← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 57

Sashe 9

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Rukayya da take zaune a falo itada Hajiya Jamila sauran yara sunyi shirin islamiyya suntafi sai Yasir kadai ya rage a gidan da shiko yana gurin Aunty Amina yanama babynta Ummu kursum da take goyo wasa ,AbdulMalik a haka yashigo yasamesu da sakon Rufaida a hannunsa a leda abindama batace ba saida yasiyomata yayi musu Sallama suka amsa masa Rukayya tace "Sannu da zuwa Yaya Abdulmalik"ya amsa mata kamar anmasa dole da" yawwa"Hajiya Jamila tace "ya aikin naku"yace "Alhamdulillah"daganan yasa kai zai wuce bangarensu ganin sakon Rufaida a hannunsa kuma baiganta a gurinba yasa shi cewa" Umma ina Rufaida naga shiru banji motsinta ba" baki ta ta'be tace "tana kitchen ta doramana abincin dare" ya 'dan juyo ya kalli Ruqayya yace"Umma ita Ruqayya ai yakamata taje suyi tare"tsaki Hajiya Jamila tayi tace"Abdul malik ka kiyayeni fa bandama shirme irin naka ina zaka hada Ruqayya da Rufaida kodai kai wawane sai haka tuntuni nake nunama banbancin dake tsakaninsu"AbdulMalik yace"haba Umma ni haryau bana ganin banbancinsu a zahirin gaskiya ma Rufaida tafi Ruqayya dangantaka da gidannan ta kowacce fuska gaskiya"Hajiya Jamila data fusata tace" to yima Ruqayya gori cewa tazo gidanku cin arziki arzikin da duka yaushe ubannaka yayi kuma kasani komai zakace idan ni kahanani fa'dar banbancin dake tsakaninsu to bazaka hana duniya fada ba,abinda bakowanne biladama zai iya ba saiga wancen matsiyacin yayi da kuma waccen...."AbdulMalik ganin Ummantasu bazata tsaida wannan cin zarafinba yasashi harda saurinsa dan yasan indai zai biyemata tone tone zatayi abinda yasan yana daga cikin kaddarorinsu to akanme za'a dinga jagwalgwala magana dashi haryau yake tantama ga waccen labarin kanzon kuregene da saboda suma suji waccen tsanar kamar yadda ita kiri kiri take nunawa ga wancen rayukan masu matukar muhimmanci a rayuwarsu tabasu labarin da babu kamshin gaskiya a ciki dukda dai mahaifiyarsu ce tabasu,to shi koda ma hakanne shi baiga abin da zaisa yaki 'yan uwansa ba danshi yama jahilci labarin tunfarko kodama gaske ne,Rufaida da take kokarin shigowa falon ta fadawa Hajiya Jamila ta gama abinda tasata mai zata kara dorawa a kunnenta ta fara jiyo maganganun Hajiya Jamila da yaranta data fahimci akanta ake maganar bata karasa jin maganar b takoma kitchen din gudun kada AbdulMalik yazo yasameta anan da haka yasata komawa kitchen din dukda bawai tsaiwar ta gulma bace a'a kowa 'dauka zaiyi itace tana kuma tsoron Hajiya Jamila taji Abdulmalik ya mata magana ta zata ra'be take musu shikenan kuma abin ya zama abin magana a gidan tarasa wannan wanne labari ne kuma wanne tarihi ne dayake shafar rayuwarta har yakawo tsanar da Hajiya Jamila a duk cikin zuriyarsu sai tace tafi nuna musu dukda ita 'din ba zuriyarsu bace kai tsaye a'a aure yakawota zuriyar tasu amma tasan abune babba karon farko ta fahimci shine ya raba wancen ran mai muhimmancin gaske a zuciyarta shine yajawo tafiya mai nisan gaske a tsakaninsu da haryau babu waiwaye,tanbayar zuciyarta take yaushe zatasan labarin waccen rayuwar ta baya da tasan tabbas itace rusa waccen rayuwartata kuma take cigaba da shafar rayuwartata dumin da taji a kuncinta yasata sa hannu ta duba abinda tasan tabbas shine dama ta gani wato hawaye ,tuno waccen rayuwartata dama wadda takeyi yanzu shine abunda a kullum yaake kokarin da gula lissafe lissafen rayuwarta dama tunaninta kai tsaye zama tace Sallamar da taji AbdulMalik yayi kitchen din yasata saurin daidaita nutsuwarta ta goge hawayenta kafin ya karasa shigowa amsa masa sallamar tayi yayi murmushi ya karasa inda take tsaye tana kokarin cemasa "Yaya sannu da zuwa"Ya amsa da" yawwa Rufaida"kafin ya'dan ha'de rai yace "Rufaida"ta amsa da " na'am Yaya"cikin muryar raunana ta amsa masa"ya sake murmushi karo na biyu ganin yadda ta ru'de dagajin kiran sunanta yana mamaki haryau Rufaida bata canza ba daga yadda take,dukda