← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 57

Sashe 31

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kyalesa dai baffa ni narasa maiyasa yaran nan suka raina Danbatta, Har da fa yaron nan Bello"
"A'a Yakumbo Allah ba mu raina Danbatta ba"

Hira suka cigaba dayi inda Baffa ya kallesa yace"ya labarin bikin naka yake , wata nawa a ka sa"

Kansa yana duban 'kasa da yake 'ko'karin maida hawayensa yace "Baffa ai an fasa biki su Abba Sule sunce bazan aure taba"

Baffa da ransa yake 'bace ya soma cewa a kanme bari na kira Sulen naji akan me? shi duk sanda yaran nan zasu nemi aure sai ya kawo wata matsalar ta daban ita kanta yarinyar da Ahmad ya aura sai da yaso kawo wata matsalar mara tushe, To inda baku yi auren ba mai yakeso kuyi"

Yakumbo tace "a'a karka kira sa tunda sunfimu iko da yarannan ka barsu kawai mu zuba musu ido sai dai mu tayasa da addu'ar Allah ya ha'dasa da wata ta gari idan kuma da rabo saika ga ya aure ta komai 'kin su da haka"

Baffa ya amsa da Amin

Tare da kallan Ra'uf ya ce "masa Ra'uf kar kuma hakan ya saka nemi yiwa 'yan uwan mahaifinka da mahaifiyarka rashin kunya ko nuna rashin darajasu domin dai ba kada kamarsu , Kuma kowa ha'kuri yake da halin 'dan uwansa wata rana sai labari"

"Insha Allah Baffa bari na je na gaida su Umma ban shiga ba 'dazu kuma gobe na ke son tafiya na kira Bello ya samamin Viza za mu tafi jibi nida Ammi zamu kwana gidan Bello daga nan saimu tafi tunda yacemin jirgin safe za mubi"

"To shikenan sai ka fito"

Da haka ya mi'ke yabar 'dakin ya sami Mukhtar suka cigaba da fira a dakin da suka sauka*JININMU 'DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL
Wattpad SadiyaIbrahimKhali

SHAFINA TALATIN DA UKU 33

_Dady ya kalli Momy Hannatu yace ya banga Ra'uf a falon ba ta dubesa tace "ya tafi Kaduna zai bi yaya Ma'u su tafi tare jibi"

"Kan wannan abun zai ta fi shikenan to yafi ruwa gudu yaro mara sanin ciwan kansa akan wannan 'karamar magana ya tafi ba sani na idan yana ganin tsira zaiyi idan ya tafi kadunan

Momy shiru tayi tana jinjina al'amarin Dady lokaci 'daya ya birkice saboda san zuciya irin nasu sun hana yaro auren za'bin ransa falon Momy Hannatu ta bari ganin zaman ma baida anfani a gurin ta Dan gaskiyya saita fa'di gaskiyya indai ta zauna su kuma ta lura bamai san gaskiya a cikinsu

________________________________
Abba Aliyu da ya sami Ummi Hauwa'u a zaune gefen gado gefenta shima ya samu ya zauna da shigowar sa kenan cikin 'dakin ya dubi ummi Hauwa'un yace

" Hauwa'u magana na keso muyi bata wasa ba kuma, yanzu yaya Bukar ya sanarmin zai tafi da Rufaida ko dan ta manta da yaron nan gaba 'daya,kuma su fahimci juna itada Ahad kafin ayi aurennasu.

"Amma Abban Abdul ba ayi shawara da niba kwatsam sai azo min da maganar tafiyarta kuma harma da kudurinku na auren Ahad kana sane da kiyayyar da mahaifiyar yaron ke nunamin nida 'ya'ya na

"Ki fa'damin wake da iko da yarinyar nan ne wai"Abba Aliyu yayi firicin da alamun ransa ya soma baci

"Cikin sanyin murya tace kai ne amma gani nayi kasan komai akan zaman da mukayi nida Hajiya Jamila yanzu kuma ace Rufaida ta auri danta"

