← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 31

Sashe 27

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwaan ne yace"nasan ai kinsan da maganar auren mu ko,kuma nasan kina tinanin cewa zakiyi wa umma bayani saboda ba sonki nakeba.

Najwa ki sani tinda allah ya hallicceni ban ta6a son wata ba bayan mahaifiyata da abbah kamar ke, najwa kece nutsuwata, najwa kece komai nawa, haka kuma kece kwarin gwiwa ta.

Najwa ce ta dago ta kalli safwaan wanda yake magana.

Safwaan ne yace"eaa najwa kcece kwarin gwiwata,a lokacin da ina qatar ma najwa videon ki nake gani na school da ake dorawa a net su ne suke sakani na kara zabura na kara zage dantse nayi abinda ya dace.

Najwa to ki duba kigani a yanzu ta dalilinki mai na zama,najwa yau zan furta miki kalmar dana dade ina boyemiki, kalmar da nasan cewa maza da yawa sun furta miki ita kafin ni.

Najwa bansan tayaya zan iya bayyana miki tsantsar son da nake miki ba amma nidai nasan ina sonki har rananr da numfashi na zai bar gangar jikina.

Najwa You Have long been a secret in my heart, but today, my heart can no longer hide you – I must tell you the truth it holds inside.Every night, my thoughts pause at you. I’ve loved you in silence for so long, but fear always stopped me from speaking the truth.I could string together a hundred words, but not one could truly express how I feel about you. You’ve been my dream, my hope, and my desire since the day I first saw you."There was a day I remained silent, even as my heart called out loudly. But now I’ve realized love doesn’t need silence – it needs honesty."I can’t say I just fell in love with you today, because this love has been building a home in my heart for a long time. You’ve become a part of my thoughts—even in my dreams.I waited so long for the right moment, but now I know there’s no better time than now to say this: I love you more than words can ever express."If loving you is a crime, then I’ve been guilty for a long time, secretly loving you. But today, I want you to be the special one—my heart’s moon."You are the only woman my heart beats for. I don’t know how you’ll take this, but I hope you understand that this love is real—pure and full of good intentions."My life doesn’t feel complete without you. I’ve kept this feeling buried for so long, but now that my heart is overflowing, I have to tell you: You are the happiness I’ve been searching for.My heart has held onto a secret for years with your name written all over it. But today, I want you to read that heart yourself, and see how brightly your name shines in it."

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 47

Najwa ki yarda dani ki karbi soyayyata I LOVE YOU SO MUCH.
Bazaki san ya nake ji ba sabods zuciyata ba ajikinki take ba amma najwa ya kamata ki karbi soyayyata ko na samu nayi bacci a rai ba tare da tinanin komai ba.

Najwa ce ke kallonsa yayin da hawaye ke zuba a idanunta,matsowa tayi hadi da rungume safwaan wanda shima hawayen yake zubarwa.

Safwaan tsam ya rngume najwa ajikinsa yayin dayake fitar da wani numfashi wanda daji kasan na kwanciyar hankali ne sabanin dazu da yake gurnani.

Najwa ce ta fara janye jikinta daga nasa,hannunta ya rike hadi da fito da wata kyakkyawar zobe an saka s&n a jiki ya zura a hannunta yan akara kallon face dinta wadda ta sunkuyar dakai.

Safwaan ne yace"najwa kina sona kenan,shiru tayi tana kara kallon zoben tana shafawa,a hankali ta dago zoben tana kallo hadi da sumbatarta,da mamaki yake kallon abnda ke faruwa sai kuma yayi murmushi ya mike yace"ki kwana lafiya kinji ki tashi da wuri gobe domin a goben nan zan cika miki burinki da kika dade kina fata najwa, daga nan ya fice ya barta.

Sai da ta rufe sannan ta juyo tan adafe kirji, a rabta tace"dama ya safwaan na sona haka amma ni bansani ba,gaskia rashin sani yafi dare duhu, to amma meyasa baya kirana lokacin daya tafi Qatar.

Sai kuma tace"to kodai saboda baya son ya takuramin ne,murmushi tayi hadi da hayewa kan gadon tana jan bargo yayin da baccin ma yaki zuwa tana tina movement din ya safwaan.

A bangaren safwaan ma baccin kasa zuwa yayi yana kara tina yadda yau ya fadawa najwa irin yadda yake sonta da kuma rungumar datayi masa,a haka wannan ruhina suka ci gaba da tinani har sai da bacci barawo yazo ya sace su.

Tin asuba ba wanda ya koma bacci shiryr shirye kawai suke, yayin da najwa ta shirya kayanta a akwatu har yanzu ta kasa mantawa da maganar yah safwaan.

Karfe 7 daidai wata katuwar motace kirar jeep ta fito bayan saka kayan sai kuma umma da najwa suka shiga baya sai abbah da safwaan suka shiga gaba yayin da safwaan ne ke tuki,amma rabin hankalinsa yana kan najwa wadda take danna wayarta.

A ransa yace"ba wanda ya gaya miki inda za aje sai dai kawai ki ga mamanki yau, daga nan yaja motar suka bargidan suka dauki titi.

