← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi tana tafiya sannu a hankali yayin da shi kuma ya kwala mata kira, juyowa tayi ta tsaya daidai lokacin ya zaro wayarsa ya mata hoto, ganim haka yasa ta saurin juywa, a falo ta zube tana fadin"aunty sakina, aunty safna badai tafiya zakuyi ba,umma ce tace"yo dama ke ina zaki san tafiya zasuyi saboda kinje kin biyewa safwaan da ba gajiya yake da driving ba,muryar safwaan ne yace"haba umma ina gajiya mana da driving murya a shagwabe, daidai lokacin daya lura da rayyan da kuma abdallah,najwa ce ta gaishe sushi kuma yaje tsakiyarsu ya zauna.

Abdullahi da rayyan ne suka mike suka ja safwaan dayake fadin ku barni na huta, basu bashi amsa ba suka nufi hanyar dakinsa,suna shiga direct safwaan bedroom yayi, suma suka bi bayansa, abdallah ne yace"safwaan wai nikam wannan najwan anya ba sonta kake ba,kallonsa yayi yace"auhh dama kai sai yanzu ka sani,to allah ya sawwake maka, shidai rayyan bai ce musu kala ba,safwaan ne ya dubesa yace"abbah ya fada muku wani week din zakuje court ko, gurin umman safna,rayyan ne yace"eah ya fada mana.

Safwaan ne yace"nidai ba zan samu zuwa ba saboda nan da jibi zan wuce fa, abdallah ne ya kallesa yace"wai yanzu safwaan dole sai ka bar kasar nan,safwaan ne yace"bazaka gane bane abdallah ni kaina banason barin kasar nan amma abbah ya dage yace"sai na tafi, da tini ma na tafi samu nayi a can akace an samu hutu kuma yau da dawowa kusan wata 2 yanzu dole na koma, rayyan ne yace"ai shikenan amma ya kamata fa ka tafi da aurenka,safwaan ne yace"to dan sarkin magana,ai sai na dawo za ai auren tinda amaryar tawa ta gida ce.

Sakina ce da abdallah suka fito yayin da rayyan da safna, suka dauki hanyar gidansu,safna ce ta kalli rayyan sai kuma naga ta sunkuyar da kai,rayyan ne yace"nikam safna lafiya kike najiki shiru, da alama zaman gidan ya miki dadi ko,batayi magana ba aai jin shassekar kukanta yayi,parking yayi ya tsaya yana kallonta, iya ganin fuskarta ya isa ya game me take nufi, dan haka matsowa yayi ya rungumeta yana bubbuga bayanta.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 38

Najwa ce ta baza kayan akan gado tana gani, dik yawanci irin dogayen riguna ne da takalma, sai hijabai ba mayafi ko daya,a ranta tace"to amma ya kai bai sako mayafi ba sai ya sako hijabi, a fili kuma tace"yo ni ina ma ruwana,hadda takalmi,wayar ta ciro daga leda kwalin infinix na hanga hot 50i,wani tsalle tayi, kamar yadda umma ta gaya mata ciro ta tayi ta saka ta a chaji tana cigana da kallon kayan.

Knocking din da akayi ne yasa ta fadin"shigo, umma ce ta shigo tace"to ai naga kallon kayan ya isa haka,zan fita ne ko zaki rakani, najwa ce tace"umma kije sai kin dawo nidai ina gida,umma ya safwaan yaushe zai tafi,umma ce ta dubeta tace"gidanku najwa ga zancej dana ke miki shi ne zaki dakko min wani can daban ko.

Murmushi najwa tayi tace"umma sai kin dawo allah ya kiyaye hanya,dariya ummar tayi tana kara kallon najwa a ranta tace"ohh yarinya mai hankali da sanin ya kamata,amma ta fuskanci kaddara, daga nan ta fice ta bar gidan.

Ganin magariba tayi sai da tayi sallah sannan ta fito zuwa kitchen,shiru tayi tana tinanin abinda ya kamata ta fara dafawa,sai kuma can naga ta janyo tukunya tace"kawai bara nayi jellop ya safwaan yana so, murmushi tayi ta dora pot din,tana cikin aikin ne taji kiran safwaan, ajiye kayan aikin tayi ta fita tana fadin"ya safwaan ka ganni,wata katuwar leda ce ya mika mata, da mamaki tace"ya safwaan wanannfa, zama yayi yace"mi kizo ki kar6a mana,murmushi najwa tayi ta kar6a tana zama kusa da shi.

Budewa tayi ta fara kallon kayan cikin,books, pens, biros,uniforms da komai dai da dan makaranta ke buqata ne a ciki,dagowa tayi yayin da hawaye suka zubo a fuskarta,ganin tana kuka tana kuma kokarin bude baki ne yasa safwaan fadin"aa karki bude min baki malama kawai ki min addu'ah allah ya bani abinda nakeso, yana mai kireta da idanu, bata iya magana ba har ya tashi ya bar wajen ya tafi ya zuwa dakinsa.

Kayan ta bari anan idan abbah da umma sun zo sai sugani,ta koma kitchen,a ranta take fadin"dama a rayuwa akwai kamar wadannan mutanen,umma da abbah bani da abinda zance muku a wannan rayuwar, tabbas kun cancanci komai daga gareni, idan nace komai ina nufin komai, daga nan taci gaba da girkinta.

