← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 31

Sashe 5

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can kuwa gombe, a tsakiyar wani katin daki, wani mutum ne shi ba fari ba kuma zaka kirashi baki ba, sanye yake da wani bakin gajeren wando, lokaci guda ya saki wata muguwar kara yana fadin"no karka min haka, bayyanar wasu bakin halittu ne yasa shi yin shiru da bakinsa, sun kasanxe mutane ne amma kuma su wadan nan irin katon kai ne dasu, cike da wani irin kalami suka kallesa, dayan ne yace"Gambo ka sani dama 1 ce ta rage maka idan ba haka ba k sani taka ta kare, iya tsawon kwanaki 239 gareka idan har baka bayyana yarin yar nan ba, to ka sani sai dai muce ka zalunci kanka, daga nan kuma suka 6ace.

Cike da bakin ciki ya fara kiran kin cuceni nasan aikin kowaye wanann, dole haka ya fiti daga dakin jikinsa dik wani jan abu, sai da nayi gaba sosai sanann naga ashe jini ne, gana daya zama yayi akan gadon dakin yana huci kamar tsohon zaki, can kuma ya mike ya fara tattara kaya a akwatu, kamar daga sama naji ana Knocking.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 7

Wata mata ce fara bazaka ce mata kyakkyawa ba, ba dan ma arzikin farin ba da bazance mata da farar ba, kallonsa tayi tacr"haba alhaji wanann wane irin abu ne taya zaka fara harhada kaya, wani kallo ya wulla mata yace"kinsan kwanaki nawa suka bani akan na kai musu ita kuwa, saura kiris aikina ya cika amma ban taya akai ba ta dakatar da hakan, a yanzu haka saura kwana
239 wa'adina ya cika, a hankali tace"amma naga ai akwai wani za6in ko, kallonta yayi sai kuma ya tofar da yawu yace"za6in nasu idan har nayishi ki sani maimaikon nayi gaba baya zanyi sai dai idan zan cika wa'adin su, to ka cika mana ta basa amsa kamar ba ita tai maganar ba.

Kallonta yayi yace"wai mufeedah ke kamar baki da hankali kinsan kuwa me kike fadi idan har hakan zata kasance sai na basu guda 20 ta ina zan samo ne, murmushi tayi tace"zan samo maka su nikuma, murmushi yayi sai kuma ya zauna yace"tayaya zaki samo idann har kika samo shikenan nasan zan kara matsayi amma ni kuma ita nake hari yadda zan zama shugaba a cikin su.

A hankali tace "zaka zama ai amma yanzu maimakon ka tafi neman waccen halittar kuma kazo kayi ba wan ba kane, a yanzu abinda yafi maka sauqi shi ne kasan yadda zakayi ka kara matsayi, daga baya sai ka san yadda zakayi ka nemo wannan halitta, shiru yayi sai kuma yayi murmushi yace"mufeeda ashe kina da hankali bansani ba, ashe kinsan me kike, kai amma kin birgeni, shikenan yanzu sai ki fadan inda zan nemo wadan nan yara, murmushi mai sauti tayi tacecka barmin komi a hannuna amma akqai fidda kudi.

Dan karamin tsaki yaja yace"kin sani kudi ba matsalata bane nidai na cika muradina shi ne kawai dik wani abu dazai biyo baya mai sauki ne inda har buqata zata biya, wata kofa ya bude sai ga uban kudi cikin dollars, murmushi tayi tace"ba wannan nake magana ba, zaka bada million 200, tsaki yaja yace"cash ko transfer, batare da tayi magana ba ta mike, sai da taje bakin kofa sannan tace"transfer daga nan zuwa jibi buqatarka zata biya.

Bayan awanni 8 najwa ke fara tari a hankali, gaba dayansu suna zaune suna jiran ta farka, jin tarinta ne yasa su saurin motsawa daga wajen suka nufi wajenta, da kyar ta bude idanunta wanda sukayi jajawur, kallon mahaifiyar ta tayi sai kuma ta kalli sauran kannen nata, malamin ne ya taso da wani rubutu a hannunsa, zainabu yayi alama da ta d'agota, a hankali ta dagata ya fara bata ruwan rubutun,sai da tasha sai kuma yace"yarinya karki kwanta zauna da kanki, zama tayi tana kallon tsohon mutumin.

Zainab ce ta fara masa godiya sai kuma ya dakatar da ita da fad'in ba godia zakiyi ba, addua zakiyi ga mahaliccinki wamda ya bata ikon farfadowa, sannan kuje waccen bukkar ya nuna musu wata yace"kuje ku kwanta da safe kya bani labarin naku, domin kuwa tabbas akwai wani babban lamari a jikin wannan yarinyar taki, daga haka ya juya su kuma suka mike suka tafi bukkar.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 8

*Kaduna State*

Wani katon gida ne a tsakiyar unguwar wanda kallo daya ya isa ya tabbatar da cewa eaa ba laifi gidan akwai wato arziki ba,tinda ga falon nake jiyo sautin karatun alkur'ani kasa², hakan ya tabbatar da cewa gidan suna riko da addini, a falon gidan ba kowa hakan yasa na fara dudduba sauran dakuna nan, wani daki. Daya na bude turus nayi ina kallon saurayin dayake ciki ya zabga tagumi yana kallon papern hannunusa, yayi nisa sosai hakan yasa na karasa wajen sa na leka takadar, kyakkyan zane ya kasance ba fuska sai dai an fitar da shape na fuskar.

