← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga kan da zatayi ne taga gari yayi haske fauu, tashi tayi dik da jikinta ba dadi zuwa tayi ta hura wutar tare da nausa tukunyar kunu, fitowar umma yayi dai dai da tashin najwa daga kan kujera najwa ce ta tsugguna tace" umma ina kwana lafiya, ta bata amsa"ina markadan wainar shiru najwa tayi tana hange cikin masifa umma tace da ubanki kike jira yazo ya dakko miki.

Najwa ce ta kalleta ummah na dauka nabila ce zata dauko, dai dai lokacin nabila ta fito tana mika, nufota tayi tace" ke ni ce zanje na dauko markade tabb, wallahi bazan dakko ba, umma ce tayo kanta wai najwa baki da mutunci ne waya ce jiya baki dakko markaden ba, cikin inda inda najwa tace umma kinsan jiya pa ruwa ake daga mata hannu tayi tashi ki wuce ki dakko markaden tin kafin nabata miki najwa ficewa tayi tayi hanyar gidan mai markadan.......

Da kyar da dakko Markaden tsabar yawa ta dawo a lokacin ruwan kunun ya tafasa ba kowa a gidan sai ruwan zafin Dake tafasa kallon tukunyar tayi nagode allah iccen busasshe ne tana dama kunun a katuwar randar goro ta dora tandar wainar tana dorawa ana fara sallama wata yarinya ce ta shigo da flask sai kofi ta hau layi najwa na cikin aikinta a lokacin layi yayi yawa burinta ta sallami al'ummar wajen nabila ce ta taho da isa ta dauki kwano ta taho zata diba najwa ce tayi magana dan allah nabila ki taimaaka ki bari na sallami yaran nan bakiga makaranta zasu je ba kallonta nabila tayi ta babbake da dariya eyeeeh lalle najwa ni kenan gidan gala zani ko girgiza kai najwa tayi ita kuwa nabila ta tsugguna ta debe wainar ta kara gaba abinta tana shiga daki ta saka kuka yayin da umma ta taso meye kuma meye take tambayar ta cikin kuka nabila yace umma ba najwa bace dannace ta bani waina wai shine ai gidan gala zanje ba makaranta ba cikin zafin nama umma ta maimata yanzu najwa ce ta fadi hakan aikuwa yau sai naci uwarta wallahi ficewa tayi tayo kan najwa a lokacin dik ta samu layi ya ragu...........

Najwa na zaune taji wani gigitaccen mari akan fuskarta bata ankara sai kararta ta tashi wayyo umma kiyi hakuri dik da taji jikinta da zafi amma bata daina ba rike kunnanta tayi daidai nan fahad ya shigo yana mai bawa umma su hakuri sakinta tayi ta dauki plate ta zuba waina tayi dakinta har zata shiga ta tsaya kai kuma ka dauka ka zuba abincin kazo ka tafi makaranta tsugguna wa yayi a gaban najwa cikin muryar lallashi yace aunty najwa kiyi hakuri komai zai zama ba komai ba ki kara hakuri najwa ki tuna da maganar mahaifinmu ta karshe a kannu najwa kiyi hakuri da halin mahaifiyar mu kinji murmushi tayi kai fahad ba komai fa ai nasaba ma da wannan rayuwar cikin rawar murya tayi maganar taba hannunta yayi kai najwa baki da lafiya ne cikin yake tace ea dan zazzabi ne yake damuna amma ai da sauki kai najwa anya kuwa hamsin yazaro najwa wannan kisayi paracetamol nasan umma ba lalle ta baki kudin magani ba amsa tayi take ta godiya wainarsa ta basa yatafi daki sai wajen 11 wainar ta kare sannan zazzabin na barazanar kwantar da ita cikin karfin hali ta fice daga gidan tayi hanyar shagon Bala mai chemist......

Tin daga nesa yana hangota ya fara fara'a tana karasa wa ta basa kudi bala ka bani paracetamol na dika kallonta yayi najwa wai baki da lafiya ne takaitaccen murmushi tayi ea zazzabi ke damuna panadol din ya mika mata ta nufo hanyar gida tana shiga randa ta nufa ta dauki wainar da umma ta ajiye mata tayi dakinta ta dukunkune a cikin fatattakakken abin lullubar.Umma kuwa jin najwa shiru bata fito yasa ta tashi tanufo dakin nata kallon dakin tayi sama da kasa aikin banza dakin ma wari yake baxa ido take ko zataga najwa abin mamaki a kwance ta ganta tana bacci cikin wani bacin rai ta nufo waje ta samu icce ta koma dakin allah sarki najwa na bacci taji saukar duka a firgice ta tashi tare da furta inalillahi bata karasa bataga umma tayi shiru cikin masifa umma aa kya tsaya ai da sai ki karasa wato ga shaidaniya ko itadai shiru tayi daga iccen umma tayi ta kara zabga mata a baya ai da gudu ta fito daga dakin biyota umma tayi tana duka yayin da najwa bakinta ke furta ummah dan allah kiyi hakuri amma bata bi takanta ba dukanta take ihun ta ne yasa makociyarsu mahaifiyar amina ta shigo tana bata hakuri sai da kyar ta hakura yayin da najwa ke duba hannunta da ya kumbura ga jikinta dik wani wajen ya tashi yayi jawur salame ce mahaifiyar amina take mata magana yanzu ke kashe yarinyar zaki wai ke Zainab meyake damunki ne eyee haba najwa ce ta tashi saboda kallon da umma tayi mata tashi tayi jikinta dik yayi tsami ta nufi hada kwanikan a haka ta samu tayi wanke wanke a lokacin salane harta futa najwa ce ta tsaya a can baya umma ce tace ubanki kike jira kikazo kikasani a gaba kamar zaki cinyeni hawayen da take kokarin boye wane ya fito kallonta umma tayi taja tsaki wallahi najwa baki daku ba wannan ai ba kuka kikai ba zan miki mai dalili wanda jikinki zai gaya miki goge hawayen tayi kiwuce kije wajen musa ki amso dan ubanki kalli lokacin haka ta dau wani tsumman mayafi ta nufi shagon musa mai kayan provision........

