Sashe 6
Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*
✨✨✨✨✨
💪😊
https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F
Whatsapp Channel
Page 9
*Bayan Kwana 2*
Wani dan karamin daki alhj gambo ya bude sanann ya kalli wadansu halittu bakake yayin da suka zane gaba daya tiles din dakin da wani irin rubuta, wanda aka yi sa da jini, shigowa yayi sannan ya rufe yasaka key, kallon kowa yakeyi shima cike da azama ya zauna take suka fara fitar da wani irin furuci mara dadin saurare, sunfi awa 3 ba wanda yayi wani kwakkwaran motsi, daga nan ne dakin ya fara girgiza,dakin da yake duhu sai hasken candle a wanann lokacin hasken ya dauke, baya da kamar awa 1 naji wata irin muguwar murya tace"ka ceci kanka gambo.
Amma ka sani ba tsira kayi ba, domin bazaka ta6a tsira ba har sai ka kawo mana najwa, idan kuwa baka kawo mana najwa ba, to kasani dik abinda ka mallaka sai ya kare sannan kuma dik abinda kake ji dashi zaka nemesa ka rasa,sannan muna tayaka murna da samun matsayin da kayi ya kai gambo ubangidan wadan nan halittun da suke zaune, a yanzu gambo shi ne ubangidan ku, daga haka kowa ya 6arke da wata mahaukaciyar dariya daga nan haske ya fara dawowaa daidai.
Dakin ne yayi fayau yayi da kuma sai naga ba kowa sai wanann mutumin wato gambo, cike da farinciki ya mike, sai kuma naga ya turkune fuska, can kuma yace"yo me zai dameni yanzu zan nemoki najwa domin nasan yanzu bazakiyimin wuyar kamuwa ba, daga nan ya fita.
Mufeedah ce t shigo tana kallon sa, kallonta yayi sai kuma yayi murmushi ya karasa wajenta, ya rungumota yana fadin buqata tabiya ki tayani murna, yanzu abu na gaba shi ne nemo najwa a madubin tsafin da za a bani shi wani satin, a taron da za a gudanar a cikin kumgiyar, matar ce ta sumbacesa sannan ta kalli hannunsa ganin jini hakan yasa ta kar6a ta lashe tana fadin"shikenan yanzu sai mu jira ranar daga nan suka fada kan gado daga nan na fito zuwa tsakar gidan.
Ganin yara nyi birjik gasu nan,ko ta ina haka yara nake gani, a fili na furta"to fa dik wadan nan yaran na gambo ne anya bada aljanu ba, daga haka na dakko takarda ta da biro na na baro gidan.
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
A yanzu najwa ta ware bata iya shiga mutane ba yayin da umma bata fasa dukanta kullun ba, yayin da fahad ke fadin umma ki kyaleta,ko kallinsa batayi ba, yau kwanan su 2 a cikin kauyen, nabila ce ta fito zuwa kofar gida ta zauna tana wasa da kasa, wata yarinya ce wadda batafi sa'ar ta ba tace"hala ku baki ne anan ko, cike da murmushi a face din ta tace"eaa mu baki ne yau kwanan mu 2,karasowa tayi ta ajiye bokitin hannunta sanann tace"ni sunana fatsima ke kuma fa, a hankali nabila tace"nabila.
Fatsima ce tace"ke bazakije debo ruwa ba,da murmushi tace"dama ana zuwa debo ruwa anan dariya fatsima tayi tace"ana zuwa mana, nabila ce tace"to bara na tashi na dakko baho sai nazo mu tafi, bata dade ba ta fito suka tafi rafin garin.
Najwa ce a zaune tana kallon kasar wajen tana share hawaye, a hankali ta furta umma na gama, ummarce tace"to tashi ki wuce kije ki dakkomin nikan saura kuma ki dade sai na tattakaki, mikewa tayi ta bar gidan tana gyara mayafin kanta, tafiya take ita kadai, daga can nesa ta hangi wajen mai nikan, karasawa tayi ganin bai nika ba yasata juyawa ta koma gefe a zauna ta rafka tagumi.
Sai can ta mike ta nufi bayan shagon nan ne taga ashe daji ne, shiga tayi tana kokarin tafiya taji wata tace"ke baiwar allah ba'a shiga nan wajen, jiyowa tayi tace"meyasa ba a shiga, yarinyar ce tace"ana samun mugayen halottu wanda suke iya cutar da dan adam, najwa ce ta juya tace"to ni an gaya miki 'yar adam ce, cike da tsoro ta fara karkarwa, sai kuma najwa tai saurin mazewa tace"ina nufin dama nima ai' yar adam ce.
Yarinyar ce tace"amma ke bakuwa ce ko,najwa ce tace"eaa bakuwa ce yau kwanan mu 2 a garin nan, ke kuma fa, a hankali tace"sunana kulu kuma ni 'yar gidan me gari ce, murmushi tayi tace"ni kuma najwa, daga nan suka fara hira dik da najwa ba magana take ba amma yau kadai taji ta sake da wata har sunyi hira, bayan an nika musu haka suka taho hanya suna hira, daga karshe kuma kowa ya kama gabansa.
Tana zuwa gida ta tarar da fahad ya dawo daga cikin gari, kasancewar umma ta aikesa, kallonta yayi sai kuma yace"yaya najwa kindawo, da eaa kawai ta bisa bata kara magana ba,wata leda ya mika mata,kar6a tayi tace"nagode fahad, daki ya koma wajen umma yace"umma kin lura yanayin najwa ya fara canjawa, cike da kulatace"nagani fahad ni kaina ina tsoron wanann lamarin domin kuwa saura kwana 10 ta cika shekara 18 daga nan wani sauyin ne zai zo mata.
