← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 31

Sashe 19

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadin hakam da fahad yayi yasa nabila mikewa tana jan hijabinta da yake jikin igiya, nan suka fita daga gidan,sallamar da ake kwadawa ce a kofar gida yasa zainabu jan mayafinta ta leka,yaran mai gari ta gani dan haka tace"lafiya dai ko,yaran ne yace"lafiya qalau dama malam ne yazo akan maganaar najwa, shi ne mai gari yace"azo a kiraki,zainabu ce tace"to kaje zanzo yanzu, daga nan ya huce.

Da kamar bazata je ba kome ta tuna sai kuma naga ta tafi, tana tafe tana kallon yara jefi jefi kasancewar ba makaranta yau asabar,har ta karasa fadar mai gari,bayan sun gama gaisuwa mai gari ne ya kalli zainabu yace"dama akan maganar malamin da zaiwa najwa magani ne sai yau muka samo sa,zainabu ce ta kallesa tace"to ni yanzu ranka ya dade ina ma naga najwar, bare har na saka ran za ai mata magana.

Ranka ya dade abinda yafi kawai shi ne a hakura da batun najwa haka, na tabbata bazata ta6a fadawa hannun bata gari ba,malamin me yace"eh gaskiyar ki baiwar allah a hakura a fawwalawa allah komai, mu namu kawai addu'a ne da kuma allah ya bata lafiya,bayan sun gama maganar ne mai gari ya sallamesu suka wuce.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

Habiba ce ta kalli abbah tace"dan allah abbah ka taimaka wallahi bani na saci abin da ake tuhumata da shi ba, sawun barawo na taka, abbah ne ya kalleta yace"lalle habiba na tabbatar da cewa baki da hankali, yau na kara tabbatar da cewa kwakwalwarki tayi tsatsa da kika tashi tafiya kin nemi izini na, yau kwananki 12 baki gidan nan.

Aa ga surajan mahaukata bansan me kikaje kika dakko ba, saboda ni soko ni sai na shiga maganar hukuma ko, to wallahil azeem badani ba, officer's ku tafi da ita taje tayi muku bayani,kunga tafiya na, zazzagewa yayi tare da yun cikin gida,nan habiba ta zube a kasa wayyo allah na shiga 3 ni habiba,tabbas na cuci kaina yanzu ga inda halina ya kaini, kallon safwaan take da rayyan da kuma abdallah, da suma ita din suke kallo.

Haka suka juya suka shiga motar su suka koma zuwa charge office din su,baya da kamar mintuna 30 dpo ne ya shigo ya kallesu yace"wanann matar ba nace kuje,sai kuma yayi shiru, daya daga cikin officern ne yace"yallabai munje inda tacce muje, shi kuma ya nuna ba ruwansa dik hukuncun daya kama ayi mata kawai shi bashi da tacewa,dpo ne yace ok to ku cike mata F. R. I sai mu huce koto,gaban habiba ne ya yanke ya fadi, sai wani marayan kuka daya kwace mata.

Ko kallonta dpo bai yi ba, bare sauran officers din daga nan kuma ya huce ya bar office din ma gaba daya.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

Mutane 3 ne a gefe daya sai kuma wasu guda 5 a dayan gefen,yayin da gambo ke tsaye dagashi sai boxer, wani katon kwano ne an cikashi da ruwa, wannan mutane 3 ne suka masa alama daya shiga, ba 6ata lokaci ya shiga take suka masa siddabaru ya koma ja jawur.

Sai da aka yi haka sau 3 a na 3 ne kuma ya koma baki kirin, a take wata magana ta fara bayyaana, tana fadin"hahahaahaaa ya kai gambo dan gidan Sabitu,dan daya gagari rugarsu, wanda ya bamu uwarsa da mutanen rugarsu wanda sunfi su 50, a yau ga sakamakon aikin ka nan,a yau ka zama shugaba, sannan kuma mai kula dani da bani dik abinda na buqata, a yau komai zai dawo hannunka, komai kakeso a yau zai dawo.

Wata kara ce ta bayyana sai kuma wani bakin hayaki daya ke fitowa daga saman dakin yana sauka cikin jikin gambo, wanda shi kuma ke babbaka dariya, anan kowa ya dauki dariya na dakin, baya da kamar mintuna 20 ne nan dakin ya fara girgiza.

Wata shakakkiyar murya ce ke furta, ka zama shugaba, karkai tinanin shugaba mai adalci, aa shugaba mugu wanda sam baya adalci, shugaba wanda idan aka karya doka dole ya hukunta mutum, jeka ya kai gambo dan sabitu, kaje ka mulki al'ummar wannan kungiyar ta matsafa jeka sai kuma wajen yayi shiru kowa na kallon gambo.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

Magariba ce tayi a wannan lokacin aminatu da su safna sun kusa gari,najwa kallon jikinta takeyi domin yau kadai jikinta ya mata dadi, ta daina jin zafi a jikin ta da kuma cikin jikinta.

Dai dai lokacin da motarsu ta shiga gidan,safwaan ya fito zsi shiga masallaci, kin shiga tyayi ya tsaya yana kallon motar, sai da ta gama parking da gudu safwaan ya karasa ya rungume umma, anan dai na gane sarar sa ce gudi idan ya dade bai ga abu ba.