Tafiya take kamar batason taka kasa a lokacin har anfara taso 'yan makaranta gefen wasu samari su 3 ta wuce suna kallonta sukai mata magana kasancewar sun santa sai da suka gaisa sannan ta wuce daya ne ya kalli dayan yace nifa wannan yarinyar tana bani tausai gata yarinya amma kuma tana da hankali nifa ko dik mai saida abincin da nake gani bantaba ganin wata kamar yarinyar nan ba ga ladabi kai allah sarki dayan ne ya kallesa ni kaina tana birgeni matsalar ta daya mahaifiyar ta batasonta bata kaunarta tafison sauran yaran ta su biyu wanda bai magana bane yaja tsaki aiki banza wai mutane su haifi yara amma kuma ku zabi wasu su bar wasu ita fa wannan ko zata kwana a titi kuna nufin ba wanda zai nemeta amsawa sukai da naam sannan suka sauya akalar zancen.Najwa sai da ta jira layi sannan ta karasa sai da suka gaisa ya kalleta aa najwa mahaifiyar ki ce ta aikoki daga masa kai tayi da eaa cikin sakin fuska ya bata kayan abinci da suke dafawa idan ta siyar ta biyo ta basa kudinsa ta taho gida a hanyarta ne suka hadu da fahad yana kallonta yay murmushi aa aunty najwa har jikin yayi sauki ne dariya tayi eaa mana fahad idonsa ne yakai kan hannunta zaro ido yayi kai najwa meya sameki waye ya dakeki.......

MAHAIFIN MU NE SILA

BY

🩷_Queen Waleedah_🩷
❤️_Official Ashkiey_❤️

*TAURARIN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION*

*Team Of Hazik'ai Writers*

From the writers of
Aishatul Humairah
Fateemah Zahra
And more❤️

DEDICATED TO MY FAMILY

*PAGE 3*

Fahad ne ya kamo hannunta suka shigo gidan ko sallama bai yi ba ya fara kwala kiran ummah umma daga labule tayi ta fito lafiya fahad bata karasa ba ganin da tayi rike da hannun najwa tsaki taja a zuciyarta ta furta yanzu zai hau banbami kamar kuwa ta sani matso yayi yanzu umma ya dace kenan kalli fa dukan da kikai najwa sai kace ba mutum ba umma najwa pa 'yar ki ce amma kin mai data kamar jaka itace tallah itace jan ruwa wanki wanke wanke kuma tana miki biyayya amma kuma dik baki gani ba sai kin daketa dukan ma da icce haba umma kuma... Katse aa tayi ya isa fahad wato da kazo ka titsiyeni yanxu rama mata zakayi kallon ta yayi aa umma amma tsawa tayi masa amma me yayin da najwa tana gefe tana kallonsu ai nadauka dukana zakayi ko ma nace ka rama mata fahad ka fita daga ido na wallahi ka fita daga idona na fada maka pa ko tsaki taja again ta juyo kan najwa le kuma uwarki kike jira kikazo kika sani a gaba shegiya fice kije ki dora girkin kar rana tayi sumi sumi ta wuce ta fara kokarin hada wuta fahad ne ya wuce wani dakin na gefe da najwa......

A haka rayuwa tayi ta tafiya bayan kwana 3 da faruwar wannan al'amari ne a lokacin bayan isha'i najwa na tasha tukuru ne ya taso a buge ya nufo najwa,najwa tana ganinsa tasha jinin jikinta tare da furta addua da tazo bakinta dik da ba wata addua ta sani maganarsa ce ta tsinkaye ta ya furta ke naj..wa wai..ya maganar mu tashi tsaye tayi dan allah tukuru ka kyaleni banason takura kasan bazan soka ba kaima kasani kallonta ni kike gayawa haka najwa wai dan kinga kinada kyau ko tsaya ki gani yana juya baya tsaki najwa tayi ta dau robar danwaken ta tafi kaiwa wani juyowar da tukuru zaiyi mai ne mai zafi a wani ludayi watsowa yayi take man ya sauka kan amina kawar najwa kara ta saki take mutane suka cika wajen yayin da tukuru ya fara dariya.....

Cikin maye ya furta shegiya da wayace ki zauna tafiya yayi yana tumbelensa yayin da dawowar najwa taga mutane yasa ta matsawa kusa abinda fito daga bakinta ne nashiga 3 matsawa tayi kusa da ita hannun ta ne sai gefen wuyanta daya fallatsar mata najwa ce ke furta mata sannu amina ce yayin da hawaye ke zuba ta hankadata da dayan hannu dallah matsa kuma wallahi wallahi najwa bazan yadda ba kinji dai nafadamiki shiru najwa tayi can kuma ta tashi ta karkade kasar to ni amina me naimiki nai kifadan mana tsaki amina taja dogon tsaki laifin waye nakine ai shegiya mai siffar birrai murmushi najwa tayi to amina sai me dan kin zageni amma ni nai miki ne ai tukuru ne ya miki ba ni ba dallah matsa shashasha kawai allah ya isa kuma wallahi sai na fadawa zainabu aikin banza tashi amina tayi tana kuka ta nufi hanyar gida.......
Chapter 2 · 0% Book details