← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 31

Sashe 4

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nabila ce ta Mike tana kallon Fahad da ya maida hankalinsa kan waya,a hankali tace"wait yaya Fahad Ina ka samo waya,bai Bata amsa ba dole ta wuce ta tafi,dakin ta shigo zaune ta tarar da zainabu ta rafka uban tagumi,nabila ce ta zauna sannan tace"umma wai meyake damunki ne,kallon ta tayi tace"bakomai yawwa kin gama ko,gya'da Kai tayi,umma ce tace"ki tashi kije gidan hajiya baito kice mata idan sakon yazo ta baki,kudi ta zaro ta Mika mata tace"wanna Kuma kiyi kudin machine sanann ki tabbatar kin dawo da wuri gari na ruwa,da toh ta Mike ta fito tana kallon najwa data kwanta a kasa tana bacci.

Umma ce ta fito da sauri tace"Fahad Ina ka samo waya,ban hanaka rike wayaba,wai Fahad yaushe zakai hankali,kasan iya matsalar da kake jefa kanka ta hanyar wanan wayar,d'agowa yayi yace"umma wai meye matsalar,kwace wayar tayi tace"zaka sani Nan bada jimawa ba,sanann zaka rike waya dai zarar komai ya dawo daidai.

Kallon najwa da take bacci a kasa tayi,take wani tausayinta ne ya Kama ta,dik abinda ke faruwa Fahad na kallonta,Shi kansa tausayin mahaifiyar ta su yake,saboda Yana kokwanton akwai wani abu a kasa tinda gashi a kwana nan yanayinta sauyawa yakeyi it's kadai kaga tana kallon najwa ko Kuma tana tunani,tabbas akwai wani abun da su Basu San dash Nabila ce ke hanyar dawowa daga Aiken da umma tayi mata,tindaga nesa ta hango wasu mutane su5 sanye da bakaken Kaya da Kuma jajaye,tana Kara matsowa ta gifta su,har sun wuce sai Kuma Suka tsaya,dayanne yace"Kai Kuma idi me ka tsaya,saurin janyo wayarsa yayi yace"Kai banza ne wannan it's ce wadda oga yake nema,saurin juyawa sukayi,kamar ance nabila juya taga sun juyi suna kallonta,cike da tsurewa ta tattare skirt yayin data saki mayafin anan ta saka na Kare,binta suka yi suka rufa mata Bata,gudu take tana kuka domin sun kusa kamata,batare da tinanin komai ba Tasha wani lungu hanyoyi mabanbanta,anan ne suka nemeta suka rasa,idi ne yace"Ashe dama sun garin Nan dole oga yaji lafiyayyen labari domin nasan Muna da tukuici.

Nabila gudu take gida ta shigo tana huci tana faman tari,Zama tayi bakin baranda yayin da idanun ke zubar da kwallah,cikin yanayi Mara dadi tace"umma ummah tana yi tana nuna mata hanyar wake,da sauri suka zagaya yayin da Fahad sai a lokacin ya shigo ya dawo daga masallaci,zagayeta sukayi har najwa sun tambayarta lafiya,cikin yanayin firgici tace"umma sun dawo sun dawo,sun Kara biyo mu wannan garin,mutanen kazaure sune sun biyo mu Nan,ba abinda zainabu ta furta sai inalillahi wa Inna ilaihi raji'un,saurin mikewa ta shigo dakin ta,cikin wata akwatu Naga ta daga ta fara bincike,can naganta da wata da Kuma batiri,kunna wayar tayi kirar Nokia,Jin wani sako da tayi ne yasa ta sake tabbatar da cewa su ne,da sauri ta fara tattara kayayyakinta.

Fitowa tayi ta kalli nabila,Fahad tace"kuje Maza ku tattaro kayanku dole mu bar garin nan,ba Zama tashi sukayi suka tafi,najwa ce tace"umma Kinga bana gani,wani irin  faduwar gaba taji,karasowa tayi Tana haske ta da fitilar touchlight,wani irin firgita tayi ganin idanunta na zubar da jini,da sauri ta wanka mata Mari Wanda ita kanta sainta taji tausayin 'yar Tata,karavta saki ganin haka yasa taita marinta,sai Kuma a take a wajen ta Fadi ta rufe idanun,ayatul kursiyyu take karantawa take tofawa,dik bakin wajen sai da wani bakin abu ya fito daga cikin idanunta,ganin haka yasa zainabu mikewa ta karasa hado kayan su daga nan ta mikar da it's suka bar wajen.

A soron gidan fahad ya tsaya yana kallon mahaifiyar tasu da a lokaci guda ta firgice, mika masa najwa tayi tace"riketa da kyau karka saketa, da tohm yace.

Fitowa sukayi suka fara tafiya sunayi tana kallon yanayin garin da ruwa ya tsinke, basu dade ba suka je tasha,mota daya ce ta rage ta katsina ita sukai saurin shiga daganan motar alkah ya taimaka ta cika, daga nan suka hau kwalta, yayin da dik addu'ar data fado bakinta yi takeyi, kallon najwa take da har yanzu tana bacci, fahad ne ya kasa jurewa yace"umma mene ya faru, umma ki fada mana, alama tayi masa da yayi shiru, daga nan har suka fice daga garin na gombe.

Tafiya suke a wannan daren yayin da tafiya tayi nisa kowa na bacci, banda zainabu data zabga uban tagumi tana faman tunani.

Tin bayan komawarsu nan ogan ya basu umarni da su nemo masa wanann ahalin, a haka suka bazamo nemanta, da kyaar suka samo gidan su, cikin daren nan gidan suka shiga, bincike suke yayin da ruwa ya fara zuba, nemanta suke amma ba kowa.