Sakinta yayi ya kalli najwa da ta kara canja masa, ga wani kyau da tayi, ga jikinta ba laifi ta kara kiba, gaba daya ya shagala da kallonta,safna ce tace"yah safwaan ina wuni, hankalinsa na kanta yace"lafiya loa, yayin da najwa ta sunkuyar da kanta, umma dai ganin ba kunya a lamarin safwaan gashi har an fara tada sallah yasa ta janye najwa, hakan ne ya sashi dagowa yana sosa kai, umma ce tace"wuce ka ban waje, mara kunya kazo ka kafeta da idanu ko, murmushi yayi yace"toh umma ayi hakuri naga dai ai sai kuma ya tafi yana murmushi.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 33

Abba bayan an idar da sallah isha'i ya shigo, yayin da safwaan kuma ya tsaya wajen su abdallah a garden,abba ne ya kalli najwa data tsugunna ta sunkuyar da kai, a hankali yace"najwa jikin naki da sauki ko, yanzu ya kikejin jikin naki, najwa ce tace"abbah alhamdulillah da sauki, abbah nagode da dawainiya dani, dik da kansancewar bamu hada komai ba amma kun min taimakon da bazan iya biyanku ba,sai dai na muku addu'ah da fatan gamawa da duniya lafiya.

Abbah da umma ne suka amsa da ameen, yayin da umma tace"haba najwa kin mana abinda bazamu ta6a iya biyanki ba,saboda kin ceci safwaan da ba dan kin isa inda yake ba, na tabbata da tini ya mutu yanzu, amma yanzu ki duba ta sanadinki yake rayuwa,murmushi najwa kawai tayi ta wasa da yatsunta.

Sallamar safwaan ce yasata dagowa ta kalli umma tace"umma zanje daki na,yayin da safwaan idanunsa na kanta,umma ce tace"to shikenan kiyi addu'a sannan kisha maganin ki kamar yadda malam yace, najwa ce tace"tohm umma abbah sai da safe, daga nan ta tashi ta bar fakon, dik da safwaan bai so hakan ba amma ba yadda ya iya dole ya zauna suna ci gaba da tattaunawar.

Safna ce ta dafe kai tana tinani nasihar da malam yayi mata, safna nasan ke mai hankali ce dik da nasan da kin sani amma zan kara tinatar dake kamar yadda ubangiji mai girma da buwaya ya fada a cikin littafin sa mai tsarki wato alkur'ani “Da zan umarci wani ya yi sujada ga wani, da na umurci mata su yi sujada ga mazajensu.”

Allah ya ce:

> “Kuma ku zauna a cikin gidajenku, kada ku bayyana kamar yadda jahiliyya ta farko ta bayyana.”
(Surah Ahzab: 33)

Manzon Allah (SAW) ya ce:

> “Mafi alheri daga mata ita ce wacce idan mijinta ya dube ta, sai ta faranta masa rai...”
(Ibn Majah)

Hakkokin miji suna da nauyi a kan mace, kamar yadda ita ma take da nata hakkokin. Auren Musulunci gininsa a kan adalci ne, jinƙai da fahimta. Idan kowa ya san hakkin dan uwansa ya kuma cika shi, za a samu zaman lafiya da albarka a rayuwar aure.

Safna ce ta lumshe ido tana kwanciya akan gadon dayake dakinta,tayi shiru sai ka rantse bacci takeyi amma idanta 2 ba bacci take ba.

Najwa ce kwance ta runtse idanunta tana tina abinda ya faru sati 1 daya hu e a gidan malam adam,sai kuma naga hawaye ba bin kuncinta,kuka take sosai kama wadda take kewar wani, kodan ba shakka masan tana kewan ahalinta ne.

Abbah ne yace"yanzu abinda ya kamata sai a nemi makaranta a sakata,umma ce tace"eaa nima nayu wannan tinanin amma ai ga safwaan nan shi zaiji da komai,shiru abbah yayi sai kuma ya kalli aminatu yace"idan kin gama inason ganinki, mikewa yayi ya barsu tare.

Yana fita safwaan ya matso yace"umma wace makaranta kuma, nidai umma a ganina kawai ku kyaleta a nemar mata malamin addini amma ki dubeta kiga fa, tin tana primary rabon ta da makaranta, umma ce ta kallesa tace"gidanku safwaan dan gidanku ai dole a nemi makaranta ko ta manya ce a kai ta,da yamma sai ana mata karatun islamiyyar, safwaan ne ya turo baki ya tashi ya huce.

Umma ganin ya huce ita ma mikewa tayi ta kashe fitilun dakin sanann ta rufe kofar bayan addu'o'in neman tsari sannan ta shige zuwa falon abbah.

Safwaan ne na gani tsaye a bakin kofar dakin najwa yayi tsaye yana kallon kofar dakin, yayin da wata zuciyar ke fada masa ya shiga, wata kuma na hanass ya shiga, dakyar ya iya janye kafarsa ya tafi ya zuwa dakin sa, ya lalla6a zuciyarsa ya huce zuwa dakinsa.

Umma ce ta kalli abbah da yake hada takardu tace"wai nikam abbah ya batun habiba, tsawon sati 1 baka je ba, kuma kasan da tafiyar ta ma an kusa sati fa,bai juya ba bare ya kalli aminatu yace"ai habiba ni bansan me yake damunta ba amma ki bari zuwa safiya zamu tattauna, yanzu nidai bacci nakeji, kashe fitilan dakin yayi ya koma ya kwanta hadi da yin addu'a.

***********************

Alhaji gmbo ne zaune akan wata karagar mulki wata kujera ce makekiya, wanda da za a dagata tabbas da sai an hada majiya karfi,yayin da kowa ya mai da hankalinsa kanta yana kallonsa,wasu 'yammata ne a gefe sanye da wata bingilalliyar riga iya gwiwa,suna kai wa da komowa.
Chapter 19 · 0% Book details