← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 57

Sashe 46

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin sallamar Wahid a 'dakin yasata kokarin tashi daga kwanciyar da tayi a gado tana danna wayarta ta tashi zaune tana amsa masa sallamarsa
Kallon Rufaidan yayi yana kokarin zama gefen gado yace
"Badai har kin kwanta ba"
Murmushi tayi ta kallesa
"A'a ina kokarin kiran Samiha ne,kuma nagama bata dagawa"
Yace
"Kila bata kusa da wayar ne"
Tace "Eh nima nafi tunanin hakan"
Dube dube ya fara kafin yace
"Ya banga Yasir din ba"
"Gashi nan dakyar na samu ya kwanta bayan ya gama rigimar tafiyar Yusuf" tayi maganar tana nuna masa Yasir din da yake kwance gefenta
Murmushi Wahid yayi yace
"Ai Yasir da Yusuf shakuwarsu kamar tagwaye"
"Gaskiya kuwa" fadin Rufaida
Gyara murya Wahid ya danyi ya dubi Rufaida ya soma magana
"Dama inaso muyi wata muhimmiyar magana"
Kallonta ta maida kacokam garesa tace
"Ina saurarenka"
Wahid ya gyara zamansa ya soma da cewa
"Rufaida,nasan dazu kunyi maganar auren Rukayya da Umma takeso na kara keda Luba sai dai maganar gaskiya bana son aurenta saboda ke irin halarcin da kikayimin da biyayyar da kikayi wa su Abba dan nasan tuntuni ba nine zabin da kike so ba,amma da Allah ya zaba miki ni sai kika hakura,ki amshi zabin da Allah yayi miki da hannu biyu,kuma kika zama mai hakuri da irin barazanar da Umma tasha yi miki,da zagi da cin zarafinki kafin auranmu dukdan saboda kice kin fasa aurena,dama yanayin zaman mu yadda yakasance bayan aurenmu da Umma da Rukayya suka shigo cikin rayuwarmu,kuma suka riqa yi miki abubuwan da zasu bata ranki amma duk kika jure,amma yanzu bana tunanin nayi miki adalci muddin na amince da abinda Umma take so nayi,na auri Rukayya,saboda nasan Rukayya sai tayi barazanar tarwatsa zaman mu,ni kuma banaso na rasa mace kamarki a cikin rayuwata"
Murmushi Rufaida tayi jin ya kawo karshen zancensa tace
"Karka damu Yaya Wahid,ka aureta din,insha Allah babu abinda zai faru garemu,kuma zata kasance alkhairi a tare damu,zamu rayu nida ita saboda faranta ranka,da tarbiyantar da yaranmu hanya madaidaiciya"
Murmushi yayi jin maganar da tayi yace
"Haba Rufaida wannan tunanin na kine kawai ba nata ba,ita abinda zai kawota rayuwarmu so take ta wargaza zaman mu ni da ke kamar yadda Umma take so"
Murmushi ta sake yi tace
"Karka bari wannan tunanin yayi tasiri a zuciyarka domin Allah shine mai gyara ko wanne al'amari ba tare da munyi tunanin hakan ba"
"Eh haka ne,mata ta,zan fahimtar da Abba dan shi haryau yakasa amincewa da maganar auren,saboda yana tsoron karsu yima diyarsa wani abu"fadin AbdulWahid
Rufaida ta murmusa jin karshen maganar Wahid din tace
" Allah yana tare da mai gaskiya,nayi alkawarin zan rike gaskiya a zaman mu,zan kira Abba na sanar masa indai saboda nine bayason ka auri Rukayya toni nace babu komai,saboda inasan mijina ya kasance mai biyayya ga mahaifansa,bana so na zama silar kasawarsa"
"Au harda,kinasan mijin naki zaki fadawa Abban" fadin AbdulWahid
Rufaida ta 'dan hararesa tace
"Eh mana tunda kasan ba nida kunya"
Dariya yayi yace
"Oh dan kin fadawa Abba irin son da kikewa mijinki shine rashin kunya"
Ta sake harararsa tace
"Oho ma"
Ya dan sake yin murmushi yace
"Wallahi Rufaida,ban taba tunanin zaki so ni haka ba a baya can"
Ta 'dan zaro ido
"Saboda me"
"Hmm,saboda ba nine zabin ranki ba"
Fadin Wahid
"To waye zabin ran nawa bayan gaka"
Fadin Rufaida
Murmushi yayi jin maganar ta yace
" 'dan uwanki shine zabin ranki mana,ni rashin uwa ne yasa akayi uwar daki dani"
Murmushi tayi ta dan zaro ido kadan tace
"Ko daya kaine dama zabin da Allah ya zaba min,kuma waye dan uwan nawa nufinka Ra'uf ai bamuda dangantaka da shi"
Dariya yayi kadan yace
"Eh mana dan uwan kine,tunda kun hadu a dangin Annabi Adam"
Murmushi tayi tace
"Ah to sai dai hakan,yawwa bana fadama,ka dai na min maganar wani tsohon saurayi na ba,bansan mai yasa baka kishi na ba?"