Idi ne ya juya ya kalli dayan yace"shikenna munyi rashi fa domin kuwa matar nan ta gudu, kallon kallo suka fara a take a wajen suka fara farfashe dik wani abu daga nan suka kulle gidan suka tafi ya zuwa wajen ogansu.

Tinda sassafe mutanen unguwar suka fara ganin abinda basuyu tsammani ba domin kuwa,ganin gida sukai a kasa ya zube gashi ba komai a tsakar gidan, kowa ya fito yana mamaki, mutanen jiya ne suka kara dawowa yayin da suka fara tambayar zainabu da yaranta amma ina ba wani labari, dole ja kafafunsu zuwa wajen wanda ya aikosu.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDA MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BIYAR DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

Page 6

Wani hadadden gida ne dai dai lokacin da su idi suka tsayar da mota suna jira a bude musu gate din, ba zato kuwa aka bude musu, kunna motar yayi cikin gidan yana hangen inda zai ga messenger alhajinnasu.

Can ya hangosa kasan wata bishiyar goba yana jin wata radio kasancewar sa tsohon mutum, fitowa yayi ya tsugunna a kasa yace"Baba alhaji yana nan, da kyar ya ɗago kqnda yace"ea yana ciki amma yace"kar wamda ya shiga domin ya riga daya shiga wani babban aiki,jiki a sanyaye idi ya mike yana kallon sauran yaran yace"mu tafi tinda ya riga ya shiga aikin nan fitowar sa sai wani satin, cikin abinda basuyi zato ba kawai sukaga wani bakin duhu ya lullubesu daga nan kuma bansan ya akayi ba.

Tafiya suke a wanann yinin har tsawon wanann lokacin najwa bata farka ba, nabila ce ta kalli mahaifiyar tasu tace"umma shikenan najwa wannan karon ma sai ta kara wani watan bata farka ba, umma wai me yake damun najwa, batai kokarin bata amsa ba, sai kokarin hawa wata motar take wadda naji ana kiran bakori cikin karamar hukumar katsina.

Hawa dikansu sukayi har tsawon wanann lokacin zainabu batace dasu komai ba, sai abinci data siya musu ta mika musu suna ci, tafiya sukeyi a motar yayin da motar ta dau sautin shiru, najwa ce naga ta fara zabure zabure, kamar ba ita bace ke baccin, gaba daya ta fara gigita, ta fara fita daga hayyacinta, yayin ds jini yake ta zuba daga bakinta da kuma kunenta.

Gaba daya al'ummar cikin motar ne suke kallon ikon allah, zainabu ce ta kalli drivern tace"dan allah direba tsaya sauka zsmuyi, cike da tausayi yace"amma baiwar allah da kin bari mun karaso Tasha nan ai cikin kauyinka ne, bata sauraresa ba ta fara kokarin sauka, haka kuwa suka sauka yayin da mutane na tofa albarkacin bakinsa.

Gefen titin jikin wata bishiya suka tsaya, nabila xe ta fashe da kuka tana kallon magaifiyar tasu da ta gama fita a hayyacinta, ba tare da sanin inda zata je ba ta dauki najwa ta fara tafiya cikin bafulatanna da suke kiwon dabbobi,kallonta suke cikin yanayin tsoro, cike da tsoro suke kallonta, da kyar wani bafulata ni ya karasa wajenta cikin maganarsa ta fulani yace"baiwar allah lafiya, cikin kuka ta mika masa najwa da take zubar da jini, kallon ta yayi sai kuma naga ya juya da sauri ya koma zuwa bukkarsu, ba wani 6ata lokaci ya fito da gudu yana kallon najwa a zube a cikin kasa, baiyi wata wata ba ya sungume ta ya komar da ita zuwa bukkar daya futo.

Binsa sukayi nan sukaga bukka ce gaba daya bukkar magunguna ne kala daban daban, kowanne da nasa amfanin, gefe kuma wani mutum ne saman buzu yana jan carbi, sai da ya gama ajiyeta sannan ya juya ya koma inda ya fito, zainabu da sauran yaran suka zauna suna jiran ya gama, abin da ya bawa zainabu da yaran mamaki ganin da sukayi najwa ta daina wanann shure shuren amma dik da haka jinin bai daina fita ba.

Ajiye carbin yayi ya shafa hannayrnsa a face dinsa, sai ya kalli najwa ba tare da yace uffan ba ya mike ya dakko wata tasa da ruwa a ciki, kallon tasar yayi sai kuma ya zauna yana mai rufe idanunsa, ya dauki tsawon mintuna 1 sannan ya bude idansa yana mai yin tofi a wannan ruwa da yake cikin tasar, dauka yayi a hankali irin tafiyar malaman da suka kwana 2 ya karasa gabanta, ajiyewa yayi sai kuma a hankali ya bude bakinta, a wanann lokaci ne naji bakinsa ya furta"بسم الله الرحمن الرحيم sannan ya diga mata ruwan a baki.

Bai fi mintuna 3 ba jinin ya fara janyewa da kansa, sai a lokacin na lura dashi dattijo ne fuskarsa cike take da furfura, sai kuma wni katon carbi a hannunsa wanda da shi ne yake tasbihi ga ubangiji mai girma mai komai, ganin jinin ya tsaya ya saka zainabu matsawa kusa dashi tana masa godiya, kallonta yayi yace"ku zauna nan sai ta Farka, zata farka amma bazata farka da wuri ba, daga nan ya koma zuwa kan vuzunsa yaci gaba da wuridi.
Chapter 4 · 0% Book details