← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 31

Sashe 12

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 20

Fitowa tayi tana kara kallon su fahad da suke tsaye, dakin da kayanta take ta shiga tana kokarin dakko kaya, wata 'yar yaloluwar diguwar riga ta saka, sai dai tana da kauri, ta yafa mayafin ta.

A zaune ta gansu suna jiran fitowarta,tana fitowa ta zauna, umma ce ta mika mata kwanon koko da kosai a faranti, ci ta fara yi tana kallon gidan da kuma su fahad, lokaci guda hawaye ne ya gangaro mata ta kalli umma.

Umma ta kalla tace"umma bazaku iya zama dani ba, murmushi wanda yafi kuka ciwo umma tayi tace"nasani najwa koma menene yake faruwa daku laifi na ne, ban duba mijin da zan aura wanene shi ba, bansan sana'arsa ba, bansan asalin sa ba amma na yadda na aure sa ba, kowane bawa akwai tasa kalar jarabar ni kuma tawa kalar jarabawar kenan najwa,haka kuma ga taku kalar jarabawar.

Najwa ce ta kalli mahaifiyar ta ta tace"umma ki daina fadin haka, allah y tsara komai tin ba yau ba, dan haka abinda ya kamata kawai ki daina damin kanki, umma sallama nazo yi muku, domin kuwa a yau zan bar garin nan,umma indai na zauna bazaku iya zama dani ba.

Fahad ne ya kalleta yace"amma najwa ya kike fadin haka, to ina zakije kenan,murmushi tayi tace"dik inda naje zan dawo, bazan fada muku inda zanje ba, sai dai ku tabbata dawowata zata dawo muku da alkhairi da kuma sabuwar rayuwa.

Murmushi nabila tayi tace"to yah najwa idan kika tafi yaushe zaki dawo,najwa xe tace"bazan ce ga ranar dawowata ba amma kuma nasan dik inda naje zan dawo, kuma dik halin dana shiga bazan manta daku ba,umma dik wannan hirar tana jinsu ta kasa basu amsa.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

Sakina ce ta kalli Abdullahi tana mai sunkuyar da kai tace"me za a dafa, cike da soyayya ya kalli sakina yace"yanzu ke zaki shiga kitchen a wanann yanayin, daga zuwanki jiya.

Sakina ce tace"to menene dama ai aiki na ne, Abdullahi ne yace"dik da aikinki ne na barki ki huta, kuma fa baki da lafiya ko, saurin kare fuskarta tayi, daidai lokacin da wayarta ta hau kara, miko mata wayan ke kokarin yi yace'kayan kuka ga wayarki, dan naga har yannzu kamar marmarin kukan kike ko.

Murmushi tayi ta kar6i wayan bata iya basa amsa ba,ganin umma ce yasata mikewa ta baar falon, sa a lokacin na lura, wasu coffee brown din kujeru ne, wanda na kasa tantance kyaun su da kuma fasalinsu,sai dan karamin dining a gefe daya, sai wata siriryar kofa, a takai ce dai falon yayi matukar kyau, gashi dan daidai azanci.

Abdallah ne yayi murmushi yana mai shafa gemunsa, mikewa yayi ya shiga wata kofa, wadda na tabbatar da kitchen ne.

Umma ta furta a hankali,umma lafiya qalau, umma kowa lafiya, shidin yana kitchen,banji mai umman tace ba tace"to umma, insha allahu, umma ina abba, kodan ma zan kirasa da kaina, dan nayi kewansaa, umma labarin yayi safwaaan shiru ko, sai kuma ta katse wayaaan.

Zama tayi tana kallon wayar, tagumi ta zabga tana kallon screen din wayar,ta nausa a duniyar tunani, bata ji shigowa ba, sai ji tayi abdallah yace"baby yadai naga kinyi shiru,saurin janye tagumin tayi tana kallon gefe,murmushi yayi yace"naga alamun sai na karasa cire miki wannan kunyar ko,dariya tqyi tace"aa ba sai ka cire min ba ta fita, to fada min menene fadin abdallah.

Shuru tayi can kuma tace" dama so nake gobe zanje makaranta, domin zan duba result di na, munyi exam ance ranar monday results din zai fito,abdallah 6ata fuska yayi yace"ni baby banason wannan karatun gaskia,saurin kallonsa tayi nan da nan idanunta suka hau kwal kwal kamar zatayi kuka,abdallah ganin haka yasa shi fadin shikenan, sai na kaiki ko, idan kin duba sai mu dawo gida, dariya tayi tana fadin"yawwa my sai kuma tai shiru.

Abdallah gyara zama yayi yace"kinsan allah saikin karasa,sakina ce tace"na karasa me kuma nifa dama ba abinda zan ce, murmushi abdallah yayi yace"zancen kikeso yarinya idan baki karasa ba, bazan kaiki ba, dariya tayi tace"to ya hakuri my world,murmushi yayi sanann ya tashi ya rungumeta, domin tabbas yasan yayi dace da mata ta gari.

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

A lokacin da magariba na kawo kai, a wannan lokacin najwa ta mike domin tasani a wanann lokacin ne halittar jikinta zata chanja,kallon umma tayi wadda take girki gefe kuma nabila, take wani hawaye ya gangaro mata, ba zato kawai tazo ta rungumeta tana kuka mai ratsa zuciyar mai saurare,sakinta tayi nan ta fara soshe², tana kuka cikin abinda bai fi second 10 ba wata katuwar kura ta bayyana.