"Sorry matata,ina kishinki matukar gaske,amma kuma yanzu ke matata ce babu mai kwace min ke yanzu,ji nayi kawai yau ina sha'awar tuna baya"
Ya karasa maganar yana jiran jin amsar da zata basa sai yaji tana cewa
"Tuna bayan har saika tuna da Ra'uf kuma bayan babu wata alaka tsakanin mu bare har yasa mu dinga tunawa da shi a cikin bayanmu"
"Muna da alaka da shi a bayanmu mana,tunda ya taba shiga cikin rayuwar kanwata"
"Hmm to naji,abar maganar tasa
Cewar Rufaida
" shikenan,amma wallahi ban jidadin abinda ya faru ba da ya zama sanadiyyar baki aure saba,nasan da shine zai kula dake fiye dani"
Karar wayar Rufaidan yasa Rufaida maida maganar da take kokarin fada ta maida hankalinta ga wayar ganin Samiha ce yasata sakin murmushi ta nunawa Wahid wayar
"Kaga mutuniyar taga kiran ta biyo" daganan ta kara wayar a kunne tare da gabatar da sallama
Samihan ta amsa
Rufaida ta fara tsokanarta
"Uwar biyo ya kike ya ya takwarata,yaya Ahmad"
"Wato uwar biyu ko?,Duk muna lafiya yaya Wahid,da surikina"
"Eh mana uwar biyu zance tunda ni banida shi,Gashi nan yana jinmu,Yasir kuma ya kwanta"
"Zaki yi shine,yawwa bawa Yaya Wahid wayar naji ya akai zai karo mana kishiya"
"Gurin wa kikaji wannan zancen"
"Kinga nidai bashi wayar muyi magana"
Da haka Rufaida ta mika masa wayar tana ce masa
"Ungo Samiha tana so ku gaisa"
Ya amsa wayar da murmushi kan fuskarsa,yasa a kunne ya fara magana
"Assalamu Alaikum uwar biyu"
"Wa'alaikumus salam ,au harda kai amasu cemin uwar biyu zan rama ne"
Yayi dariya
" Eh mana,amma kafin ki rama zaki rame"
"Eh amma dai na rama,hmm ba mu gaisa ba Yaya Wahid, ina yini ya aiki ya kawata"
"Lafiya Alhamdulillah,ya UK ya maigidan naki ya takwararmu"
"duk muna lfy ba lafiya ba"
"Subhannallah maiya sameku"
"Eh to cutar kishi ke da munmu munaso muji maine kawarmu bata yi maka,har daga aurenku zaka kara mata kishiya"
"Au sai mace bata yi ma wani abun zaka kara aure kun manta karin auren Allah ne yace ayi,matukar mutum yana da sararin yi kuma yanada bukatar karawar ,kuma yasan zai iya adalci a tsakaninsu"
"Eh hakane amma dai"
"Amma me fadi"
"Kamata yayi kukai shekara kamar hudu zuwa biyar sai a fara maganar auren"
"Nima naso hakan amma Umma ce take so nayi yanzu,saboda Rukayyan ta kusa kammala karatunta,sai tayi service bayan aurenmu,kuma kawarki ta fahimce ni"
"To Allah ya tabbatar da Alkhairi yasa ta gari ce"
"Amin Samiha,yau ma tukun waya fada miki wannan zancen"
"Ai kasan abun duniya baya buya"
"Hakane kam,amma dukda hakan ana samun wanda yake fadar wani zancen har wani ya sani"
"Eh to haka ne"
"To Waya fada miki kodai Kawarta kice?"
