← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 31

Sashe 14

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safwaan ne ya kalleta yace" karki fadam maganar banza kamar ya mahaifin ki ne sila malama ki fada min wacece ke, murmushi najwa tayi tace"dama nasan ba lalle ka yadda ba amma ka sani cewa mahaifina ne silar shiga wannan rayuwar dana tsinci kaina, shi ne silar komai.

Amma kai wanene,me ya kawoka wannam dajin da babu kowa a ciki,safwaan cikin mamaki yace"a ina nake yanzu,najwa cikin magana kasa kasa tace"katsina muke,wani kuka ta jiyo daga can nesa, hakan yasata saurin mikewa, kallon safwaaan tayi tace"mike mu bar wajen nan yanzu domin dajin nan cike yake da ababen ban tsoro,safwaan ya tsorata haka yasa ya mike yana mai kama hannun najwa,kallonsa tayi kamar tayi dariya, komai ta tuna kuma sai ta fasa.

 Da Gudu Suke fito daga wajen, gudu suke amma Wannan kukan na binsu, cikin kankanin lokaci Wannan wadansu irin halittu suka kewayesu Suna kallonsu, tsintsaye ne amma kamar ba tsuntsaye ba Saidai kowanne da Fuka Fukai a Jikinsa.

Najwa Cikin lokaci guda idanunta ne suka sauya kala daga farare suwa bakake wulik ganin haka yasa wannan halittu dare wa kowa ya kama gabansa, ganin Sun kama gabansu ne yasa najwa Jan hannun safwaan suka cigaba da tafya, basu dade Suna tafiya Suka fito bakin titi, safwaan yana ganin haka yayi handala ga allah dayw kubutar dashi, tafiya Suke ba wanda yace da wani komai.

Daidai bakin tasha Sukazo wucewa Safwan ne wata dabara ta fado masa ya kalli najwa yace" baiwar allah dantsaya anan yanzu zandawo, bata basa amsaba ta saki hannunsa.

Cikin tashar ya Shiga yana kara kallon najwa a ransa yace" wannan ai Itace wadda nake gani mafarki, dik da haka bai gasgata hakan ba, wajen wani mai pos ya tsaya, hakan yasa ya bar zancen. kallonsa yay bayan Sun gaisa yace" Dan allah dan allah malam waya nake So zanyi, za'a turo min da kudi da fari mai pos din bai yadda ba, daga baya kuma ban san me ya gani ba, sai ya mika masa wata keypad,da Sauri Safwaan ya karbi wayan ya matsa gefe. Numbern Abbah ya saka ya fara kokari kiransa, ya kirasa a lokacin abba yana driving ganin numbern ba Suna yasashi bai daga ba ganin har anyi kira 3 yasa Shi yin parking, Daga wayar yayi yakara a kunne, jin muryar Safwaan da sauri yace Safwaan, Safwaan, Safwan na hawaye yace "Na'am Abba, Abba na kubuta, Abba yanzu haka Ina katsina, Abba ne yace" ok to ok to yanzu ya kakeso ayi, So nake na ganka ka dawo a yanzu tinda yanzu Safiyan tayi.

Safwan ne yace" abba bazaiyi yuba Sabida wata yarinyace ta Ceceni, Abba ne yace karka damu bara na tura maka kudi ku taho tare da yarinyar da ta cece ka domin na tabbata akwai wani abu, Safwan ne yace" amma da alama Abba tana cikin matsala, Abbane yace" Naji Safwan ka hanzarta dawowa gida tare da yarinyar nan.

Sai da ya gama bawa abba labarin yarinyar Sannan abba yace" to shikenan yanzu bawa mai wayar, safwan mikawa mai wayar yayi Sannan ya koma gefe ya dan dauki lokaci Sannan ya katse, baya da kamar mintuna 10 naga ya kirgo wasu bandir na kudi ya bawa Safwaan yayin daya masa godiya ya Juya ya koma wajen Najwa.

Karasawa yayi yace" baiwar allah na barki kina jira ko, dan allah ya hakuri, amma ya Sunanki, kai tsaye tace! Najwa kaifa, Safwaan ya bata yana kokarin zama,yace" amma Ina zakije a hankali tace" masa Gombe, da mamaki yace" ni kuma kaduna, murmushi tayi tace "masha allah a ranta a fili kuwa murmushi tayi, Safwaan ne yace" to zaki lya bani labarinki, A' wajen wasu Siraran hawaye Suka zubo mata, anan ta basa labarinta.

cikin tausaya wa yace" tohm karki damu zan taimaka miki,kamar yadda kika taimaka min, In Sha allahu kuma zaki warke, murmushi, Najwa tayi tace! kada ka taimakeni har sai naje ga mahaifina wanda ya zama Shine sila na wannan abin daya Faru da ni.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮

Page 24

Safwaan ne yace"amma najwa da zaki bi ta tawa da kin kyalesa da mahaliccinsa, domin kuwa allah yana ji yana gani, kuma dik abinda mitum ya aikata allah yana madaka ta yana jiransa,najwa ce ta kallesa sai kuma tayi shiru tana tinanin maganarsa, har ta bude baki zatayi magana yace"najwa indai tinanin ki yadda halittarki take canjawane ki kwantar da hankalinki domin ni da kaina zan sama miki lafiya.

