Sashe 29
Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbah ne ya fitodaga masallaci yana kokarin shiga gidansa domin so yake ya huta yayi matukar gajiya,wani mutum ne ya taresa cikin dauda da tarin kazanta,yana fadin"alhaji suraja, alhaji suraja,dole ya tsaya yana saurarensa.
Mutumin ne yace"dan allah alhaji kayi min izinin ganin matarka da kuma dana,sai a lokacin abbah yace"mittaka dama kaine,inalillahi wa inna ilaihi raji'un,muttaka yayin da shi kuma ke fitarda hawaye a cikin idanunsa.
Haka ya shigar dashi har guest parlo,baya da haka da kansa ya kai masa abinci da abin sha yaci ya dawo hankalinsa.
Daidai lokacin umma da safwaan suka shigo,neman waje sukai suka zauna suna jiran suji yau kuma me zai ce.
Muttaka ne ya kalli aminatu daidai lokacin ya tsugunna gabanta yana fadin"aminatu ki yafe mini, nasan na cutar dake kuma na cutar da dan da muka haifa, har na aibata sa, kuma na jefeki da kalma mafi tozarci da wulakanci,nasan ba lalle ne ki yafe mini ba amma dan allah aminatu ki yafe mini.
Sai kuma ya juya wajen safwaan wanda yake kusa dashi,kafarsa ya kama yana firta"da na ka yafe mini nasan ban kyauta maka,kuma ban raineka ba,ban kula da kai ba, hasalima nayi maka asiri wanda yasa ka bar garin ma gaba daya,safwaan, safwaaan.
Yayain da safwaan ke fitar da wasu hawaye masu zafi,idanunsa gaba daya sun juya daga farare tass zuwa jajaye,yahin da hawaye ke sintiri a kan kyakkyawar fuskarsa.
Gaba daya falon shiru idan ka cire karar ac da takeyi,muttaka ne yace"tabbas jamila ta cuceni ta rabani da komai dana mallaka kuma yanzu na gane gaskia,a yanzu haka ma na koma ga allah na kuma koma masallaci na koma ina zuwa daukar ilimi.
Muttaka ne ya hade hannuwansa yana mai rokonsu da su yafe masa amma shiru,abbah ne yayi gyaran murya yace"muttaka tabbas kabi san zuciyarka,kuma sam baka yi sa'ar mata ba,domin kuwa gashi yanzu kazo kana fargar jaji (Littafin mu na gaba) dana sanin da bashi da amfani,aminatu, safwaan bara na kara tinatar daku dik da nasan kun sani.
Wanda ya cika da bacin rai, ƙiyayya, da ƙin yafiya – to ya cika da girman kai da rashin tsoron Allah. Ba zai iya samun cikakken kwanciyar hankali ba. Kuma zai iya rasa gafarar Ubangiji idan bai yafe ba.
Manzon Allah (SAW) yace:
“Duk wanda bai yafe wa dan uwansa ba, to Allah ma ba zai yafe masa ba.”
(Sahih al-Bukhari).
Sannan kuma yafiya tana kawo, zaman lafiya, rahamar allah hadi da rage cuttuka da kuma abin da bazan iya fada ba.
Aminatu safwaan a gani na ku yafewa muttaka tinda har ya budi baki yazo kuma wajenku a lokacin da kuke da ikon yafe masa,dan haka koma menene ya rage gareku, mikewa yayi ya bar dakin.
*MAHAIFIN MU NE SILA*
*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_
QUEEN WALEEDAH
_HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*
✨✨✨✨✨
💪😊
*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*
✨✨✨✨✨
💪😊
https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F
Whatsapp Channel
💮💮💮
🌼🌼🌼LAST CHAPTER
💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.
Page 51
Bayan fitarsa aminatu ce ta kalli muttaka tace"kaje na yafe maka duniya da lahira, nima ina fatan allah ubangiji ya yafe maka zunubanka,sanann allah yasa tuban gaskia kayi.