"Cikin 'bacin rai Abba Aliyu yace"ke harkinada sauran magana akan 'ya'yana kinmanta da abinda kika mana dake danasan da sa hannunki a ciki"
*****"*"
Ra'uf ya fito Cikin shirin sa shadda milk colour jikinsa 'dinkin mai yalwataccen fa'di da tayi matu'kar yi masa kyau da 'kara haska sa, ya fito da'ki da Mukhtar tuni ya fice da kayan sawarsu yasa a boot da yake waje yana jiran fitowar Ra'uf, da Baffa Ra'uf yaci karo tsakar gida yana 'ko'karin yin alwala

"Baffa sallar walhar ce"
"Eh Abdur-Ra'uf ba dai har tafiyar ta tashi ba
Eh baffa sai dai kuyi mana addu'a Allah ya 'kaddara saduwarmu"

"Baffa ya furta amin da ya ajiye butar ya 'karaso gun Ra'uf da yake 'ko'karin su fita tare da Ra'uf, Yakumbo da ta shigo gidan ta dubi Ra'uf da cewa "ba dai har ka fito ba tun yanzu, Wato da tuni sai da nazo na iske tafiyarka daga fita makwabta yi musu barka shiyasa Baraka tace na tashi kar ka tafi yanzuma take shaidamin ashe har gidan ka shiga jiya kayi musu abin arzi'ki

" A'a Yakumbo zan Shiga nayiwa su Kawu sallama , Eh mun shiga nida su salmanu da salmanun yace min mu shiga gidan 'kawar Yakumbo, sai dama muka gaisa na gane ta Gwaggo Baraka ce sai dai naga kamar ta fiki tsufa yanzu"

"Banga alama ba zaka jira dawo wataba, Abdul-Ra'uf kenan ai Baraka abar a tausaya mata ce musamman yanzu da ta 'kara tsufa a zaman 'kauye kenan da kaya basu lunka ku'din zabi ba kamar yadda suke yi a cikin birnuka,Yaran nata duk sunyi karatu amma ba wanda ya samu abinyi yanzu haka dai iro yana birni ya kammala digri yana tsaron shagon unguwar da ya zauna har ya gama karatun to gaba 'daya ku'din da yake samu basu taka kara sun karya ba kuma a hidimar iyaye suke 'karewa a hakan ma badan sun isa ba"

"Da gaske nake yakumbo ina zan tafi ban sake saki a ido ba, To amma Yakumbo mai yasa baki fa'dawa Momy ba tasa Dady ya sama masa aiki"

Baffa yace "kaga Abdul-Ra'uf ta ho ka tafi ka daka ta Yakumbon ku ba abinda zaka yi tunda dai ba ka tafi ba ta dawo ai shikenan, ka shiga ka yiwa kawun naka sallama"

Suna 'ko'karin fita Yakumbo tace "Ahaf a baki ba amma nasan da tuni ka tafi ba muyi sallama ba"

Baffa yace "saiki ta yi dai amma wannan abokin nawa ba haka yake ba"

Yakumbo tace"kana dai tare masa ne kafin mu jiku a rana"

Da haka suka 'karasa 'bangaren kawu Lami'do da suka tarar suna karyawa gaisawa su kayi sauran yaran kawu biyu duk maza suka koma gefen Ra'uf suka zauna
Umma ta ce "Amira jeki kawo wa su Baffa Abincin karin kumallonsu yanzu nake cewa ta je takaimu Ku tace sai tayi karin kumallonta zata kai muku
" Baffa yace barshi Zuwaira Yakumbo tun asuba ta 'dora sanwa saboda Abdur-Ra'uf mun 'karya tun 'dazu Allah ya yi muku albarka yasa kuma naku su yi muku"
"Umma tace" Amin Baffa"
Ra'uf ne ya dubi Amira yace "Umma Amira tayi girma kyau a ha'data aure da Bello sai mu'kara 'karfafa zumunci ni jiya ma banganta ba a gidan"