Kallonsa take sai kuma tace"amma dik da haka zanje zuwa ga mahaifina, domin sai na tambayesa dalilin dayasa ya maidani rabi mutum rabi dabba, tin bayan dana shekara 10 nake fuskantar matsaloli a cikin rayuwa na daga wanann sai wannan, dan haka tabbas zanje garesa, safwaane ya kalleta yace"naji zakoje gareta, yanzu zaki ci abinci"girgiza masa kai tayi tace"naci abinci tin ba yanzu ba.

Safwaan a karo na 2 yace"bakyajin yunwa ko, gyada masa kai tayi alamun eah, kama hannunta yayi suka mike suna kallaon garejin, cikin kankanin lokaci suka samu mota har kaduna,najwa ce ta kallesa tace"kada mu hau wannan motar domin kuwa a kowane dare ina chanjawa kuma na tabbata daga nan kafin muje kaduna dare ya raba kuma a wannan daren nake komawa kura.

Dan haka mu hau wadda zata kaimu kano, daga nan kuma sai mu kwana, washe gari kuma sai mu dauki hanyar kadunan, safwaan kallon ta yayi, tabbas ya tausaya mata, amma ya sani dole sai dai ayi ta tan, dan haka kuwa nan suka hau motar kano wadda tana cika aka tashi, tafiya ake yayin da kowa ya fara bacci, najwa sai da tafiya tayi nisa sanann ta kalli safwaan tace"amma kuma kai baka fadan naka labarin ba.

Safwaan ne yayi gyaran murya yace"labari na kusan iri daya ne da naki, sai dai ba irin naki bane, najwa labari na mahaifi na ne silar komai, shi ne ya kawo ni nan dajin, domin a tinaninsa ba wanda zaizo gareni,sannan yayi min wani irin siddabaru da bazanji yunwa ba, bayan ya saka yaronsa ya dakko ni ya kawo ni nan dajin domin yasan ba wanda zaizo ya taimakeni.

Na dade a wajen shisa na tambayeki yu nawa ga wata, da kika fada min dana kirga kwanakin a yau kwanana 10 cif, kuma a yau kika taimakeni, shisa sai da na rama sallolina sannan na dawo kika bani Labarin ki, labari na ya fara daga sanda umma ta haifeni, umma ita ce mahaifiyata, sunanta ameenatu bara na baki a gurguje.

Sunan mahaifina Alhaji Muttaka, mutum ne wanda sam bashi da matsala da mu, bayan haihuwata da shekara 10 anan ne yaje ya aro wata mata mai suna jamila, jamila ta kasance makirar mace ce, domin sai da tasan yadda tayi ta kori mahaifiyata daga gidan mahaifina sanann kuma ta bimu da sharrin cewa ni ba dansa bane, dik da haka mahaifiyata bata musa ba, saboda tasan da cewa jamila asiri tayiwa mahaifi na.

A haka da wananna tsana mahaifiyata bayan tayi idda allah ya futo mata da miji mai suna alhaji Suraja, wanda muke masa lakabi da abbah, ya aureta kasantuwar matarsa ta mutu a sanadiyyan haihuwa, shi ya rikeni ya reneni har na kai zuwa wannan lokacin, jamila tin tanyin asiri a boye har sai da tazo ta saka mahaifina shima a harkar asiri.

A baya bayan shekarun nan mahaifin na ya samu matsala ta karayar arziki har bokansa ya gaya masa labarin sai dai ayi amfani dani wajen asiri domin dukiyarsa ta hauhauwa,tin lokacin da mahaifina ya saki mahaifiyata bai kara dawowa gareni ba har sai da na cika shekaru 25 sannan ya zo wai a basa dansa, inda anan ne umma tace ita bata yadda ba.

Bayan yaga da gaske umma bazata yadda bane yasashi tafiya wajen bokan har akamin asiri, a dik lokacin da wani abu yazo faruwa to wasu sassa na jikima na chanja launi kamar idanu da hannuwa na, ga wani sabon karfi da nakeji kamar zan tashi sama,bayan tsaown shekara 1 anan ne abbah ya samuya karya tsafin nasa sannan kuma ya ke bani magunguna, amma baya da kamar wata 2 anan ne asirin ya kara shuga jikina wanda har yafi na da ma karfi, shi ne dalilin guduwa na da zuwa wajen mahaifina muttaka, inda anan ne yasa yaronsa mai suna tasku ya dakko ni ya kawo ni nan,ya kuma shaka mani magani da zummar bazan ta6a ku6uta ba, domin bokansa yace"inda na ku6uta to zai talauce, talauci mai tsananin gaske.

Mahaifiya ta tana da kishiya sunanta habiba tana da yara 2,daya sakina daya safna, sakina ita ce mai hankali kuma a wajen ummana take da zama tin bayan da tayiwa 'yar ta aure' yar wajen abba wato kanwata samaiha, yayin da it kuma safna bata da kunya ko kankane, kuma sam bata girmama kowa.

Juyawa yayi yana kallon najwa da bacci ya dauketa, kallonta yaje yayin da take bacci sannu a hankali,tsayawa yayi yana karewa halittarta kallo,yayinda take da ciar gashin gira amma ba irin cunkus din nan ba, sai gashin ido wanda ya kasance madaidaita, da hanci da kuma dan karamin baki, kallonta yake a take shima ya kwantar dakia ya runtse idanu yana tinanin rayuwa.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮

Page 25
Chapter 14 · 0% Book details