← Book details Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 31

Sashe 18

Mahaifin Mu Ne Sila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah ne ya dawo yana kallon umma da har yanzu tana zaune akan kujeran, abbah ne ya dawo wajen zamansa yace"kinji yadda mukayi da Mustapha, zai turo da kayan aikin ni zan hada kuma yace"insha allahu indai akai mata aikin kwana 3 to wanann tsafin zai karye. Umma da murmushi tace"to allah ubangiji ya bata lafiya,abbah ne yace"ameen, daga nan suka canja hirar.

Safna ce kwance tana tinanin muradin ranta wato sadeeq, dik ji tayi yau idan bata gansa ba akwai matsala, amma tasan ba yadda zatayi ta gansa dole sai dai idan ba kowa a gidan,mikewa tsaye tayi a ranta tace"gani ba waya bare ma naje na samu na gansa ko ta video call ne.

Tana cikin wannan tinanin najwa ce ta bude kofar dakin ta ta shigo,hade rai safna tayi tace"uban me ya kawoki daki na,najwa ranta a hade kamar bata ta6a dariya ba tace"ubanki ne dan uwarki, an gaya miki ana dukana, to dik duniya uwata ce kadai take dukana na hakira, idan ba haka ba kuwa ba wanda ya isa wallahi,cikin kankanin lokaci ta gwara kan safna da bango.

Safna wata karar azaba ta saki hadi da dafw goshinta, jin kara tayi hakan yasata saurin juyowa, ba kowa bace ke karar sai najwa wadda take soshe soshe hadi da fitar da wani marayaan kuka, wanda dik wani mai imani idan ya ganta sai ya tausaya mata, safna ce ke kokarin zuwa inda take, dai dai lokacin safwaan ya shigo yana dakatar da safna.

Janyota yayi tana zuwa kusa dashi yayin da jini ke zuba a goshin ta, a lokaci guda najwa ta koma wata katuwar kura wadda safna bata san lokacin data fadi ba ta sume,safwaan ke jijjigata,umma da abba ne suka shigo dakin suna kallon najwa, abba ne ya kalleta kallo na tsanaki sannan ya dauki wayarsa, video yayi mata, yayin da suka fito, safwaan ne ya kashe wutar dakin ya rufo ya dakko safna.

A kan kujerar falon ya ajiyeta sannan ya huce zuwa sama,wata yar box ya dakko, daidai lokacin da wayarsa tayi ruri,ajiyewa yayi yana kokarin duba wake kiransa,dagawa yayi yace"ina zuwa ka shigo yanzu zanzo.

Umma ce ta karbi box din tana kokarin budewa, shi kuma ya fita, kayan aikin ta dakko ta fara saka mata hydrogen daidai lokacin ta farka, amma kuma sai ta lumshe idanu tana jin yadda ake wanke wajen,motsawa tayi umma ce tace"ya hakuri safna nasan da zafi,jin muryar umma yasa ta a ranta fadin"ohh yakamata yau daya na tsaya na saurari matar nan naji mai sakina ke ji idan suka zauna.

Abba ne ya shigo yana fadin"ameenatu dole sai dai ku shirya keda yarinyar nan ku tafi garin nan saboda yace"wanann babban tsafi ne aka mata wamda bazai iya warwaru wa ba dole sai dai idan tana wajen,umma ce tace"indai sihirin zai karye ni kuma zan taimaki yarinyar nan, allah sarki najwa, amma abbbh safna fa.

Abbah ne yace"sai ki kyaleta ta zauna ita kadai tinda bazata iya zama a gidan mijinta ba,umma xe tace"aa abbah kayi hakuri hannunka baya rubuwa ka yanke ka wullar, ba kin zama tayi ba kewar gida tayi shi ne fa ta tako ta ho,shikenan abbah ya furta ya mike, zai shiga falonsa ne yace"sai ku tafi tare,umma ce tai murmushi daidai lokacin da safna ta bude ido tana dariya son ranta.

Umma ce ta kalleta tace"tashi to ki wuce dakin sakina tinda najwa ta kwace dakinki,safna ce ta kalleta ko me zata ce kuma sai naji tayi shiru ta mike ta nufi dakin sakinan, ita kanta umma abin ya bata mamaki ganin ta tafi kai tsaye ba tare data kara mata magana ba, amma ta alakanta hakan da najwa da take dakinta.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 31

Alhj gambo ne ke fesa turare daidai lokacin da mufeeda ta shigo ta zauna tana kallonsa, sai da ya gama fesa turaren sanann mufeedah tace"haba dan allah jarumi na, kai kenan tinda aka fara wannan shirye shiryen baka nemana,kuma fa kasan ina da buqatar ka, ko na nemeka ma tafiyarka kake, kafin na ankara,alhaji gambo ne ya tsaya a ransa ya furta"me zan dake ga 'yammata can a leda sai na za6a zan 6are.

A zahiri kuma murmushi yayi yce"haba mana tawaan, namiye zaki wani 6atawa kanki lokaci, kinsani nan da kwana 2 na zama shugaba mai fada aji a cikin kungiyar mu, ki fmbari komai ya daidai ta mana,mufeeda murmushi tayi sanan tace"to yaushe zaka dawo,kallonta yq sake yi a karo na 2 tace"nan da kwana ki 5,amma fa ba tabbas, dan haka ki kulamin da kanki kinji shalele.

Murmushi tayi sannan ta rakasa sai da ta tabbatar ya tafi sannan ta juya zuwa kitchen, wajen masu aiki ta tsaya tace" ku tabbatar kun raba kun ba wa kowa abincin nan kuma wallahi dik wanda yayi min ba daidai ba ina kallonsa ta cikin camerar nan, hadi da nuna musu wata camera, nan fa kowa rai ya raina fata, yayin da mufeedah ta juya ta tafi dakinta.