Muttaka rasa bakin godiya yayi, safwaan ne yace"nima na yafe maka allah ya yafe mana baki daya daga nan safwaan da aminatu suka mike suka bar falon,wani kukan farinciki muttaka yakeyi.
Basu dade da fita ba abbah ne ya shigo, yayin da muttaka ke fadin"nagode, nagode allah ya saka maka da alkhairi, abba ne yace"ba komai zaka iya tafiya yanzu ai tinda abinda kazo nema ka samu,allah ya yafe mana baki daya alfarmar annabi Muhammad s. A. W.
Bayan kwana 5
Jamila ce zaune ta harde akan daya daga kujerun falon tana daddana waya,mikewa tayi hankalinta na kan wayar ko me take kallon bansani ba dai.
Kitchen naga tayi tana shiga direct kan gas tayi tana kokarin nemo ashana,cikin kankanin lokaci ta karo gas din hankalinta bai kawo a kunne yake ba,ajiywa tayi ta kyasta zata dora take wuta ta tashi sama,jamila sama tayi sannan ta fado,take kitchen ya kama da wuta,itama gata a kwance.
Gaba daya gidan cikin abinda bai fi mintuna 20 ba yababbake sai kauri,hadi da mutanen unguwa da suka kirawo fire service,nan aka fara kokarin kashe ragowar wutarda tayi saura.
Gaba daya al'ummar unguwar jimami suke da irin yadda gidan ya babbake,can gefen gidan cikin wasu ciyayi wani mutum na gani da ka gani kasan yana da siffa irin ta bokaye, jikinsa banda layu da guraye ba abinda zaka iya fahimta,a tawa fahimtar nace boka ne, ji nai yana wasu surutai,sai kuma can ya babbake da dariya yana kara saka wata dariyar wadda sai da ta fitar da wani bakin hayaki.
Tohm karshen mai bin bokaye kenan da malaman tsibbu,nasihata a gareku 'yan uwa mata da kuma masu bin bokaye hadi da malaman tsibbu.
A zamanin da muke ciki, mun ga yadda mutane da dama ke komawa wajen bokaye, yan sihiri, malaman tsibbu da masu yin kallo da rana, da nufin warware matsalolinsu ko samo wata hanya ta gaggawa domin samun biyan bukata. Wannan dabi’a ce da ke kara yaduwa cikin al’umma, musamman a lokacin da mutane ke fuskantar kalubale ko wahalhalu.
Amma ya kamata mu sani cewa.
Bin boka haramun ne, yana rushe imani!
Annabi (SAW) ya ce:
"Wanda ya je wajen boka, ya tambaye shi wani abu, ya yarda da abin da ya fada ba, ba za a karɓi sallarsa na kwanaki arba’in ba."
(Sahih Muslim)
"Wanda ya je wajen mai tsibbu, ya gaskata da abin da ya fada, to ya kafirci abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (SAW)."
(Abu Dawud, Tirmidhi)
Illolin bin bokaye suna da yawa amma ga wasu daga cikin su.
Rusa imani: Wanda ya gaskata da boka ya yi kafirci.
Karya tauhidi: Saboda hanya ce ta neman taimako daga wanin Allah.
Biyan kudade akan karya: Bokaye sukan karbi kudi da kayan sadaka bisa karya da ruɗi.
Tushen rikici a gida: Wasu suna amfani da sihiri domin rabata da mazajensu ko iyayensu.
Toshe hanyar addu’a da tawakkali: Idan mutum ya koma ga boka, yana kauce wa dogaro da Allah (SWT).
Lalata tarbiyyar al'umma: Sihiri da bokanci suna haifar da kiyayya, gaba da cutar da bayin Allah.
Abubuwan daya kamata muyi shine.
Dogara ga Allah (tawakkali) Allah shi ne Mai iko da komai, shi kadai za a nema.