Tinda suka fara tafiya ba wanda yace uffan,yayin da najwa ta kwanta a jikin umma tana bacci,karfe 11 suka shiga garin katsina,yayin da safwaan bai manta sunan kauyen nasu ba,tafiya suke yayin da karfe 2 suka iso cikin kauye kasancewar hanuar bata da kyau ga kuma kasa a wajen.

Sai a lokacin najwa ta farka da salati ta farka tana yi tana kallon garin ta tagar mota,safwaan ne ya fita daga motar bai dade ba ya dawo yace"abbah sai mun danyi tafiya zuwa can lungun.

Tin daga bakin lungun safwaan yayi parking yayin da al'ummar kauyen suka fito suna kallon katuwar motar data faka a kofar lungun da tsakar ranarnan.

Gaba dayansu fitowa sukayi suna kokarin shiga lungun,yayin da najwa ta na kokarin tino inda ta san garin amm kwakwalwarta taki bata hadin kai.

Nabila ce tazo giftawa abbah ne yace"yarinya inane gidan zainabu,anan take kirjin najwa ya buga yayin da take ganin wanann budurwar yarinyar kamar ta santa,ita kanta nabilar sai da ta kare musu kallo amma gaba daya hankalinta yana kan najwa wadda itama ita take kallo.

Nabila ce tace"ku biyoni na kaiku,kallon budurwar take sanye take da wani kodadden zane sai wani hijabi daya fashe ta tsakiyar kai, kanta dauke da kayan miya da alama tallah takeyi,tafiya take yayi da najwa ke kara kallon yarinyar kamar wadda ta santa din nan.

Nabila kofar wani gida ta tsaya tana cewa bara naje na mata iso sai ku shigo,nabila tana shiga da gudu ta karasa tana fadin"umma umma, zainabu na makewayi ta fito tana fadin"wai nabila yaushe zakiyi hankali,kinsan dai ko yanzu aka miki aure tsab zaki zauna.

Nabila ce tace"umma baki kikayi wasu masu kudi,umma kinga motarsu wata katuwa ce yara sunje sun kewayeta,umma kuma dayar tana kama da yaya najwa,umma da sauri ta yar da butar tace"maza kije kice su shigo ina ga yau mafarkina zai tabbata.

Tabarmi ta shinfida a lokacin umma ce a gaba sai najwa wadda take binta a baya tana leke,a tsakar gidan kuwa umma ce a tsaye tana jiran shigowarsu,yayin da najwa da umma suka hada ido sai kawai umma ta fara fadin"najwa cikin karkarwar baki,sai kuma ta tafi luuu ta fadi,umma ce tace"maza kirawo safwaan da abba su shigo,ke kuma yammata miko mana ruwa.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 48

Najwa ce ta taho wajen zainabu wadda umma ke watsa mata ruwa, yayinda safwan ke kallon gidan yana mai kara kallon yanayi na gidan su najwa,gashi dai ginin kasa ne ko ina a lalace amma kuma fes ko ina a share a tsaftace.

Najwace tace"yah safwaan ku zauna,kallon tabarmar yayi dik da dai gata a mace amma kuma a tsaftace take tasha wanki.

Zainabu ce ta fara yayin data fara tozalo da idanun najwa suna zubar da kwallah,najwa ce ta dubeta tace"umma.

Zainabu ce ta dubeta tace"ashe dama zan kara ganinki a dubiya najwa, ashe gaskiyar ki da kikace zaki dawo da canji a cikin rayuwar mu,najwa ina kika shiga, tsawon wanann shekarun kina ina najwa.

Najwa ce ta kalli umma ta kalli safwaan da abbah sanann ta daga zainabu tace"umma ki zauna, umma ina fahad.

Umma ce tace"yawwa zainabu zauna dik wannan amsoshin tambayoyin zaki samesu insha allahu a bakina ba a bakin najwa ba,umma ce ta mike da kanta tace"bara to na hada wuta na dora mumu abin sawa a baki,njwa ce tace"aa umma ki barshi ku zauna ki kawo nayi miki.

Umma ce tace"najwa anya zaki iya kuwa duba da yanayinki ya chaanja,gaki kin zama 'yar gayu, safwaan ma kallon ta yake yayin da yake kokarin cewa ta barshi zasu je su siyo amma sam taki yadda su hada ido.

Umma ce ta katse maganar da cewa najwa ki huta ina safwaan kuje sai ku siyo mana a cikin gari,zainabu ce tace"ai kuma hanyar bata da kyau baiwar allah to kokuma tsaya bara na aika nabila ta karbo muku kindirmo sai na dama muku fura.

Nabila! NABILA!! UMMA ke kwala mata kira,nabila ce ta fito a tace"umma gani.

Umma ce tace"kije gidan su kuluwa sai ki amso min kindirmo anjima zanzo sai mu tattauna, nabila ce tace"toh umma,mikewa tayi najwa ce tace"tsayani kinji,safwaan zai mike umma ta zaunar dashi.

Tafe suke suna hira jefi jefi,najwa ce tace"nabila ya kai na ganku a haka kuma ina fahad.
Chapter 27 · 0% Book details