gata da 'da harma ya kusa shekara uku ita kanta a shekaru zata kai 22 a yanzu haka koma da uku amma haryau yarintarta ta rashin son hayaniya da shiga abinda bai dameta da hakurinta yana nan yadai fahimci wannan halayyar a jininta suke"magana AbdulMalik ya cigaba dayi da cewa"yanzu Rufaida Fisabilillah dukda matsayin da kike dashi a gurin mu kinada wata bukatar ta wani abu kudi ko abinci ko abinsha ace bazaki tanbayemu kai tsaye ba muyi miki ba sai kin cemin zakimin transfer haba Rufaida duk abinda muka miki aike din tamuce bama bukatar ki bamu abin hannunki,muddin muna dashi idan bamudashi mumasu tsaya miki ne da karfinmu,bare ina tunanin dubu 2 zuwa uku ko ma fiye da haka ko Abdussalam kika tanbaya ko Hassan ko Hussain ba zata gagare suba haba Rufaida tuntuni kinsan kina bukatar wani karamin abu wato caza danni dai a a karamin abu na dauketa dan inada ita kamar abin banza a dakina tunda nasan zata kai 4 ko 6 duk wayoyin da nayi da caza dinsu a dakina ace bazaki ce na baki ba ko Umma da kike gudun taji kinsan ba zata hana na bayar da abuba tunda kinsan bata hana kabayar da abu bare ma kinada lambar Iowa a gidannan name tunani haba mana ki zama wayayya ta wasu fannonin mana"Rufaida da sai yanzu take ganin laifinta ne dan ita kanta amsar dalilin da zata fadawa Samiha Idan ta sake kiranta jin dalilin kiran nata bata samuntan bazatama iya fadar wancen dalilin ba dan baikai matsayin ka fadawa wani ba tunda akwai hanyoyi da dama na magance waccen matsalar,sai dai ita dalilin kin maganar gani take kamar zata matsawa mutanan gidanne kaita cewa ayima ayima ko abani abani ita bata saba dashiba mijintama da yarasu bata yimasa,bare tayi anan da surikartata bata raina abin magana ,Rufaida tace"Yaya kaya hakuri na daina"yace "Yawwa shikenan ina Yasir din ne ga alewa nan na siyomasa" Rufaida tace" yana can gurin karamar Auntysa Ummu kursum yana mata wasa"AbdulMalik yace "ok to ga naki sakon nan" ya bu'de ledar ya dauki wata ledar ya aje mai dan girman yana cewa bari nakaiwa Yasir nashi"Rufaida tace" Allah ya kara bu'di"AbdulMalik yace "Amin"kafin yace "au na manta ina Inna Lamin" wato mai tayasu aiki Rufaida tace "taje gidan Gwaggo Lariya" AbdulMalik da ya gane Gwaggo Lariyar kanwar kakarsu ce mace yace"lafiya dai ko"Rufaida ta visa da cewa "lafiya lau abincinta ne ba'a kai mata ba har 'yan makaranta suka tafi"yace mata "Ok ", da yasan halin Ummansu Hajiya Jamila sarai ko 'ya'ya zasu fasa gidan indai Inna Lami na gidan aiken duniya ita zata yiwa kaikace Inna Lamin sa'ar tace a haifema Inna lami ta haifi Hajiya Jamilar amma nuna ikon Hajiya Jamila kamar kanwar kanwartama ta maida Inna lamin sai kace ita ta bawa kanta daular da take ciki ba Allah ba itama Inna Lamin sai Allah ya bata Iran yaso hakan da haka yake cigaba da tunanin halayyar mahaifiyartasa datayi sanadiyyar kawosa duniya ,yana kokarin ficewa yaga Rukayya tsaye a bakin kofar kitchen din da Hajiya Jamila tace ta biyo AbdulMalik taji neman maiyakewa Rufaidan ha'de rai AbdulMalik yayi daya ganta cikin rawar jiki na nuna alamun rashin gaskiya tace masa" dama Umma ce tace na samo mata ruwa a kitchen"tsaki AbdulMalik yayi yace" tanbayar ki nayi abinda yakawoki koko yaya?" Rukayya kai ta girgiza alamun a'a wucewa AbdulMalik yayi Inda yana kallon Ruqayya ganin ya tafi yasata bin hanyar komawa falon danko kitchen ma bata waiwaya kai kawai AbdulMalik ya girgiza yana tunanin halin mahaifiyarsa mara kyau wato bata yarda da su ke'be shida Rufaida ',year uwarsa suyi fira ba sai ta sa anjiyo mata,ita batasan shi baya gudun fadan gaskiya ba koma gaban waye ba shifa aransa cewa yake baza'a masa abinda akayiwa yayansuba ya yarda yanzu za'ayi kaca kaca dashi danshi bazaiyi biyayya gurin abinda zak cutu ba kuma za'a cutar da abinda yakeso ba shiyasa yake da kudure kudure aransa da yasan bamai yunkurin hanasa tunda kudurin vamai cutarwa bane da haka ya karasa sashensu da sai ya kammala abinda take zai fito kaiwa Yasir alewarsa
Chapter 9 · 0% Book details