Yin addu’a Addu’a ita ce makamin mumini. Ka nemi mafita ta hanyar istighfari da salati.
Rokar taimako ta hanyar halal Idan kana da matsala, je wurin malamai masu ilimi, ba bokaye ba.
Karanta Al-Qur’ani da ruqya Wannan yana magance dukkan cututtuka da sharrin bokaye da aljanu.
Ka guji bin sahun masu bin bokaye Kada ka kusanci irin wadannan mutane.
Daga karshe inayin nasiha ga Masu bin bokaye suna jefa kansu cikin halaka da fushin Allah. Duniya da lahira na cikin hadari. Duk wanda ke da wata matsala, ya koma ga mahaliccinsa, domin Shi kadai ne mafita.
Allah ya shiryar da mu duka, ya kare mu daga sharrin bokaye da masu sihiri. Ameen.
Mudawo kan labari
Hakance ta faru a nan,karshen mai bin bokaye kenan da malaman tsibbu.

Page 52
Kano
Abbah ne zaune akan daya daga kujerun dakin yayin da yake tasbihi a cikin ransa, wata figaggiyar yarinya ce ta fito taba ta6e baki tace"ku jirasa ya fito sai kuyi magana yana ganawa ne da wasu, daga haka ta juya tana kallon fridge din dakin.
Alhaji Attahir amini ne ga alhaji suraj wato abbah tare dashi sukazo kamar yadda addini ya tanada,har zuwa wannan lokacin suna zaune,can sukaji motsi abbah ne ya daga kai yana kallon inda mutumin zai fito.
Alhaji gambo ne yayi wani katon tumbi ga baki daya karayi ga ciki yana jansa,kai abin ma ba kyan gani muni iya muni ga wani jan ido wanda yayi jawur kamar gauta,sanye yake da shadda baka dinkin jamfa.
Yana zuwa zama yayi kamar mutumin kirki abbah da alhaji attahir suka gaisa cikin sakin fuska kamar dama can sun san juna.
Alhaji attahir ne yayi gyaran murya yace"alhaji nasan baka gane mu ba ko.
Gambo ne yace"ina zan gane ku, ni ai ban ta6a ganin ku ba ma.
Alhaji attahir ne yace"gaskia alhaji baka taba ganin mu bane, dama munzo ne game da 'yarka wanda dan mu yace yana so.
Saboda haka bamuyi kasa a ido ba mukace bara muzo iyaye asan da maganar saboda halin rayuwa.
Gambo ne yayi kasake domin ya rasa bakin magana,shidai a wannan duniyar bazaice ga iya adadin' ya'yan sa ba, saboda yana da yara da yawa kuma sam bai san sunayen su ba.
Gambo ne yayi gyaran murya yace"to madallah ina fatan dai kuna da hoton ita 'yar tawa domin kuwa ni yanzu ba lalle na iya gane yarana ba,abbah kallon sa yayi sai kuma yayi wani murmushi yace"eah muna dashi,bara ma ka gani.
Abbah ne ya fito da wayarsa yana nemo hoton najwa,wani hoto na gani wanda take sanye da wata doguwar riga wadda ta kasance black da ratsin pink tayi matukar yi mata kyau,abbah ne ya mika masa wayar yana cewa"wannan ce yarinyar.
Gambo kar6a yayi yana mai gyarawa wayar zama a hannunsa,gilashin sa ya dauka ya saka,kallon screen din yayi take ya mike yacea"najwa,kaiii inaaaa wannan yarinyar ta mutu kuma bazata kara dawowa ba.
Wata kara ce ta karade gidan yayin da gidan ya fara girgiza shi kadai,wata dakusasshiyar murya ta fara fadin"innaaa gambo ka fadi, ka tina da ita,kuma ka fadi a dokarmu,a yau zaka sauka daga wannan kujera kuma zaka karbi hukunci mai tsanani.