Kyakkyawar budurwa ce dik da ba face amma hakan bai hana fitowar zanen ba, kasancewar zanen ya fita, a fili nace"to wannan ko dai yana yin zane ne, kallon gefen dakin nayi hakan ya tabbatar min da cewa tabbas yana zane domin kuwa ga kayan zanen nan a gefe daya, sai kuma gefe wani room.

Jin ana kokarin shigowa n yasa na kalli door dun, wata dattijuwar mata ce ta shigo taba kallon yanay8n dakin sai kuma ta kalli yaron tace"safwan lafiyarka kuwa tin dazu abbah ke jiranka zakuje wajen karatu amma kai kana nan kana kallon takarda,karasowa tayi sai kuma tayi turus ganinsa da takarda a hannunsa.

Safwan! Safwan!! Safwan!!!

Firgigit ya juyo yana kallon matar sai kuma yayi saurin ajiye takardar yana mai mikewa da daukar hula, sai a lokacin naga sanye yake da shadda blue sai sheki takeyi dinkin ya zauna a jikinsa sosai,kallon matar yayi yace"umma na shirya dama lokaci nake jira yayi kuma naga yayi ma, yanzu zan fita, har ya huce ta janyo sa ta dawo dashi.

Zama tayi a hankali shima ya zauna yana kallon nata, cike da tsantsar kulawa tace"safwan har yanzu kana mafarkin ne, kallon mahaifiyar tasa yayi ya gyaɗa kai alamun eaa. Da mamaki tace"kuma addu'oin dana baka kanayi kuwa,a hankali cikin wata sanyayyiyar murya yace"umma inayi kullun sai nayi har da wanda abbah ya bani inayi amma umma ko yau sai da na ganta a mafarkina.

Umma abinda yake bani mamaki shine har yanzu na kasa tantance fuskarta, sai dai kullun tazo tana kuka wani lokacin kuma tana ce min na taimaka mata, umma har tsoron kwanciya bacci nakeyi, kallon yaron nata tayi ta jinjina kai sannan tace"shikenan tashi kaje yana jiranka, daga nan ya fita ya barta a zaune.

Tinda ya fita ta zauna tashi tayi tana zagaye dakin, sai kuma ta tashi ta fita daga dakin ta koma falo ta zauna, gidan ba kowa, tana nan zaune wata yarinya ce ta shigo tana dariya, kallonta matar tayi tace"safna wai meyesa ke baki da hankali ne kiyi sallama sai dai ki shigo kina dariya ke kamar ba musulma ba, gani nayi ta kalli matar ta murguɗaa mata baaki,sannan tace dariya ma iya cew dik wamda ya iya yayi.

Dafe kai tayi tace"inalillahi wa inna ilaihi raji'un, tabbas allah yana jarabtar bawansa, yanzu kalli rayuwar wannan yarinyar yanzu kai zaka kalli wannan kace wai 'yace ga malam, malam me tsoron allah da taka tsantsan, da bin tafarkin annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wassalam.

Tana cikin wannan maganar wata jibgegiyar mata ce naga ta fito tana fadin, to uwar' yan surutu wadda bakinta bazai fadi alkhairi ba, indai rayuwar safna ce nan gani nan bari kuma safna 'yata ce, ke kije kiji da wanann mahaukacin dan naki da yabi ya takurawa kansa ya hadu da wani irin bala' i na ganin mata a mafarki.

Dik da sallamar da akayi ba shi ne ya hanata yin magana ba, wata yarinya ce zata kai sa'ar yarinyar dazu wato safna, kallon matar tayi tce"ummi meye hakan dan allah,cikin hade rai tace"sakina ki rufe min baki ko sai na babballaki, kin za6i uwar wani kin barni ko, to kije kici gaba indai zakina zama da wanann wataran sai kinyi dana sani, dik wannan abi umma batace da ita komai ba sai ma tashi tayi ta nufi part din ta, sakina bata bi ta kan ummi ba tabi bayan umma.

____________-----------------__________

A tsakiyar wani karamin kauye nagansu, zainabu ce ta ga wani dan saurayi bai fi sa'an fahad din ta ba, hakan yasa ta kwala masa kira kamar haka"kai yaro dan allah zo mana, karasowa yayi kallonsu yake, zainabu ce tace"dan allah idan bazaka damu ba gidan megari nakeson ka kaimu, ba tare da 6ata lokaci ba yace"ku biyoni tafiya suke, yayin da dik inda suka wuce kallonsu akeyi.

A kofar gidan maigari yaron ya tsaya yace"nan ne gidan me garin, daga nan yasa kafa ya fice ya barsu, karasawa sukayi gaban maigarin, bayan sun gaisa ne zainabu tace"ranka ya dade, dama mu 'yan cirani ne, so muke mu samu gida mu zauna, zuwa lokacin da zamu kuma kara yin gaba, maigari dattijon arziki ne, ba tare da wata matsala ba ya umarci daya daga cikin yaransa akan a kai su gidansa dayake kudu da gari, amma fa daga shi ba wani gidan, zainabu tace"bakomai shima yayi, daga nan bayan wasu zantuka aka kaisu gidan kamar yadda mai gari ya fada.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊
Chapter 5 · 0% Book details