← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 31

Sashe 17

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda mai gadi yaje falo ya kalli umma yace"wai hajiya wata ce ke neman safna, umma jin an ambaci safna yasata yin dogon tinani can kuma tace"kaje kace bata nan, sai kuma ta kalli mai gadin tace"mudi ka raba kanka da fishin alhaji, alhaji ya hana safna fita bare har ace wata kawarta tazo, mudi ne yace"to hajiya insha allahu za a kiyaye.

Komawa yayi, sai kuma yaga ba kowa, hakan yasa shi sawa gidan lock ya zauna yana fadin"kai nima da fati nayi mamaki'yar karamar yarinya ace tana neman safna.

💮💮💮💮💮💮💮

Wata siririyar kofa najwa taga sun shiga sanan kuma taga sun hau wani step, wata kofa ta gani,mirdawa yayi a lokacin ta bude, wani sanyi ne ya dokesu,yayin da najwa ta lumshe idanu tana kara kallon dakin, komai gashi nan tsaf tsaf,kallon safwaan tayi tace"yanzu dama safwaan anan kake rayuwa, ohhh kalli gida mai kyau, sai kuma ta hau dariya, hadi da fadawa kan kujerar dakin.

Safwaan ne ya shige ciki domin neemo wayarsa,yana shiga ya ganta akan table na wardrobe dinsa, kunna ta ke kokarin yi amma taki kawowa, hakan yasa shi sakata a charji yana kokarin cire kaya,yaji ana fadin safwaan! Safwaan!! Turus tayi sai kuma naga ta jiya ta koma da gudu,safwaan ne ya juya ya kalleta sai kuma yayi murmushi.

Najwa kuwa zama tayi tana kara kallon wani zane da ta gani,mikewa tayi ta nufi wajen zanen inda aka tanada don zane kadai,kallon zanen take, wani zane ta hango take ta furta"kaii wannan kamar ni ce,murmushi tayi sai kuma tace"kai ba kama bace wannan ni ce, ba shakka ni ce,ta shagala da kallon hoton taji safwaan na fadin "najwa zo kici abinci.

Juyowa tayi take ya kalleta ya kalli hoton, runtse idanunsa yayi sai kuma yayi saurin budewa yana fadin" ke ce dama, dama. Zan ganki a rayuwata,kece wadda kike zuwarmin mafarki,najwa ce ta kalle sa tace"ni ce kalli kaga, yayin data kara hoton da face din ta take komai ya fito, murmushi ne ya su6uce mas take ya karasa gareta yana rungumeta.

Kamar yadda abbah ke fada hakan ce ta kasance tabbas najwa kina neman taimako na, nikuma zan taimaka mi ki, insha allahu zan taimaka miki, tabbas kece, jin ya rungumeta ta karfi ne yasa ta sakin 'yar kara tana fadin"kuma ka rungumeni da karfi,jin ta ambaci hakan yasa shi sakinta yana furta"astagfirullahil azeem.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 29

Baya da kamar mintuna 20 wayar yaje ya kunna, yana kunnawa nan fa messages,suka fara shigowa,kalon message din yake, sai da ya tabbartar da sun gama shigowa ne sannan ya dauki wayar, ko message daya bai duba ba ya tafi wajen calls, wata number da akayi Saving da abbah ita naga ya dannawa kira,abba yana cikin masallaci dan haka wayar tasa tana aljihu kuma a silents bai ji kiranba, dan haka sai ya kira umma.

Umma tana kitchen tana kokarin dafa abinci ta jiyo ringing na wayrata

Mamaki ne ya bayyana Fuskarta ganin numbern da batayi tinanin ganinta ba, Cikin zumudi ta daga wayar tana fadin" Safwaan safwan na bedroom yace Na'am Umma na dawo ina dakina tin dazu, umma ce tace tsaya, tsaya yanzu zan karaso, tṣaya ta kara fadi a karo na biyu, bata katse wayar sa ta nufi upstair, takawa take sannu a hankali har Saida taje dakin Safwaan kai tsaye ta shiga sai kuma tayi, turus ganin wata, kallon Najwa take da take sallah can a kan sallaya.

Umma ce ta furta" Safwan, safwan nan ya Fito daga dakin, Umma kallonsa tayi tana zubar da hawaye kallonsa umma take ya rame yay, baki, Sanye yake da jallabiya Coffee, Umma ceta Shafa kansa domin tabbas tayi kewar Safwan.

Najwa ce ta idar da Sallar tajuyo mikewa tayi zata gudu, Safwan ne yace" Najwa Ina zakije, murmushi Najwa ta kakalo tace" bako Ina, Ummace ko, Umma na wuni mun Sameku lafiya, Umma sakin baki tayi tana kallonta, ganin kamar bata gane ta ba, yasa Safwan Dakko zanen nan ya mikawa Umma, Saida ta karba Sannan yace" Umma duba da Lyau fuskar Ce kadai babu amma sak itace wadda nake nema.

Umma ce ta karasa kusa da najwa
Sannan ta rungumeta. Sai kuma ta sake ta tace"yarinya ya Sunanki, kasa tayi da kanta tace" Najwa,Umma ce tace" Najwa dik da ban sanki ba nasan kece kika taimaki safwaan amma kedin wacece.

Najwa ce taja da baya ta fara kokarin barin wajen,ganin haka yasa Safwaan bude baki zai magana daidai lokacin aka bude kofan dakin, gaba dayansu kallon kofar sukayi, Safwan ne ya ruga hadi da rungume abba kamar wani yar, yayın da najwa ke kallonsa, Abba ne yadago ya kalli najwa in kalli Safwaan Yace" Najwa ko murmushi najwa tayi tace"eah abbah ina wuni, safwan ne yayi murmushi abba ya amsa da lafiya louh najwa.

