allah,kallonsa umma tayi tace"zamuje amma najwa zasu fara exam sai allah yayi idan sun gama zamu halarta,sai zancen bake shop dinta wanda take gudanarwa,abbah ne ya bude mata kuma ba laifi mutane suna so,shidai baiyi magana ba kawai ya rufe ido yana shafa ciki.
*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 44

Motoci 4 ne sukai parking a parking space din dayake tsakar gidan,wani kamshin turare ne ya ziyarce ni a lokacin da aka bude murfin motar,tsayawa nayi ina karewa halittar wajen kallo,wani saurayi ne ya fito sanye yake da suit ash wadda ta karbi jikinsa, sai shoes black wand ayake daukar idon mutane.

Sannu a hankali yake tafiya da sauri nasha gabansa,yayin da sumar kansa wadda ba dayawa bace ta gama taruwa a kan nasa,sai kuma wata kasumba wadda bai riga daya gama aske ta ba ya barta ta kwamta luff a kan kumatunsa.

Falon ya shiga da sallama a bakinsa yana yi yana karewa falon kallo, daya daga kujerun falon ya samu waje ya zauna jin fakon shiru,zaune yake har yanzu falon shiru shi kuma yaki mikewa daga zaunen da yake,najwa ce ta shigo da waya a kunnenta tana fadin"ohh kana bakin gate, ok to ka shigo yanzu zan fito,katsewa tayi sam hankalinta ya kada ta tafi upstairs ta haye ta fara taka matattakalar bene.

Yayin da safwaan sai da ya bari ta huce yabi bayanta, dakinsa ya shiga ya barta direct bedroom yayi a cikin shekaru 2 an chanja komai na dakin daga marron zuwa blue and white wanda yayi matukar yiwa dakin kyau, shi kansa dakin ya burgesa,bai kalli toilet ba ya dauki kujera ya dasa bakin windown dakinsa yana kallon yadda zai ga ita kanta najwa.

Yana nan zaune harta shiga ta fito,kallonta yake yayin daya shiga motarta ta tada ta fice daga gidan,a ransa yace"lallae wannan yarinyar ta cika yawo amma zanyi maganinta, dsn naga idan har ba auren aka daura ba bazata barni na huta da cecekuce ba.

Bayan awa 2

Kowa zaune yake a falon, sakina safna umma da samaiha dikansu da mazajensu, yayin da aka saka safwaan a tsakiya ana zolayarsa, ko kallonsu bai ba,najwa ce ta shigo da sallama, gaba daya hankalinta yana kan dining area,ganin ba abinda aka shirya yasa ta furta"ohhh umma kin kyauta da baki jera komai ba, naje wajen Gloria kar6ar aikin da mukayi dazu kafin na tafi speech, batare data juyo ba,safna ce tace"najwa ya akai na ganki a social media,cigaba tayi da gyarawa tace"oh aunty safna ba dole ki ganni ba,ni ai bansan zaki dauki hoto ba da bazan je ba.

Umma wai ina yah safwaan ko bai dawo bane,rayyan ne yace"wane safwaan kuma, abdallah ne yace"safwaan har nawa kuma bayan gashi a zaunr yana kallonki,najwa ce ta murmushi tace"aa yaya abdallah kaima ka cika abin dariya ya safwaan ne zai dawo bani da labari,wayarta ce ta fara ruri,shiryawa take a haka dauki wayar tana fadin ka shigo ina aiki ne,jin wata kakkausar muryar da bazata ta6a mantawa ba taji yace"ba inda zakije har maza nawa zaki gayyato mana gida stupid.

Take hanjin cikinta ya kada, hankali ta juyo tana kallon sa ganin kallon da yake aika mata ne yasata sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta,mikewa yayi yazo dab da ita yayin da umma ta mike ta bar wajen tana murmushi a ranta,najwa jiki na tsuma ta fara ja da baya, har sai da ta tokare bayanta a jikin dining din.

Safwaan ke kallonta yayin daya shagala da karewa halittarta kallo,kallonta yake wanda a cikin shekaru 2 ta zama wata beautiful, wadda bai zata ba, gata ta zama cikakkiyar budurwa, wadda take fitar da wani sihirtacen kamshi a jikinta, najwa ce ta durkushe yayin da wayar ta fara ruri, tana shirin dauka ya kar6e wayar, a handsfree ya sakata yayin da mai magana yace"class captain na iso,wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke yace" kije ki kar6i abinds zaki kar6a.

Ai da sauri ta mike har tana tuntube,yayin daya juyo ransa a hade yana kallonsu, dik da sunso yi masa tsiya amma haka ya huce yabi bayan umma zuwa dakinta,sai da suka tabbatar da cewa ya tafi sannan suka fashe da dariya kasancewar sun san halinsa bayasan dariya.

Najwa a ranta tafiya tati cike da tsoro domin ita bata ta6a jin tsoron yah safwaan ba sai yau , domin kuwa ya mata wani kwarjini wanda ita kadai ne ta gani ko su safna sun gani ne ko basu gani ba ita dai ta gani.

