← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 31

Sashe 30

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wullar da wayar gambo yayi yana fitar da wata kara wadda da kaji ta kasan bata lafiya bace,ga wani sauti dayake tashi,alhaji attahir da abbah mikewa sukayi suka bar gidan inda suka dauki hanyar komawa kadunaa.

Abbah ne yakira najwa,a hanakali ya bayyana mata komai,najwa ce tace"abbah shikenan kuma ai tasa ta kare kuma a yanzu ba wani abu daya isa ya yi,domin kuwa dakaji wananj kalaman kasan ya fadi kuma mutuwa itace karshen sa.

Da haka suka rabu yayin da najwa ke ta farinciki ita da umma da sauran 'yan uwanta,fahad ne ya kalli najwa yace"auty kamar yadda kika fada, dawowar ki zamuga canji gashi kuwa mungani,tabbas aunty ke kika zame mana bango a cikin wanann rayuwar aunty,gaba daya rungumeta sukayi yayin da umma ke kallon su cike da kaunar juna.

*******************

A can gida kuwa abbah ne ya kwashe labarin abinda ya faru tsabb ya gaayawa umma, ita dai ba abinda ta furta sai dai allah ya kyauta.

Umma ce tace"to yanzu wa zaiyi wa najwa waliyyi,abbah ne yace"ai ba komai bane ni zan mata,shi kuma safwaan sai mahaifinsa ya karba ko ya kika gani.

Umma ce tace"allah ya sanya alkhairi dik yadda kukayi daidai ne,addu'a ce allah ya basu zaman lafiya da zuria dayyiba.

Najwa gaba daya ta canja ta saba da mutanen kauyen nan yayim da dik inda ta gifta sai dai kaji ana kiran najwa najwa.

Ba laifi yanzu wani love suke zubawa ita da safwaan,dan a yanzu ni kaina love din nasu mamaki yake bani,komai nasu suna yi cikin tsafta da kuma kaunar junansu.

Ga safna da sakina wanda suke waya suma, sai umma wadda dik tafi nuna kulawarta a gareta,a haka har ta cinye sati 2 a sati na 3 ne aka fara shiryr shirye, a wannan sati ne aka kawo lefe na najwa akwati goma sha biyu,kowa na garin yana mamaki yana kuma jinjina iko na allah.

Ba wani event da aka gudanar sai dai kullin umma na mata fada da huduba akan rayuwar da zata shiga,najwa na saurarenta domin tabbas ta rasa ta ada amma a yanzu bazata bari ta rasata ba.

A ranar Jumu'ah karfe 2:00 bayan sakkowa daga sallar jumi'ah anan ne aka daura auren RABI'AH GAMBO Wadda al'umma suka fi sani da Najwa Suraja Muhammad sai kuma MUHAMMAD SAFWAAN MUTTAKA, Wanda mutane suka fi sanin sa da safwaan bisa sadaki naira dubu dari da hamsin,lakadan ba ajalan ba.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮
🌼🌼🌼LAST CHAPTER
💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 53

A washe gari ranar asabar inda aka dauketa da ita da nabila sai fahad da sauran al'umar garin wanda yawancin su gulma ce zata kaisu aka kaita gidan umma,umma a daki ta saka najwa yayin da najwa ke kuka tana kara fadawa jikin umma.

Umma tayi mata huduba sanann kuma tayi mata fatan alkhairi da fatan ubangiji ya basu zaman lafiya mai dorewa.

Abbah ma yayi mata fada sosai akan rayuwar aure da kalubalen dayake cikin aure.

Daga nan kuma aka gabatar da wata kwarya kwaryar walima wadda aka tar mutane aka ci aka sha akayiwa amarya da ango nasihohi a wannan dare ne kuma aka dauketa zuwa gidan mijinta.

Yayin da nabila da fahad su suka zauna su kuma sauran al'ummar kauyen suka juya,umma da kanta ta nuna nabila daki,shi kuma fahad wani guest room ne anan umma tace"yaje ya kwanta,ai fahad tinda ya shiga dakin yana zare idanu yana kara kallon daakin,kamar yadda fahad ya zama dan kauye haka ma ta bangaren nabila ita ma.

A bangaren amarya kuwa safwaan ne ya shigo shi da abokansa,bayan yiwa amarya huduba ana ne kowa ya juya aka tafi aka bar amarya da angonsa.

Safwaan ne yayi gyaran murya yace" babie najwa"

“Assalamu alaiki, ke uwar gidana, ke amaryata, ke ce farin cikin zuciyata da mafarkin raina. Yau Allah Ya hadamu bisa halal, kuma ya bani ke a matsayin matata – amana daga wajen Ubangiji. Ina rokon Allah Ya sanya wannan auren albarka, Ya zaunar da mu lafiya, ya azurta mu da farin ciki da salama.

Ina so ki sani cewa ni ba cikakke bane – kamar yadda ke ma ba cikakkiya bace – amma zan yi iya kokarina wajen kyautata miki, kula da ke, kare ki daga bakin duniya, kuma in zama mafaka gareki a lokacin farin ciki da damuwa.

Ina rokonki ki bani hadin kai, ki bani goyon baya, ki bani hakuri in na kuskure, ki rarrashe ni in zuciyata ta dame ni, ki kasance matata kuma kawata – domin rayuwa zata tafi cikin sauki idan muna juna.

Ba zan dora miki nauyin da ya fi karfinki ba, kuma ba zan taba cutar da ke da gangan ba. Ina fatan za mu zama abokai kafin komai, domin abokantaka ita ce ginshikin soyayya da zaman lafiya.

