Sashe 16
Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Katon littafin ya bude ya kalli alhaji gambo sannan ya kalli sauran al'ummar wajen yace"kamar yadda wadan nan dokokin suke, na farko shugaba zai bada yara guda 2 daga cikin yaransa, sannan dik abinda ya aikata kar ya kara tinaninsa ko kuma yayi ganganci kallon wanda yayiwa aikin,na 3 karya kuskura abinda ya faru shekaru masu yawa wanda ya aikatawa hakan ya dawo masa,na 4 kuma dole ne ya bada kyautar jini ga kowane dan kungiya domin zuwa dayi wa gunkin mu wankan jini, na karshe kuma shi ne mai muhimmanci, karya kuskura is koda wasa su hadu da wanda yayi wa tsafi ko sihiri idan ba haka ba a wannan ranar zai mutu.
Gaba daya wajen ihu ya dauka kowa na fadin"alhaji gambo sai kayi, sai kayi mai girma gunki yajaka daga nan har zuwa tsawon ran da alhaji dahir yayi, daga nan kuma aka tafi ciye ciye da kuma surutai.
Alkalamin
Queen Waleedah
*MAHAIFIN MU NE SILA*
*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_
QUEEN WALEEDAH
_HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇
*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*
*T.M.W.A.✍️*
✨✨✨✨✨
💪😊
*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*
✨✨✨✨✨
💪😊
https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F
Whatsapp Channel
💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.
Page 27
Tin bayan sallar asuba daya fito yayi sallah ya zauna yana kallon awannan kurar, yayin da gari ya fara sha ne a take wannan kura ta zabura ta mike, cikin wani irin yanayi ta fara gurnani hadi da fitar da wani hawaye daga cikin idanunta, abinda ya bawa safwaan mamaki kenan a take a wajen ya fara karanto kowace irin addu'ajh da take fitowa daga bakinsa, a lokaci daya gurnanin ya tsaya, bude idanunsa yayi a take yayi tozali da najwa tana kuka.
Hakan ne ya basa damar karasawa wajenta,dagota yayi, yayin da ta tafi zata fadi yay saurin riko ta, jijjigata yake amma shiru, da sauri ya ajiyeta ya fita zuwa tsakar gidan, sai kuma ya dawo ya shiga kitchen, cup ya samu ya debo ruwa sannan ya shiga tofa ayatulkursiyyu a ciki, sai da ya gama sanann ya fara shafa mata a fuska,firgigit ta dawo tana fitar da numfashi.
Kallonta safwaan yayi yace"sannu gyada kai kawai tayi,sai kuma yace"kije ki wanka sai kiyi sallah, rike baki tayi ita har ta manta rabon da tayi wanka ma, dan haka yana nuna mata bandakin ya huce ya fita daga gidan,bandakin ta kalla da kyar ta hangi bokitin hakan yasa ta janyo, murda kan famfon tayi a take ruwa ya zubo, sai da ta cika shi tsaff sanann ta fara kokarin wankan.
Bata dade ba ta fito tayi sallah, sannan ta zauna a kan sallayar tana duba hijabin da ga gani, a ranta tace"ko ina safwaan ya samo hijabi kuma, batasan akwai hijabi ba a gidan, sai kuma ta furta"ya allah meyasa yau nafijin azaba akan kowace rana, meyasa yau naji ni da zan koma mutum kamar ana ciremin wani abu a jikina, shiru tayi jin motsin safwaan, hakan yasa ta saurin kwanciya da rufe idanu kamar mai bacci.
Safwaan ko da ya shigo yaga tana bacci kayan ya ajiye a kan kujera sanann ya shiga bedroom din daya kwana a ciki,sallayar ya nade ya maidata cikin wardrobe, sannan yaja towel ya shige bandaki.
Najwa ce ta tashi ta kalli ledan,kamar wata mai Hannun mayen karfe haka ta bude ledan, ganin doguwar riga mai kyau tayi, hakan yasa ta saurin dauka da sakawa hadi da daukar dan karamin mayafin ta saka a jikinta,tsayawa tayi tana kallon kanta, domin ita kam abin har mamaki yake baya yau ta saka sabin kaya.
Ba 6ata lokaci yana fitowa yaga ta saka kayan, a ransa yace"ai kam kayan sun miki kyau,sai kuma ya tahio ya janyo ledan, kallon yayi yace"zo ki break sannan mu tafi ko, tsayawa tayi ita dai batasan me yake nufi ba, amma taga ya bude abinci hakan yasata gane cewa ashe abinci zasu ci.
💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮💮
Safna ce ta mike daga baccin da take,sai kuma naga ta janyo akwati,tanayi tana dibar kaya hadi da zumburo baki, rayyan yana daga toilet, yace"baby safna bani towel, banza tayi dashi,jin bazata bashi ba ne yasa shi kokarin zuro hannu da jan towel din.
Fitowa yayi yana kallonta, abin ma dariya ya basa amma ya kanne yace"ke kuma ina zakije,ta6e baki tayi tace"gidan mu mana, ko ina da wani gida dayafi namu ne, rayyan ne yace"kina dashi mana tinda ga gidan mijinki uban 'yayanki ba.
Dan karamin tsaki taja, taci gaba da zuba kayanta,rayyan bai hanata ba domin yasan ba hanuwa zatayi ba, sai da ta gama komai sanann ta juya ta kallesa tace"bani takarda ta, dsn wallahi yau sai ka sakeni, maimakon yaji haushin abin, dariya yayi yace"to kije gidan anjima zan kawo miki takardar insha allahu,ko kallonsa batayi ba ta fito daga gidan, tana yi tana murmushin samun nasara, yayin da rayyan a daki ke wani killer smile da shi kadai yasan mai yake nufi.
