← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Habiba ce tace"nagode dikanku tabbas alhaki kwikwuyone kuma sharri dan aike ne,yarinya dik da bansanki ba amma tabbas nasan da cewa kin taimakeni nasan dacewa na fuskanci rayuwa a cikin gidan yari kuma abinda na shuka na girbe abuna.

Daga nan aka fara gabatar da 'yar karamar walima a cikin gidan nasu wanda safwaan da kansa ya shirya, ga safna ga kuma sakina da sauran al' umma.

Bayan kwana 2 kowa ya koma sai safna da sakina a zaune kusa da umma habiba,wata kwafa umma habiba tayi tace"ai wallahi daga suraajan har aminan ba wanda zan bari,wata zabura safna da sakina sukayi suna kara kallon mahaifiyar tasu.

Safna ce tace"umma me kike nufi,tsaki ummar taja tace"abinda kike nufi shi nake nufi dan uwarki, tashi tayi ta bar falon.

A can bangaren safwaan kuwa zaune yake yayin da yana rungume da najwa ita kuma sai shagwaba take zuba masa,juyowa yayi ya kasance suna kallon juna yace"babie hankali ya kwanta ko,bukata ta biya ga aaikin lauya kuma,ga kuma bake shop sai kuma me.

Najwa ce ta ce"shikenan sai kuma kai da ka zame mini bango a cikin rayuwata yayana,yanzu dai yaushe zakaje ka dakko dawha da afraz,kallon yayi bayan ya sumbaci bakinta yana shafa cikin ta yace"sai rananr dana tabbatar da wani babien a cikin babaiena.

Daga nan dagata yayi sama suka huce zuwa badroom bayan sun rufo dakin.

Sakina da safna ne suka karasa suka ce"haba umma kenan baki sududa ba,haba umma dik wannan zaman da kikayi a prison amma baki canja ba,dagowa tayi tace"ke koda zan rasa raina sai na dau fansa ta (Sunan wani novel di na) safna da sakina ne suka mike suna fitowa daga falon.

Safna ce ta dubi sakina tace"sakina ni bazan kara yadda da umma ba, domin a baya ta cuceni ta kuma zalunce ni,sakina ce tace"bare kuma ni,dan haka ni daga yanzu iya ka ci na part din umma aminatu, daga nan suka fice suka koma part din aminatu.

🍂Alhamdulillah! 🍂alhamdulillah!!
A nan ne zancen zuciya ya tsaya. Duk da cewa an gama rubutun nan, amma sakonsa zai ci gaba da rayuwa a zukatan masu karatu."

Kamar yadda kowace hanya ke da ƙarshe, haka ma wannan littafi ya zo ƙarshe. Amma darussansa, za su ci gaba da haskaka rayuwar masu fahimta."

Rayuwa cike take da sirrika, kuma wannan littafi yana ɗaya daga cikin hanyoyin bayyana su. Na gode da kasancewarka tare da ni har zuwa ƙarshe."

Wannan ba ƙarshe bane, illa kawai sabon farawa ne ga tunani, hisabi da gyara. Ku kasance da kyau, kamar yadda labarin nan ya ƙarfafa."

*ALHAMDULILLAHI*.
_Godiya ta tabbata ga ubangiji mad'aukakin sarki daya bani ikon kammala wannan novel nawa mai suna *MAHAIFIN MU NE SILA* ,ina rok'on ubangiji ya yafe mini kurakurrena abinda na fad'a daidai ubangiji yayi mini sakamakon alkhairi, ina fatar makaranta littafaina zasu dauk'i darasin dake cikin wannan labari su watsar da abinda nayi cikin kuskure._

*Ku cigaba da kasancewa tareda ni Waleedah Muhammad domin samun daddad'an labarai daga gareni, ina muku fatar alkhairi arayuwarku masoyana sai kun jini asabon novel d'ina mai suna *ZABIN IYAYE NA KO ZABINA* .

_QUEEN WALEEDAH ce mai son farin cikinku zaku iya nemana ta wad'annan nombobi._

07033313681
08021211421
Chapter 31 · 0% Book details