Binta nayi sai dai ina shiga nahango wani katon mutum baki wulik, mufeedah tana zuwa ta fada jikinsa tace"washhh dama nayi kewarka, gaskia bazaka tafi ba sai rananr da alhaji zai dawo zaka tafi, bakin mutumin ne yace"angama ranki ya dade, wa zaiga kayan****ya tafi ya barsu ai sai jahili, daga nan ne fa naga labari ya fara canjawa nikam na janyo musu kofar na fito.

BAYAN KWANAKI 7 (One Week)

Najwa ce zaune a wani katon soro, sai umma da take gefe ita da safna,malamin ne ya kalli najwa yace"tashi kije ciki ki ce yakumbo lami ta baki abinda na bata jiya,tana fita ya juya ya kalli aminatu yace"alhamdulillah, sai dai muyiwa allah godia, domin cikin ikonsa allah yasa an karya tsafin dake jikin wannan baiwar allahn, daga yanzu bazata kara zama wata dabba ba.

Sai dai ba daina maganin za ai ba, saboda har yanzu bata gama warkewa ba,amma kuma zaku iya tafiya zan baku wasu magunguna da zakuna amfani dasu, nan da kwanaki 30 zata dawo yadda take,aminatu sai zubawa malam adam godia takeyi, wanda shi kuma ke fadin ba komai,insha allahu komai yazo karshe..

A wanann ranar ne kuma suka fara tattara kayansu, zasu dawo kaduna daga kano,nikam lamarin safna har mamaki yake bani jin tayi shiru kuma dik abinda aminatu tace take takeyi ba wata gargada, da fari na dauka sakina ce sai daga baya kuma na lura ashe safnan ce dai mara kunya.

Abbah na gida shi da safwaan suna kokarin shiryawa dan zuwa kano, wayar umma ce ta katse masa shirin tana fadin"ku kwantar da hankalinku ba sai ma kunzo ba, yanzu haka mun dakko hanyar dawowa, domin kuwa malam adam yayi wa najwa aikin sati 1 kamar yadda ya fada, sannan kuma aiki yayi kyau, insha allahu gamu nan dawowa, jin haka yasa abbah yin godiya ga allah yana mai tina muguntar da mahaifinta yayi mata kawai dan san abin duniya.

Fitowa yayi safwaan na jiransa,abba ne ya gaya masa yadda akayi sannan yace"abinda zai fi su zauna su jirasu, safwaan a fili yake nuna murnan sa, daidai lokacin da rayyan ya shigo shi da abdallah,safwaan da kansa ya mike ya basu wajen zauna, amma fafur sunki zama a kujera, dole sai a kasa kan carpet suka zauna.

Bayan sun gaisa ne abba yace"rayyan ya aikin naka, fatan dai komai ya daidaita,rayyan ne yace"abba komai lafiya lou kuma aiki anyi nasara,abbah ne yace"masha allah, amma kuma safna yanzu suka dakko hanya daga kano, amma idan suka dawo zan kokarin kiranka, ko na saka safwaan ya kiraka, bai jira mai zai ce ba ya mike ya fita daga gidan.

Yana fita suka haye kujerun dakin nan fa suka kalli safwaan suka saka dariya, abdallah ne yace"ohh mutumina kai wai bazaka yi aure bane,safwaan yasan dashi suke a take yasha mamur irin ba mutuncin nan,safwaan ne ya kallesu yace"kuyi ku gama domin ni idan na tashi aure matata sai tafi taku kyau da kuma, rayyan ne yace"aa allah baka isa ba kuwa, safwaan dai shiru yayi ya kyalesu, saboda shi can dama baya san musu.

Safwan ne ya mike tsaye yace"idan kun gama jan maganar zaku iya tashi ku tafi, mutanen banza kawai ni office zan tafi,abdallah ne yace"to da mudin ina zamuje idan ba office ba,bai ce musu ta tafasa ba yayi gaba, abdallah na ta dariya yayinda rayyan yasan halin sa yaki dariya, saboda yasan muguntar safwaan.

Haka suka fiti daga gidan, daidai lokacin da habiba ta shigo gidan tana dangyasawa ga kuma kanta dauje da bandage, gefe da gefe kuma 'yan sanda ne,turus abdallah, safwaan rayyan sukayi suna kallonta.

*MAHAIFIN MU NE SILA*

*By*
_*WALEEDAH MUHAMMAD*_

         QUEEN WALEEDAH

   _HAZIƘAI BAKWAI DAGA_👇

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

        *T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
       💪😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
        💪😊

https://whatsapp.com/channel/0029VbB4z8xCnA7sRc849y0F

Whatsapp Channel

💮💮💮CHAPTER 2💮💮💮
©®WaleedahMuhammad.

Page 32

Zainabu ce ta fito da sauran 'yan kudi tace"nabila kizo kice ki saro kayayyaki nan ga fahad na kokarin tafiya sai ki bisa ya ajiye ki ko, nabila ce ta turo baki tace"umma ni wallahi bazan iya zuwa ba, umma ja na fa suke suna ce min mai kanwar kira, umma aunty najwa ce fa kurar,umma kallonta tayi ita kanta abin baya mata dadi amma ta daure,fahad ne yayi saurin tashi yana fadin"umma kawo kudin naga dai mitum baya canjaawa kansa kaddara ko, dan haka ki kwantar da hankalinki kuma da suke cewa najwa kura na tabbata kuma inaji a rai na zatq dawo da alkhairi.
Chapter 18 · 0% Book details