Idan na bata miki, ki tuna cewa ni dan Adam ne, kuma ki yi mini magana da kyau – kamar yadda nima zan kiyaye bakina da halina gareki.

Ina fatan ki bude ranki ga wannan sabuwar rayuwar, ki rike mutuncinki da mutuncina, ki rike gidana da daraja, domin ni zan rike ki da daraja. Allah Ya sa soyayya ta zauna tsakanina da ke, kuma Ya albarkaci gidamu da zaman lafiya da zuri’a ta gari.”

“Ya Allah! Ka sa aurenmu ya kasance na alheri. Ka ba mu zaman lafiya da fahimta. Ka sa mu rike juna da mutunci har mu mutu muna tare cikin salama. Ka sa mu zama juna ne cikin alkhairi, ba cikin azaba ko sabani ba. Amin.”

Najwa ce ta kallesa kallo na fahimta sanann tace"tabbas nayi sa'ar miji nagari insha allahu ya safwaan zan maka biyaya gwargwadon iyawa na allah ubangiji ya hada mu da farinciki.

***************
Washe gari al'ummar da suka halarci biki na safwaaan suka fara bajewa,kowa na kokarin tafiya yayin da nabila ce ta zage take aiki tukuru na goge gige da kuma share share.

Fahad kuma yana bakin gate yana hira shi da mai gadi.

Umma ce ta fito tana kallon falon dake fitar da wani sanyayyen kamshi,lumshe idanu tayi a take najwa ta fado mata a rai,nabila ce ta tsugunna tace"umma sannu ina kwana,sai a lokacin ta budr idanu tace"sannu nabila, sannu allah yayi miki albarka, da ameen ta amsa sanann taci gaba da aikin nata da mutsuwa irin ta najwa. *MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮
🌼🌼🌼LAST CHAPTER
💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 54

A bangaren ango ma lafiya qlau suka tashi,yayin da ya zauna akan gadon yana kallon ta tana bacci sannu a hankali kamar wata babie.

Kallonta yake yana karewa halittar jikinta kallo yana kuma tina movement din su na jiya,a fili ya furta"INA SONKI NAJWA ALLAH UBANGIJI YAYI MIKI ALBARKA.Mikewa yayi ya tashi ya bar dakin domin zuwa ya sama musu abinda zasu ci.

A haka rayuwa taci gaba da tafiya a cikin wadan nan gidaje guda 2,daga nan ne kuma a dauke alkalami na na tafi hutu domin na gaji da rubutu,kunsan na tafi kasar qatar na leka samaiha wadda bata samu damar zuwa biki ba saboda laulayi da take fama dashi.

Sai kuma na leka babin gambo wanda ya kasance yayi mutuwar wulakanci da tozarci hadi da abinda ni kaina baki na bazai iya fada ba gaskia saboda munin abun.

Sai kuma na sake lekawa garin gombe inda anan ne kuma naga canje canje da dama, daga nan kuma na dawo gida na zauna domin yawon ya isheni haka,ku kunsan yadda nagaji kuwa,kai jama'ah ban ta6a rubuta novel wanda ya bani wahala ba kamar wanann gaskia.

BAYAN SHEKARU SHIDA (After Six Years)

Yah fahad yaushe zaka dawo kenan,
Fahad ne yace"bazan dawo ba sai dai ku boyoni.
Murmushi nabila tayi tace"ina zamu iya zuwa qatar nidai allah ya taimakeka,kuma allah ya sakawa abban afraz da alkhairi gaba dayaan su ameen suka amsa a tare.

Wata yarinya ce ta gudu naga ta shiga gidan abbah tin daga bakin falon take fadin"granny granny granny.

Yayin da karamin ke binta yana fadin"ki tsaya ni dawha amma ina har tayi nisa tana kara fadin"granny.

Zainabu na zaune taji dawha na fadin"ammah yeeeeee,murmushi zainabu tayi daidai lokacin wata matashiyar budurwa tayi tana fadin" to iyayen sangarta shgwababbiyar granny.

Zainabu ce tace"gidanku nabila zaki huce ki bani waje ko sai na 6ata miki, nabila hucewa tayi tana kara kallon kofar.

Hango Afraz tayi yana gudu yayin da ta isa itama ta tarosa tana fadin"yawwah babyna dama kai nake jira saboda nasan kaine kadai nawa a gidan nan.

Murmushi yayi yana mai sumbatar kumatunta,daga nan ta daukesa ta bar falon suka huce zuwa dakinta.

*******************

A bakin babbar koton wata ce sanye da black din kaya irin na lauyoyi sai kuma wasu cincirondon mutane da suke kallon fadin"najwa suraj Muhammad sai kinyi,daga nan na zubo idanu ina kara kallon zubi na halitta da kyawu irin na najwa,ta kara zama wata babba ga kuma kaya irin na lauyoyi da sukaai matukar karbar jikinta.

Haka suka shiga koto yayin da kotu tayi shiru inda aka fara gudanar d kara, bayan awanni 3 alkali ya yanke hukunci,bisa sakin wadda aka kamaa tsawon shekaru 8 ba tare da wata kwakkwarar hujja ba,sannan kotu ta wanke ta.

Umma habiba ce ita kotu ta wanke,gaba daya kowa ya fito yayin da alummar da yawa da 'yan jarida suka yo kanta,wasu na fadin Mrs Safwaan wasu kuma na furta"najwah.

A haka abbah da sauran mutane suka taho ya zuwa gida,bayan kowa ya kintsa ya kuma dawo.
Chapter 30 · 0% Book details