Zabura nabila tayi tana kuka wiwi,kurar ce ta matso kusa da zainabu, fahad ne ya kalli najwa ya fashe da kuka yqna fadin"tabbas yaya najwa kinyi gaskia, bazamu iya zama dake ba.

Umma yanzu ya zamuyi da ita ta a daga garin nn, umma ce ta kalli fahad, ta kalli najwa ta kuma kalli nabila sai ta fashe da kuka ta durkusa,tabbas gambo ka cuceni, ka zalunci rayuwata, bazan tta6a yafe maka ba,wani gurnani wannan kura tayi,sai ga hawaye ya zubo daga idanunta, nan ta nufi hanyar fita daga gidan.

Gari ta fito tana tafiya a sannu a hankali, wasu dandazon yara da suke wasa, kallon kurar sukayi take suka dare suna ihu da iface iface, nan fa gari ya hautsine, yqyin da wasu ke kokarin kama kurar,najwa ganin haka yasa ta saka gudu, binta suke ta rasa yadda zatayi.

Zainabu ce ta fito da yaraanta suka bi bayansu suna fadin"karku lahanta ta, ba kura bace mai cutarwa najwa ce, amma ina ba wanda yabi ta kanta, da kyar da sidin goshi najwa ta samu ta fada wannan katon dajin na bayan shagon mai nika.

Zainabu ce ta zauna tana kara kallon wajen, wanda ta riga da ta tabbatar da cewa shikenan najwa bazata dawo ba,ta riga ta tafi,wani sabon kukan ne ya kara taso mata, wanda da kyar ta mike suka nufi gida.
*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮

Page 21

Tinda ta samu tabar wannan kauyen taje gudu, ta kai kusan awa 2 tana gudu sannan ta tsaya, kasancewar jiyo karar mota da tayi,ta cikin ciyayin ta leka, nan ta gani ashe titi ne,gaba daya ba kowa ko haske babu, kasancewar karshen gari ne,sai da ta shirya sannan ta fita da wani matsiyacin gudu ta tsallaka titin, wani dajin ta shiga tayi tafiya mai nisa sannan ta samu kasan wata bishiya ta zauna tana fitar da huci.

A can kuwa bayan an samu kurar ne ta tsere, a wannan dare al'ummar wannan kauye sukayi wa mai gari caaa a kofar gida,yayin da kowa ke tofa albarkacin bakinsa,maigari ne yayi gyaran murya yace"na saurare koken ku, sannan kuma a daren nan zaba toshe wancen dajin na bayan nura mai nika, sannan kuma mun zauna mun yanke hukunci cewa, zainabu da sauran yaranta 2 bazatayi yu ta zauna a garin nan ba, domin zamanta a nan hadari ga lafiyar mu, mu da yaran mu, domin indai najwa ta kara dawowa to tabbas sai dai buzun mu.

Nan fa kowa ya fara cewa"eaa a koresu, kara ma su tafi mahuta da wannan bala'in,jin haka ne yasa zainabu mikewa tana mai share hawaye tace"ku kwantar da hankalinku, har abada najwa bazata dawo ba, domin kuwa a yanzu haka ma zuwan da tayi tazo tayi min bankwana, najwa ta tafi, nasan har abada ba lalle najwa ta dawo ba, somin itama tana jin tsoron shiga cikin al'umma.

Kowa shiru yayi, can galadima yace"to ranka ya dade tin da har ta tabbatar da cewa najwa bazata dawo ba, ai bai kamata ace ta tafi ba,domin kuwa mu muna mata fatan dawowar 'yar ta ta, kuma bamusan nan gaba mai zai faru ba,liman ne yace"gaskiyarka galadima domin kuwa hadisi ne ingatacce daya ke cewa"kasowa dan uwanka abinda kasowa kanka, dik cikin nanba wanda yakeso' yar sa ta zama kamar najwa, dan haka ayi hakuri su zauna.

Maigari ne yace"to kunji jawabi abin fadi kuma yana gareku,nan fa al'ummar aka fara cecekuce, da kyar aka tsayar da matsaya na zaman zainabu da 'yayanta a wannan gari,zainabu ce ta tashi tana kuka ta bar wajen, kowa na wajen ta basa matukar tausayi.Haka suka tafi gida sunayi suna kuka kasa² mai cin rai.

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

Sanye take da wata English wear iya gwiwa kanta ba dankwali, a wannan daren haka ta kure kida cikin wakar KHAID (orobo),cikin sanyi jiki ya shigo gidan, sakin baki yayi yana kallonta, cike da 6acin rai yace"wai safna menene haka, me yake damunki ne?.

Sororo tayi tana kallonsa,sai kuma naga taci gaba da rawarta,zuwa yayi ya kashe wakar, cikin zafin rai tace"uban wayace ka kashe min waka, rayyan mamaki karara a fuskarsa yace"safna iskancin naki har ya kai da ni zaki zaga,safna baki sanni bane, baki san wanene ni ba ko,kina dab da kikaini bangi na fara aikata miki abinda baki ta6a tinani ba..

Safna ce ta kallesa ta saki tsaki tace"and so what, kai nifa yanzu rayyan ko sakina kai, kaine zakai dana sani amma ni sam ba zanyi dana sani ba akan wannan maganar,murmushin takaici yayi yace"ashe ba banza ba da akace min baki da kunya karna kar6i aurenki, amma dayake ni me biyayya ne ga mahaifin ki haka na kar6a.
Chapter 12 · 0% Book details