← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta kusa da itace tace"zo kawo ta ni ai bazan gudun aunty amina karama ba,tana basu ita ta fita daga dakin tana murmushi, a ranta tace"ohhh umma ni ba' yar fari ba amma ki duba kiga yadda umma ke min, dariya tayi kawai tana jijjiga kai.

Kiran Abbane ya katse mata tinanin da take, wayar ta daga tace"tohm bara nazo, tashi tayi tace"Sharifah bara naje wajen alhaji na dawo, sai da ta fito ta fara duban sakina amma ba ita ba alamunta,dakinta ta shiga nan ta tarar da kawayenta, kallonsu tayi bltaga ba ita, labiba ta gani zata huce tace"ni kuwa labiba ina kikaga sakina,lqbiba tace"tin dazu da aka daura aure na nemeta na rasa, murmushi umma tai ta fito ta nufi dakin safwaan dan ta tabbatar da cewa nan kadai zatwje ta ganta.

Tana shiga ta ganta a zaune sai rusa kuka take, tana rike da rigar sa wanda ya bari akan gadon,umma ita kanta da kyar ta daure ta karasa wajen sakinata dafata, tana dafata ta juyo ta fara rera sabon kuka,da kyar umma ta rarrasheta tace"haba sakina kiyi hakuri mana muma hakuri mukeyi, kowa da kika gani akwai kalar tasa jarrabar, kiyi hakuri indai safwaan ne dik inda yaje zai dawo, a jikina nakeji yana cikin alkhairi, kuma insha allahu zai kasance a cikin alkhairi,sakina da kyar ta dago idanunta ya kalli umma da ita ma hawayen take.

Da kyar ta lallabata suka tafi dakin abba, bayan sun zauna abba ne ya kalli safna yace"safna ke zanyiwa fada dan ina da tabbacin sakina bata da abokin fada, safna ce tace"haba abba kenan ita sakina kafiso shisa ka hadata da kyakkyawa ni kuma ka bani mummuna,abba ne ya kalleta yace"safna ninkikewa fadawa wannan maganar,kuka ta saka ta tashi ta mike ta fice tana bubbuga kafa, amina sai kiranta takeyi amma tayi kunnen uwar shegu da ita.

Amina ce tace"haba habiba kiyi mata magana mana, kallon ta habiba tayi tace"aah ai gaskia ta fada yafison sakina, tin ba yau ba yake nuna wariyar launin fata a tsakanin yaran nan, dan haka kamar yadda 'yata ta mike ta bar wajen nima haka zan mike na bar wajeb, sai dai ku zauna kuyiwa' yar so din fada.

Mikewa tayi ta bi bayan safna, aminatu zatayi mata magana abba yace"kyalesu suje suyi dik abinda suke tinanin shi je daidai, sunkuyar da kansa yayi yace"sakina tinda kike baki ta6a 6atan rai ba,tabbas kin cancanci yabo a wajena, dik abinda zan fada miki na tabbatar da cewa kinsani, sai dai na tunatar dake, ki sani zaki shiga wata rayuwa wadda wannan rayuwa ita ce rayuwar da ko wace mace ke fatan shiga, wato rayuwar aure, ki sani komai da kika aikata a rayuwar aure lada ne dashi, dan haka ki tsaya tsayin daka kiyi bautar allah,allah yayi miki albarka yayi wa zuri'arki albarka.

Wani kuka ne ya tasowa sakina wanda bata san lokacin daya kwace mata, cikin kuka take fadin"umma abba ku yafe mini, ku yafe mini,dan allah abba kayiwa mahaifiyata gafara akan abinda take maka,cikin tausayi yace"karki damu sakina allah ya baku zaman lafiya, daga nan ya tashi ya bar wajen, domin shi kansa baya son rabuwa da yarinyar.

Safna ce ta kalli umma tace"yoo umma hauka nake, taya zan zauna ana min wannan nasihar da ni ba sonta nake ba,hbiba ce ta kalleta tace"shisa nake alfahari dake wallahi, domin ke din ba irin waccen shashashar bace, kin san dai tsarin mu, kuma kinsan sadeeq na nan yana jiranki, to ki dai kula.

Sakina ce ta shigo dakin da suke tattuanawa,tsugunnawa tayi ta kalli mahaifiyar ta ta, tce"umma ki yafe mini dan allah idan har na miki wani laifi, wata muguwar harara ta zabga mata tace"laifin uban me zaki min in bada munafurci, da kin zauna da ni ne, ai baki zauna dani ba, dan haka ki tattara tsummar kafarki ki barmin gida, tin kafin dare yayi miki,jin zata 6ata mata rai ne yasa ta balbaleta da fada,murmushi sakina tayi sai kuma ta share hawayen fuskarra ta bar wajen.

Ana ta shirye shiryen kai amare, abba ne ya fito da mota, haka aka rako sakina da safna har bakin mota, sakina kuka takeyi sosai, yayin da safna ko a jikinta sai kalle kalle take tana faman bude hakora kamar gonar audiga,sakina ce ta rungume umma tana kuka, haka suka shiga mota daga nan abba ya tafi da su,dan kaisu dakin mijinsu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sai dai muyi muku fatan alkhairi da fatan allah ubangiji ya baku zaman lafiya ya kuma kawo kazantar daki.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 19

Tin daga bakin dajin nakejin wani gurnani wanda ni kaina Saida ya tsoratani, banyi aune hanaga Wata bakar kura wanda idanunta ya kasance Jajawur tana fitar da wannan Sauti mara dadin saurare,tafiya takeyi cikin Sauri sauri kamar zata fara gudu Sai kuma naga ta juya tana kallon bayanta, a hankali naga ta juya a wajen naga ta zauna tana mai rufe idanu.