Haka take girkin har ta kammala ta jera, tana zaune tana gyara wayarta safwaan ya fito yace"najwa kawo min black tea yanzu, sanannki hadomin da abinci na bazan iya sakkowa ba,har ta juya sai kuma yace"me kika girka ne,najwa ce tace"jellof din shinkafa,kinga karki kawo min abincin kawo min iya tea din kawai, daga nan ya juya ya koma sama.

Tana shiga umma da abbah suka shigo ganin ba kowa a falo ne yasa umma tafiya dakinta, shima abbah ya tafi dauro alwala, domin an fara kiraye kirayen sallar isha'i,safwaan ne ya fito ya tafi masallaci, najwa na can sai da tagama sannan ta fito da tray a hannu, direct dakin safwaan tayi da tray din,knock take jin shiru ta kuma ji kiran sallah anan tinaninta ya kawo kan ya tafi masallaci, dakin nasa ta je ta ahiye masa sannan ta fito da sauri, kasantuwar ta jiyo muryar umma.

Umma ce tace"ke yanzu najwa bazaki huta ba,yanzu ma sai da kikai girkin nan da kin barshi ai da ansha tea kawai,najwa ce tace"umma fa kadan nayi, umma da ace da ne da yanzu haka ina tsakiyar tasha raba abinci,umma ce tai shiru tana kara jaddada labarin najwa, daganan ta zauna nan fa najwa ta fara nuna mata kayan.

BAYAN KWANA 5 (After 5 days)

Safwaan ya tafi kasar Qatar yayin da najwa idan ta tafi school bata dawowa sai 6 kasancewar karatunta ya banbanta dana saura, gashi kuma dadin da dawa harda tahfix.

Najwa ce ta shigo tin daga falon ta fara wurgi da dan babban hijabin sai kuma naga ta zauna tana maida numfashi,fridge din gefe ta bude ta dakko ruwa,tsiyaya tayi tasha, sanann ta fara cire sauran kayan,wata dattijuwar mata ce ta shigo yace"najwa ya akai yau kika dadai ne, tin dazu sai shigowa nake naga ko kin dawo ki bani uniform din na wanke, najwa ce ta washe hakora tace"innah ki barshi sai gobe tinda kinga ai akwai wasu kuma kin goge su jiya, inna ce tace"aa yanzu dai tashi kije idan kin cire ki kawo min ina baya daga nan ta huce ta bar falon.

Abbah ne ya shigo da murmushi a face din sa yace"'yan makaranta,najwa ce tace"abba ina wuni ya gida, abbah sannu da zuwa, abba ne yace"yawwa ya karatun najwa,alhamdulillah abbah karatu ba dadi kam, sun rike min wuta basa barina na huta, gobe abba ba school amma wai kaji sai naje, za ayi baki kuma ni aka za6a a wanda zasuyi bayani a wajen,abba ne ya dubeta yace"najwa kuma zaki iya, naga baki dade da zuwa ba,najwa ce tace"abba zan iya mana wallahi abba karatu suke min kamar ba gobe, idan nayi magana suce ai yah safwaan ne ya basu umarni.

Murmushi abbah yayi yace"to ai shikenan a dage sosai kinji allah ubangiji ya baki sa'a 'yata, amma dai jibi kina nan ko,dariya najwa tayi tace"eaa jibi ina nan abbah, daidai lokacin da umma ta fito tana fadin' l"aa najwa sannu da dawowa, yaushe kika dawo ne,abba ne yace"yanzu nima na shigo na ganta tana cire safa,najwa ce tace"umma ina wuni ya gida, umma yanzu na dawo,umma ce tace"to tashi kije ki wanka yanzu zakiji an kira sallar magariba, tattare kayan najwa tayi sanann ta mike ta bar wajen.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 39

Yau najwa bata fita ba sai 7 tana fita taci karo da drivern da abbah ya ajiye mata yana jiranta,har ta kusa karasowa sai kuma naga ta dawo,kofar dakin umma ta tsaya ta fara knock umma ce tace"shigo a zaune ta ganta kan sallaya da carbi a hannu,najwa ce tace"umma zan tafi sai nadawo, umma ce tace"shikenan sai kin dawo kuma karki kuskura ki tafi da wayar nan,najwa ce tace"umma bazan tafi da ita ba tana daki ma, tana fadar haka ta juya tace"umma na tafi sai nadawo, da gudu ta fito daga gidan.

Uniform ne a jikinta very neat, skirt ce gown light blue sai riga, sai kuma wani dan karamin hijabi a jiki an rubuta AL AZHAR ACADEMY KADUNA, sai black cover shoe,tana zuwa tace"kawu mu tafi ko,sai da suka shiga sannan najwa suka gaisa nan fa ta fara zubo maasa surutu shi kuwa yana driving haka har suka karasa makarantar.

Yana sauka ta juya ta kallesa tace"yau da wuri zaka dawo karfe 2 insha allahu kawu,dattijon ne yace"to 'yata najwa, allah ya kaimu, tsayawa tayi sai kuma naga wasu' yammata su biyu wanda bazasu fita tsayi ba sun tsaya, najwa ce ta karasa tace"ya naga baku shiga ba,dayar ce tace"najwa ke muke jira wallahi,najwa cetace"yanzu ke Zainab sai kun tsaya jirana,bakin sun iso, an shirya komai ne,kafin ta kara magana wata katuwar mota ce ta fara jiniya, wanda ya saka zainab jan najwa tana fadin"khadeey zo mu shiga, daganna suka shige makaranta.

Gaba dayawajen masha allah mutane ne daban daban,daga 'yan makaranta zuwa' yan gari kowa ya zauna yana ganin yadda yara ke gabatarwa.
Chapter 22 · 0% Book details