Tana fitowa ta tari mai nafef ta shiga, unguwar da zai kaita ta fada masa nan suka fara tafiya,sun danyi tafiya sanann Yazoo inda zata sauka,jakarta ta cire ta mika masa kudin, sai kuma naga ta tsaya tana kara kallon gidan nasu, knocking ta fara,gate man ne yace"ima zuwa,bai dade ba ya bude mata, da mamaki karara a fuskarsa yace"hajiya safna lafiy dai ko.
Cike da tsiwa tace"daba lafiyan ba ai da bazaka ganni anan ba, kuma naga ai gidan uba na ne ina da ikon da zan iya zuwa a dik lokacin da naga dama, ko kuma nace a lokacin da nayi niyya, fuuu ta huce, gate man dariya yayi yace"haba safna bani na kar zomon ba rataya aka bani.
Ameenatu ce zaune tana fadin"yanzu abba daka barta ta tafi yashe zakaje ka dawo da ita,abbah ne ke kokarin daga waya yace"ameenatu ba wanann zancen ba, indai yarinyar nan ta kuskura ta dawo ni da ita ne, aminatu ce tace"aa abbah ba haka za ayi ba, ka kyaleta a biyo mata ta inda bata yi tsammani ba, ba zaman gidan take so ba ka kyaleta kawai ka barni da ita dan allah.
Daidai lokacin da abba ya daga waya yana fadin"karka damu kawai ka kyaleta, zaka iya shiryawa ka tafi idan kaje ka gama ayyukanka sai ka dawo ka dauki matarka, badai sati 2 zakayi ba karka damu,kallonsa umma tayi tace"to ka gani ka kyaleni da ita, daidai lokacin da safna tayi sallama ta cuso kai.

Page 28
Wani mugun kallo abba yayi mata, a lokacin ne tasha jinin jikinta, domin ta sani a iya tarihin rayuwarta indai abba yayi mata irin wanann kallon to akwai abinda zai biyo baya, kallon umma tayi da a lokacin tayi murmushi tace"aa safna kece lale marhaban da autan gidan nan,a lokaci gida kuma taji wani sanyi a ranta, tinda ko ba komai ita bata bi ta da kallon sharri ba.
Jin wayarta ba kara hakan yasa ta janyota daga jakan ta kall, ganin umma yasa ta dagawa tana fadin"hello umma kina ina ina cikin gidan, daidai lokacin da abba ya mike ya zabga mata mari, sanann ya daga zai kara amintau ta shigo tsakani, ta fara hadasa da allah da annabi,kallon safna yayi sannan uace"ki bani wayarki tin kafin na miki illah, jiki na rawa ta ta mika masa.
Kallonta yayi yace"sam safna kinji kunya wallahi, karki manta kin girmi sakina, amma sakina tayi zamanta ke kin kasa, kodan ba komai bane illa huduvar uwarki, to ita kanta uwar taki bata gidan, itama ta tafi nasu gidan, dsn haka indai gida ne ki zauna gaki ga shi nan, kuma wallahi koda wasa naji ance kin saka kafarki a waje, to ki tabbatar da cewa ni da ke ne, dan bazaki maidani mutumin banza ba, ki zauna har kiyi iddah tinda haka kika za6a, shashashar banza.
Wuceta yayi, ai da gudu ta huce ciki ta bar akwatin tata a wajen,dakinta ta shiga ta fada kan gado,kuka ta ke bilhakki da gaskia, shikenan yanzu, shikenan ta kare min, ya hanani ganin sanyin idaniya na, wayyo sadeeq, shikenan sadeeq, sadeeq ka jirani zanzo gareka, haka umma taje kai mata akwatin taji tana wannan kalaman.
Umma ce tace"haba safna, saurin dakatar da ita safna tayi tana fadin"koma menene ai kece kikaja, kuma ko ma menene ke kika saka abba ya saki mama, kuma wallahi baza ta6a yafe miki ba,kuma karki saka ran cewa zan daukeki a matsayin uwa dan ni bazan iya hakan ba,umma ce tai murmushi ta tashi ta fita daga gidan.
Baya da kamar mintuna 30 a zaune na ganta ta zabga tagumi,a ranta ta furta fitar ma da nake kokarin yi an hanani, to wai me abba yake nufi da ni ne,sai kuma tace"wallahi kome za a yi sai dai ayi, dan ni bazan iya zama da rayyan ba eheee.
Karfe 2 motar su ta sauka a kaduna, daga nan taxi suka shiga sai da safwaan yazo unguwar su, sanye yaje da kana nan kaya, bakake ya saka wata p cap data boye fuskarsa, ita kuma najwa sanye da hijabi da riga doguwa,jin unguwar shiru hakan yasa shi jan hannun najwa yace"kinga wanann gidan kiyi Knocking kice kina neman najwa, najwa ce ta kallesa ta kalli gidan tace"nan ne gidan ku, gyada mata kai yayi.
Knocking tayi, yayin da mai gadi yace"wacece, najwa a hankali tace"kawar safna ce, dan allah tana nan,bude mata yayi ya kalleta yace"ke kece kawar safnar,hade rai tayi tace"eaa ni ce kaje ka fada mata nazo,to mai gadi yace"sai kuma yace"amma wane suna za a gaya mata,cikin dan karamin lokaci tace"nabila, haka kuwa akayi ya huce ciki.
Najwa ce ta juya ta kalli safwaan tace"ya shige fa ciki,safwaan ne yaja hannunta suka shigo gidan sannan ya rufe kofar, kafin mai gadi ya dawo yabi da bayan gidan.