Fahad ne yace "Umma Zanje dandalí daga nan kuma zan biya gidan mai gari, kallon 'dan nata tayi tace masa to.

ABUJA

Wani hadadden katon party hall ne wanda ya cika da al'umma kowa na wajen sanye da jajayen kaya a jikinsa.

Sai Gambo daya kasance yana Sanye da bakaken kaya hasken fitilu ya gauraye babban dakin taron yayin da Mc ya mikawa Gambo abin magana.

Gambo ne yayi gyaran murya yana mai Sakın wani gawurtaccen murmushi Inda wasu rinannun hakora Suka bayyana da gani Sun sha jan abu.

Magana ya fara kamar hakan"Nagode kowa da kowa da suka halarci wannan taro nawa na Shagali, Masu bani kyaututtuka in a godia.domin kuwa ina ganin kyauta, Dan haka Nagode muku, Gambo Nake Cewa Sai mun hadu a ranar rantsarwa, nan da sati 2 masu zuwa, ina godia, daga nan ya mikawa MC abin maganar ya zauna yana zazzare idanu.


Gaba daya wajen kida ne ya karade wajen, wasu mutane na hanga na magana zaune, Karasawa "nayi, dayanne yace" kasan burina a gama rantar da Gambo domin nasan Indai ya Sauka nine a layi, kuma Gambo Nasan mu zai fara Saurara domin kuwa mune manyan abokansa, Dayanne ya mika hannu yana Dariya nan Suka tafa.

Abbah ne yayi parking daidai wani Gida karamine da baki farin fenti, Sai kuma gate fari, wata motace kusa ·da Shi tayi parking, fitowa yayi ya kalli ango Rayyan yace" Ga Safna nan amanace a gareka, ka riketa amana.

Rayyan ne yace!! Tohm Abba bazaka Shigo bane, kallonsa Abba yayi yace" ea Ina Sauri akwai 'yar uwartane daganan ya Shiga mota ya bar wajen.
Sunyi tafia mai dan nisa Sannan ya Sake parking kamar yadda Ginin wacen gidan yake haka wannan ma yake Sai dai Shi fentinsa Milk ne, Abdallah ya kalla Sannan ya danka masa sakina ya juya batare da yayi magana ba, amma kallo daya ya isa ya tabbatar maka da cewa yana kewanta, ya juya ya fara tafiya "gudu Sakina ta biyo bayansa tana mai rungumesa hadi da fashewa da sabon kuka, Da kyar Abdullahi ya Janyeta Suka Shiga ciki.

Abba juyakan mofarsa yayi ya tafi
gida, gidan ba kowa Sai Samaiha da Umma Falo da alama zancen Safwaan Suke, yana zuwa ya shige zuwa falon sa, yayin da karamar ameenatu tabi bayansa, samaiha ta kamota.

Tinda Zakara yayi Cakara alamun Gari ya fara haske, Batare da tsammani ba Kuran nan ce naga ta fara futar da wani gurmani, a lokaci guda ta chanja daga kura zuwa najwa, takawa take a hankali kafarta na kalla wani katon Ciwo ne Sai Sossokewa da tayi da alama kaya ce ta soketa.

Fetowa tayi taga dajin tana kalle kalle, Ci tayi gaba kadan ta hango hanyar garın da mahaifiyarta suke, tafiya take Sannu a hankali, har takara sa tin daga kofar garin taga mutane,Yayın da wasu ke gudu da kofin siyan koko, dik da haka bata damu ba, domin a ranta tasan da hakan zai kasance.

Gidan su ta nufe a wannan hanyar taci sa'a bakowa, Gidan ta shiga da Sallama a bakın ta, Nabila ce ke alwala ganin najwa yasata sakin butar tana Fadin" Aunty Najwa umma, ya Faisal kuzo ga aunty najwa ta dawo.
Da Sauri Umma, Fahad, Suka fito Suna kallo Najwa wadda take zubar da hawaye, ummar ce ta kalleta sai kuma ta rungumeta, umma ce tace" Fahad kai mata ruwa bayi ta watsa taci abinci.


Najwa ce tace" Umma kiyi hakuri ba abinda kawoni kenan ba, Umma nazo ne na ganku ke da Kannena, Umma tafiya zanyi domin kuwa baza ku lya zaama dani ba, Nidin da nake a kowane dare yanzu Chanjawa nake umma.

Umma ce tace" Naji Najwa amma kiyi wanka kuma ki tabbatar kinci abinci, dik maganan da zamuyi Sai muyi, Najwa ce ta kalli fuskokinsu tace" Har yanzu baza ku daina kukan bako‘ daga nan ta wuce zuwa bandaki.

Safna ce ta mike daga kan gadon tanayi tana doka hamma, kallon dakin tayı, kaya ne masu kyau brown colour wanda Suke da zane zane a Jikinsu.

kallon rayyan tayi wanda yake tsaye yana kallonta ba ko Kunya baby tace" kafin na fito yakamata ka Samo mana abin ci dan kasan nagaji bakuma zan Shiga kitchen ba daga zuwana.

Da mamaki yake kallonta, sai kuma ya fice take dik abinda ya faru a daren jiya ya fara dawo masa kamar yadda Abba ya kawo min ke zan kula dake insha allahu, ko kallonsa batayi ba tace"baka dauko min plate ba dan cin kazar, kallonta yakeyi, mikewa yayi ya fito a Fili ya furta" ya Ilahy Ita kuma wannan kuma ba kunya a tattare da ita.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊
Chapter 11 · 0% Book details