"Ko daya kaga bata wayar ma"
"Au bazaki fadamin ba"daganan ya mikawa Rufaida wayar da take jin abinda suke tattaunawa a wayar dukda batajin abinda Samiha ke fa'da amma ta fahimci akan mai suke tattaunawar yana mika mata wayar ya fice daga dakin
Samiha ta soma magana
" yanzu Rufaida kina ganin Wahid yayi miki adalci duka yaushe kuka yi aure da zai kara aure,abin ya dauremin kai kodai kina masa wani abu ne"
"Babu ko daya Samiha umarnin Ummansa ne karin auren da zai yi wadda zai aura din ma Cousin sister dinshi ce"
"Au wai banda kokarin kashe kin data kusa yi kafin auren shine zata hada ki kishi da 'yar uwarta bakin ciki ya kashe ki kenan"
Jin furuci Samiha yasa Rufaida ta zaro ido kamar Samihan na ganinta,da alamun mamaki
"Waye ya baki wancen labarin ke kuwa"
"Aunty Samira ce ta fadamin,tun sanda abin ya faru,ganin baki min maganar ba yasa ta nima ban miki ba,gaskiya Rufaida wannan auren naki hatta Ummi Hauwa'u bata sanshi dandai yazo da rabo ne,amma tun muna yara kike bani labarin abubuwan da Ummansu Wahid take yi muku,kuma nima nasha gani da ji,don wallahi da na isa na fadawa Abbanku da ba zan yarda a aura miki Wahid ba,duk da dai shi yana sanki,amma uwarsa fa,irin wannan abun ake gudu gashi tun ba'aje ko inaba ta sako masa maganar aure so suke su kashe ki"
"Haba Samiha maida wukar komai mukaddari ne niba zan sauya komai ba kidai cigaba da tayani addu'a insha Allah babu abinda zai faru dani tunda dai nasan halin Rukayyan ai komai zaizo da sauki"
Murmushi Samiha tayi kamar Rufaida na ganinta tace
"Kinga Sanin hali bashi ne mafita ba addu'ar dai itace mafita kuma zan ta yaki Insha Allah"
"Yawwa nagode kawata"
"Babu komai " yar uwa, yawwa kinsan Cousin dinsu Ahmad Nasiba ta aura kuwa,tuntuni inata so na fada miki ina mantawa"
"Ke dan Allah fa bansani ba,Nasiba bata fadamin ba"
"Wallahi,kuma muna hirar a Group naga bakya duba wane shiyasa,mamar angon yayar surikina ce Ahmad ma yazo daurin aure,saida suka dawo wajen daurin auren da muka yi waya nace masa ya ganki yace a'a baki na Abuja ba,nace masa kinzo goyon ciki a gida kika haihu kuma kina gidan bikin ranar daurin aure,yace min baisaniba aida ya nemeki kun gaisa"
Cikin farin ciki Rufaida tace
"Ah ashe dai muda Nasiba no parallel"
"Eh mana,kece ma mukayi parallel din ma"
"To ya za'ayi haka Allah ya tsara,kinga wallahi na fara jin barci fa zan kwanta"
Da haka sukayi sallama Rufaida ta aje wayar ta lula duniyar tunanin rayuwarta

Bana typing mai tsawo shiyasa wasu zasuga kamar littafin zai yi tsawo
Allah ya shiryardamu bisa tafarkin tsira amin*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
47
Not edited

*RA'UF*
Chapter 46 · 0% Book details