Umma tace "Ai kasan yaran yanzu basa san auren zumunci wani 'dan bayan gidan nan take so,ta je gidan kawu isuhu sai dare ta dawo"
"Kin ji Umma shine fa ke sona ba ni ba Amira ta fa'da"
Kawu Lamido yace" ina wani so da yake miki tunda kinsan tsinke baya saidawa kin 'ki ha'kura da shi, Ga makaranta saura watanni Ku gama makarantar gaba da fira mare
Baffa yace "Bar ta Lami'do da yaron nan abokin Ra'uf na birnin tarayya Abuja da ya sake dawowa zance ya turo magabatansa"
Amira ta zun'buri baki tace gaskiya Yaya baka kyautamin ba dan ni bana son wannan abokin yaya Bellon nan

Ra'uf yace "kyautawar kenan yarinya , to shikenan tunda ba kya son sa a ha'daki da Bello dan ni banida sha'awar mata biyu ai da nayi ta biyu dake"

Amira tace "Allah ya kyauta nayi auren Zumunci, ta 'daya ma ka kasa ka tsaya ruwan ido bare kayi ta biyu dani"
Ra'uf yace "eh naji gwara ni keda da zaki ba wan ba 'kanin fa"
Baffa ya ce "nidai nagama magana ta Bilal zaki aura abokin Bello"
Ra'uf yace dama Bilal ne ai da shi a kayi bikin Ahmad yaje har Sakkwato 'daurin aure yana da kirki sosai Baffa"
Amira gurin ta bari saida zasu tafi rakonsa ta fito domin rakonsa

'Bangaren Kawu Sunusi suka shiga harda su Kawu Lami'do basu jima ba a 'bangaren Kawu Sunusi ba suka fito inda suka fito tare domin ganin tafiyar sa har bakin mota suka rakasa kafin motarsu su tashi su juyo gida inda sauran yaran ke cewa yaushe zai zo 'daukarsu, Yace musu sai sun ganshi da sunga yazo tafiya ce

Misalin 'karfe biyu suka isa Kaduna ana fitowa daga masallaci Motar su ta dira sai da suka tsaya sukayi sallah a wani masallaci kafin su isa gidan

"Horn biyu a ka bu'de musu gate 'din gidan a ' Harabar gidan suka tadda Baffa Alhaji"

Da murmushi ya tari Ra'uf yana cewa "maraba da bakano kaje kano ka guji Kaduna garin gwamna"

Hakan ne yasa Ra'uf sakin ransa da tunanin ta yiyu baza'a sake masa maganar Rufaida ba yace " yawwa 'Dan tsoho mai ran 'karfe, amma wa zai 'ki Garin Gwamna"

Mukhtar ya fito a motar suka gaisa da Baffa Alhaji

Kai tsaye yana shiga falon 'dakin Ammi ya shiga da ya yi sa'ar bai sami kowa a falon ba
A zaune ya sa meta tana 'ko'karin ha'da kayanta
Sallama yayi
TaAmsa masa tare da 'dago kanta
Kafin tace "wato sai yanzu zaka zo ko ka fison tafiyar dare ko?

" a'a Ammi ki yimin afuwa ina Safiiyyan"inda ya 'Dora da gaishe ta amsa gaisuwar
ta dora da cewa tana gidan Malika sai zamu tafi zamu dauketa mu wuce,na kirkira ka kashe wayoyinka tun jiya nake 'ko'karin kiranka ba ta shiga ba saboda Momynku ta cemin ka taho"

"Eh Ammi na biya ta Danbatta nama su Baffa sallama, tun a Danbattar na kunna wayar da muka je amma babu network mai 'karfin da zai yi kira"

Ammi cikin nuna damuwa a kan fuskarsa da tausayin yaron nata mai tsananin biyayya a gare su da bai kamata kan wani banzan dalili a hanasa za'bin ran sa ba da ta tabbatar ba wani 'kau'karar dalili ba ne amma an rabasa da Rufaida saboda suna so suna na isar su akan Ra'uf dan datasan abinda zata tarar ke nan da bata zo nigeria ba magana ta soma yi tana cewa "Ra'uf dan Allah kada Rabuwarka da Rufaida ya janyo wani sauyi daga rayuwarka dama wani lokacin sai ka rasa wani abun kake samun wani abun a rayuwa"

"Insha Allah Ammi"
Ammi tace "yawwa Ra'uf"
Chapter 31 · 0% Book details