Sai kuma ta fashe da kuka tana fadin, gambao ka cuceni har abada bazan ta6a yafe maka ba, ka cuceni ka cuci 'yaya na domin kuwa ka lalata rayuwar najwa,fahad ne yace"umma kiyi hakuri ki bani labarin mahaifinmu, zainabu ce tace"zan baku labarin mahaifinku anjima kai da sauran' yan uwanku.
*MAHAIFIN MU NE SILA*
*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_
QUEEN WALEEDAH
_HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*

Page 10
Safwan ne ya fito sanye da manyan kaya yadi ne black dinkin riga da wando, dinkin yayi kyau abinka da farin namiji me ji da wanka,falo ya sakko sakina ya tarar tana karatu a kasa ta barbaza litattafai,jin fitowar safwaan ne yasa ta hade su tana kallon fitowar tasa.
Shima yan asakkowa ya zauna yana fadin"sakeenar umma, wato dai karatu ake ko, murmushi sakeenah tayi tace"ea yaya safwaan kasan mun kusa fara exam, kuma bata karasa ba sakamakon wakar da take tashi a gidan ta khaid wato orobo, sakeenah ce ta kalli safwaan, yayin da safwaan din ya kalleta yace"safna ta dawo ko, sakina ce tacec"ea ta dawo kuma tasan muna da exam amma shi ne ta kunna wakar arna.
Safwan bai ce da sakeena komai ba ya mike ya bar falon da yake zaune,wata kofa naga ya nufa ya bude, kokarin kallon wajen naga yanayi, lokaci guda naga mood din sa ya chanja, tafiya yakeyi yana kallon safna, sai a lokacin na kalleta, sanye take da wani matsatsen wando, wanda ya fito da dik wata surarta, sai kuma wata riga top fara mai ratsin baki, kanta ba dankwali yayin da ta tula gashin roba.
Cike da takaici ya karasa wajen yana kallonta tana kallonsa amma sam bata daina abinda take ba, bai san lokacin daya daga Bluetooth din ya kwada shi a tiles din falon ba, sanann yaja gashin kanta, kokarin kwacewa takeyi amma yaki sakinta, cike da bala'i naji safna ta fara fadin"shege azzalumi kuma in allah ya yadda saurin sakinta yayi sannan ya dauketa da maruka a kowanne kunci.
Safwaan ne yace"lalle na tabbata safna baki da hankali, yanzu ni zaki kalla kicewa shege, kinsan girman zagin nan kuwa, murguda baki tayi tace"ea na fada to idan kai ba shege bane, kai wanene, na fada shege, kuma kai ba dan gidan nan bane, uban waye baisan ubanka ba, ubanka mugu ne azzalumi, sakinta yayi kawai ya zauna yana fara huci.
Safna batasan lokacin da taji wani gigitaccen mari da aka sauke mata, cike da wani mugun zafi ta kwala ihu ta zauna a kasa, wamda hakan ya haddasa fitowar sakina,umma, sai kuma mahaifiyar safna. Mahaifiyar safna ce ta karaso tana tada 'yar tata, tana fadin"kuma zaluntar yarinyar nan sam bakwa sonta.
Dattijon mutum ne sanye yake da glass a fuskarsa, kallon fuskar safwaan yayi lokacin daya kada yayi ja, sai kuma ya kalli safna yace"sam na yadda baki da hankali, hauka ne a kanki, kuma sam zaki ga matakin da zan dauka akanki, tinda ke bakya jin magana, jan hannun safwan yayi ba yadda ya iya haka ya mike yana tafiya kamar wani mai maye,juyawarsu ne yasa mahaifiyar safna fadin"ohhoooo hooo ai dai ba karya tayi ba idan yana da uban ba sai a nuna mana mu gani ba.
Dattijon ne ya juyo yana kallon ta sai kuma yace"sai yau na tabbatar da cewa habiba baki da hankali yau na kara tabbatar da maganar da take yawo cewa ciwon hauka ya kamaki, ki dubeni ni kikewa ihu, karki manta nidin mijin ki ne wanda kike neman aljanna a karkashin kafata,kallon ko inkula ta masa sanann tace"dik abinda zakayi baka isa ka chanja wannan maganar ba ta cewa safwaan ba dan gidan nan bane.
Sakina da umma suka bi bayan su, a falomsu suka tsaya yayin da shi kuma safwaan yana tsaye yana furzar da huci, a hankali yace"abbah ka barni na tafi dan allah, taya za a ce wannan karamar yarinyar ita take fada min maganar cewa ubana azzalumi ne.
Dattijon ne yace"koda zan barka ka tafi amma ka tabbatar da cewa sai kaje ka nemo wanann sassaken iccen, wamda da shi ne kadai sihirin dake jikinka zai karye, umma ce ta kalli dattijon tace"abba wai yaushehabiba tasan da maganar nan bare har 'yar ta safna, kallon ta yayi sai kuma yace"sakina wuce kije kici gaba da karatunki allah yayi miki albarka.
Abbah ne yace"ni kaina bansani ba amma na tabbatar da cewa habiba da kanta ta binciko wanann maganar,umma ce tace"to taya zata ji baya da shekara 25 ba wamda yasan da wannan maganar dagani sai kai, baiyi magana ba kawai ya juya ya mika mata wayarsa, duba tayi sai kuma naga ta jinjina kai tana kara kallon safwaan.