Baya da kamar mintuna 30 ne umma ce a dakin sakina tare da najwa a tsaye Umma ce tace kinga wannan dakin na 'yata ne sakina, kema ki zauna a ciki, har lokacın da allah zaiyi ki warke ki koma gidanku ko, murmushi najwa tayi, taci gabada murmushi.

Safna tinda ta shiga dakinta bata fitoba har Sai da taji Cikinta na kiran yunwa kuma tabbatar da cewa yanzu an gama abinci, mikewa tayita fito tana zumbure zumburen baki, turis tayi ganin safwaan a ranta tace"kutmelesi wannan dan****yaushe ya dawo gidan sai kuma ta maze ta juyo ta dawo.

Abbah, Umma, Safwan hadi da wata bakuwar fuska a dining, Karasawa tayi ta zauna tana kallon su daya bayan daya kamar bata Sansu ba, ba wanda yayi mata magana, kowa Idan ya gama mikewa yake yana barin wajen sai da ya rage daga ita Sai Safwan da najwa, safna ce taja tsaki tace" aikin banza kai kuma agola yaushe ka dawo gidan da baka da gado aciki, murmushi Safwan yayi yace" bakiso na dawo ba ko, mike wa yayi ya bar wajen najwa ce ta mike zata bar wajen safna ce tace" ke kuma fa, Najwa dariya tayi tace" lalle Safna baki Sanni bane, domin da kinsanni da bazaki taba yi min wannan rashin kunyar taki ba, Sororo tayi tana kallonta yayın da safna baki ya mutu ta rasa tacewa, cikin jin haushi ta daga hannu ta wankawa najwa mari.

Safna ce tace"banyi lalacewar da wata can zatazo har ta gaya min magana a gidan ubana ba, dallah dubeki wata kucaka dake,ki kalleni da kyau ko ban baki shekaru 4 ba zan baki 3 amma kizo kina fadamin magana,najwa murmushi tayi tace"ki tabbatar da cewa kin taro wasa kuma ki nemo 'yan wasa tin kafin dare yayi miki, idan kuma ba haka ba ke zakiyi kuka da idanunki, aikin banza yiwa mutum aure amma ya kasa zama sai dai ya dawo gidansu yana gwada izza.

Idan har ke kin yadda mace ce ai gadarar ki a gidan mijinki zaki gwadata ba anan ba,janyo najwa tayi hadi da kara wankawa mata wani marin, daidai lokacin safwaan ya karaso wajen yana fadin"ashe safna baki da hankali, mai najwa tayi miki har kike mata wanann marin,safna cikin jin haushin abin tace"na mara kuma wallahi dik abinda zai faru sai dai ya faru, murmushi najwa tayi tace"haka kika ce ko.

Safwaan ne yace"aa njwa dan allah ki kyaleta, karki cutar da ita,najwa ce ta kallesa yayin da idanunta suka fara canja launi,a take a wajen ta zauna ta lumshe idanunta,safna kuma ta wuce tana kara kallonsu.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 30

Najwa ce ta kallesa tace"bakomai ya safwaan ya wuce,safwaan dik da haka bai yadda ba saboda shi yasan me ya gani a daren jiya, kiran abbah ne yasa shi mikewa ya bar wajen.

A daki na hangesa an mika masa wata leda,abbah ne yace"kaji dai me na fada maka, sanann ita kuma najwa zan kira aboki na insha allahu zai taimaka mana, saboda wanann din aikin sa, aikin karya tsafi da asiri,amma naji kace sai dai da magariba tayi kar wanda yaje kusa da ita,murmushi safwaan yayi yace"eaa abba domin kowane dare tana komawa kura ne kuma abbah abin ba kyan gani,girgiza kai abba yayi yace"allah ubangiji ya tsare mana imanin mu da ameen safwaan ya amsa ya tashi ya bar dakin.

Umma ce ta kalli abbah tace"nikam abbah ya maganar habiba naji kayi shiru kai baka dawo da ita ba,abbah ne yace"to ya kikeso nayi mata meenatu kinsan a yanzu haka ma bata kasar wai ta tafi nijar, zaro ido umma tayi zatayi magana wayarsa tayi kara,umma ya kalla bayan ya kalli wayar yace"kingani Mustapha ke kirana,dagawa yayi sai kuma ya tashi ya fita.

💮💮💮💮💮💮💮💮💮

Alhaji gambo ne kwance akan wani katafaren gado yayin da wasu 'yammata wajen su 5 ke a wajen, wasu na masa tausa, wasu suna masa fifita, yayin da dayar ke basa abinci a baki.

Can cikin ransa ke fadin"tabbas na fara dandanar dadin shugabanci, domin kuwa wannan shi ne shugabanci,wata dariya ce ta kwace masa,, yayin da sauran 'yammatan su ma ke tasu dariyar, daidai lokacin da Agogo dakin ya buga, wasu' yammata ne suka shigo yayin da su kuma sauran suka fita.

Baya da mintuna 40 ya fito fes sanye da wasu irin kaya wanda ba wanda yaje saka su sai dai idan mutum ya kasance shuga ba ne,kallonsa suke domin kuwa yayi kyau ba karya, kowa ya mike a wannan lokacin har sai da ya zauna sannan sauran suka zauna.

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Chapter 17 · 0% Book details