A cinyar umma ya zauna yana karewa wayar kallo,gaba daya wayar iya whatsapp ne sai Instagram wanda dika ba wamda ya shiga,umma ya kalla yace"umma dan allah ayi a tsayar da magana tinda na dawo,umma ce tace"haba safwaan kasan hakan bazai ta6a yiwuwa ba, dole sai anje anga iyayen ta,an tambayesu idan su zsu yadda,karka manta lokacin da aka hada auren nan ba wani nata a kusa, dan haka ya zuwa yanzu sai dai mu je zuwa kauyen su.

Safwaan ne yace"umma yaushe zamuje dan allah,kallonsa umma tayi tace"zamuje amma najwa zasu fara exam sai allah yayi idan sun gama zamu halarta,sai zancen bake shop dinta wanda take gudanarwa,abbah ne ya bude mata kuma ba laifi mutane suna so,shidai baiyi magana ba kawai ya rufe ido yana shafa ciki.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 46

Najwa ce ta shigo da katuwar leda ba kowa a falon hakan yasa ta ajiyeta anan ta fara kwala kiran umma,umma na kitchen ta fito tana fadin"to 'yar sarkin kira gani menene kuma,najwa ce ta karasa wajen umma hadi da rungumeta tana fadin"kai umma kuma idan baki ganni ba kuma kiyi ta kewata kuma yanzu nazo amma shi ne kike cewa na fiye zance kai umma.

Umma ce ta shafa bayanta sannan tace"yanzu dai dauke ledan nan ki huce dakinki da ita ki fito kiyi dinner,najwa ce ta janye jikinta hadi da dsukar ledan tayi dakinta.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya a wannan bangarori inda a yau ne samaiha ta koma kasar Qatar,tare da yaranta su dika,shi kuma safwaan a yau ne suka koma wani katon gida dayake nan cikin unguwar tasu.

Kallon gidan nake a kalla yayi biyun gidan nasu,ga kyau ga kuma uwa uba fasalin ginin na zamani,part 2 ne a cikin gidan,abbah sai sanya masa albarka yake kasancewar yanzu shi ne shugaba a companyn na abba shi yayi retire ya dora dansa safwaan.

Safwaan ne kwance a cikin dakin daya za6a ya kasance dakinsa dan karamin daki ne wanda yake dauke da ash din furniture,komai na dskin ya kasance ash colour ne sai ratsi ratsin fari kadan kadan,lumshe idanunsa yayi yana tuno rayuwar da yayi a baya, da yadda abbah ya rikesa dik da bai haifesa,a fili ya furta bani da abinda zan saka maka dashi abbah sai dai na maka fatan ubangiji yaja da ranka.

Knocking din da ake ne yasa shi fadin
"Shigo

Najwa ce ta shigo dauke da tray a hannunta sama fkask din shayi ne sai kuma kana nan kofuna.

Da sallama ta karasa shigowa tana fadin
" yah safwaan ina wuni,bai kalleta ba yace"lafiya qalau ya gida.

Kallonta kuma ya koma yi sanye take da hijabi har kasa yayin da tayi fayau fuskarnan ba komai farin da tayi.

Safwaan ne yace" kije ki kwanta da wuri gobe da wuri zamu fita. Daga haka ya mike ya huce zuwa toilet.

Najwa ce ta sauke ajiyar zuciya ta dago sai a lokacin ta samu damar karewa dakin kallo,a lokacin ne taga wani tsohon hoto da mamaki ta kalli hoton ranar farkonta ce a makaranta.

Gefe kuma ta tina ranar graduation din su inda suka saka blue black din riguna da huluna.

A fili ta fyrta"yah safwaan ina ya samo wannan hotunan,ganin babu mai bata amsa ne yasa taja kafafunta ta bar wajen.

A falo ta tarar da umma zaune tana kallo,kusa da ita taje ta samu ta zauna, komai ta tina kuma sai naga ta kkwanta ta dora kanta akan cinyar umma.

Umma ce ta dubeta tace"najwa lafiya dai ko.

Najwace ta runtse idanu tace"umma bakomai, umma ni ba abinda zance muku,kun taimakeni umma,kun mayar dani mai ilimi, dik da bakusan ko ni wacece ba.

Umma jin ta dakko wannan maganar ne yasata fadin"shikenan ya isa tashi kije ki kwanta kinji dare yayi nima yanzu zan tashi,najwa ce ta mike tana wa umma sai da safe ta shige zuwa dakinta.

Sai da ta shige umma tai shiru tana tina lafazin yarinyar tabbas abbah sai dsi allah ya saka masa da alkhairi amma yayi dawainiya da najwa,da wannan tinanin ta mike ta bar falon bayan ta kashe wutar dakin.

Safwaan ne ya fito dakin najwa ya tura yaci sa'a a bude yake, a zaune ya ganta tana duba wasu takardu daga ita sai riga iya gwiwa mai siririn hannu.

Jin shigowarsa ne yasa ta saurin jan hijabinta ta saka tana kakalo murmushi tace"yah safwaan kazauna.

Safwaan ne ya zauna yana kara kallonta,sai kuma yace"najwa kinsan me ya kawo ni wajenki.

Najwa ce ta girgiza kai.
Chapter 26 · 0% Book details