← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 57

Sashe 56

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Rufaida tayi zuwa wani lokaci ta soma magana
"Ummi jiya Ummansu Yaya Malik ta kira ni a waya tana min barazanar kisa tace na fita harkar danta, muddin na auri danta a karo na biyu sai taga bayana,data hada iri da karuwa wadda iyaye da 'yan uwanta suka sallamata gwara ta kashe ni itama akasheta, muddin tana raye bazata bari ta sake hada iri dake ba"
Rufaida takai karshen zancenta tana goge hawayen da suka soma tsiyayowa a idanunta tunowa da kalaman da Hajiya Jamila ta wanzu gurin fadama taajiya ga kuma kalmar sallamawar da aka kira Umminsu dashi da har yau ta kasa manta kalmar wadda a jiya ne kawai ta taba jin wannan kalmar a bakin Umminsu mai Hajiya Jamila take nufi da wannan kalmar nufinta su Gwaggo ne suka sallama Ummi tasu to yaushe abin ya faru bata tunanin abin ya dade da faruwa ta yiyu jiyan nema mai Ummintasu tayi ita kuwa
Ummi Hauwa'u ta kalli Rufaida da alamun bacin rai
Maganar Ummi Hauwa'u ta katsewa Rufaida tunanin ta
"Ke shiga harkar AbdulMalik din kike kenan shiyasa kika ki fitowa waje saboda kun kulla soyayya mahafiyarsa tanason ta rabaku,saboda ke dama wawiya ce,kin manta da abubuwan da suka rika faruwa a baya ban hanaki ki auri AbdulMalik ba dan saboda kina sansa, amma kisa ni muddin kika auri dan ta a karo na biyu ki rubuta ki aje babu ni babu ke"daga fadin hakan Ummi Hauwa'u ta mike tana kokarin fara takawa
Rufaida tayi saurin rike hannayenta tana sheshshekar kuka
" Ummi yakamata ki fahimceni,wallahi ban taba son Yaya Malik ba,shima bai taba cewa yana sona ba,,sai dai idan a zuciyarsa yabar soyayyar tawa a ransa ya kasa hakuri ya bari abokinsa ya aureni ya fadawa su Abba,amma ni abokinsa ne yace yana sona yanaso ya turo gidanmu,abu daya ne yake damu na tun jiya"
Ummi Hauwa'u ta cire hannunta daga na Rufaida ta kalli Rufaida
"Mene ne abun"
"Ummi ki fadamin maiyasa su Gwaggo suka sallama ki da 'yan uwanki,meye dalili mai kika musu maiyasa ake jifanki da kalmar da hatta masu aikata abun ba saso a kirasu da shi,karuwa nasan wannan kalmar ita ta rusa wancen auren nawa, ta kuma hanayi jin dadin wancen auren nawa,dukda wanda na aura yana sona,yanzu haka nasan hanani wani auren zata yi wannan kalmar muddin mijin auren nawa yaji ni nawa asalin mahaifiya ta karuwace"
Ummi Hauwa'u ta daka mata tsawa
"Ya ishe ni haka Rufaida,tunda har 'yar cikina ta fara yarda da abinda wasu mutanan suka yarda dashi harma suke kirana da suna karuwa,bayan basu sanni ba,hasali yawancinsu basu san ni wacece ba"
"Ummi ki gafarceni ba dan ina zargi gareki na furta hakan ba illah iyaka" kukan da ya kubcewa Rufaida yasata kokarin maida maganar da takeson fada
Ummi Hauwa'u da saida ta bari Rufaida ta gama kukanta ba tare da ta lallasheta ba sannan ta komaa ta zauna gefen gadon kusa da Rufaida ta dafa kafadar Rufaidan
"Illah kawai kinaso kisan menene dalilin da yasa na amsa suna karuwa ko,amsar ita ce sunan shi ya dace dani musamman duk wanda yayi duba ga wani abu daya wuce ya zama kamar tarihi sai dai har yau ba a fasa jifana da kalmar da take tunomin da wasu abubuwa da suka faru dani a baya ba ,amsar ki ta farko da kike son sanin dalilin anbatonta gare ni itace ni Hauwa'u Mahmud Danbatta ba karuwa bace
Rufaida tayi saurin dago da kanta
" Ummi Hauwa'u ta daga mata kai
"Kwarai ni sunana haka,Malam bashi ya haifeni ba,kaddara ce ta sa ya zamo tamkar uba gare ni,amma Ra'uf saurayinki na farko shi 'dane gare ni,haka ma mijin Samiha da ne gare ni domin su yarane ga yayyena.
Ina so a yanzu kafin kisan wani abu game da tarihina ki fahimci cewa ni ban karuwa bace ban taba karuwanci ba ba sha'awarshi ba,tun daga yarintata zuwa fara girma na har zuwa yanzu dukda sunan da aka lakaba min banji ban gani ba, kaddara da tun kafin asan da haihuwarka ita ta yi dalilin anbatonta da wannan sunan

LAVARINA YA SAMO ASALI A GARIN DANBATTA KAUYEN KUNYA DA NI DIN GURIN INNATA NA SAMI ASALIN LABARINNAWA
[10/5, 11:39 AM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
Book 2
page 4

ALAVARINA YA SAMO ASALI A GARIN DANBATTA KAUYEN KUNYA DA NI DIN GURIN INNATA NA SAMI ASALIN LABARINNAWA

Malam Mamuda mutum ne bafulatani dan asalin jihar Kano karkashin wani karamin kauye na fulani kunya dake karkashin karamar hukumar Danbatta iyayensa su uku suka haifa akwai Hadiza da Salamatu shine kadai namiji a cikinsu kuma shine babba, da yana da shekaru goma Allah ya amshi ran mahaifinsa Malam Jauro

Inna wuro da take mahaifiya gasu Mamuda, da tun rasuwar mahaifinsu ta zama uwa uba a gare su sai kuma 'yan uwanta da suke kokarin taimaka mata amma banda yan uwan mijinta dukda kasancewarsu 'yan uwanta kasancewar auren zumunci aka yi mata da mijin ta Malam Jauro da asalin sunansa Bello saidai kuma su da suka fi kusa da mahaifin nasu basa taimaka musu, Mijin Inna wuro Malam Jauro nada shekara hudu da rasuwa a lokacin Mamuda yanada shekara 16 da Hadiza a lokacin keda 13 sai Salamatu mai takwas, Allah ya amshi ran Inna wuro sosai 'ya'yan nata suka ji mutuwar mahaifiyartasu shikenan sun rasa uba yanzu sun rasa uwa bayan rasuwarta ne,'yan uwan mijinta suka kwashe 'ya'ya matan suka maidasu hannunsu,'yan uwan Inna wuro da basu so hakan ba,dan sunsan wahala zasu basu tunda suka daukesu, haka dai suka hakura,suka dauke Mamuda shi kadai zuwa gurin kanwar mahaifiyarsa shekarun inna wuro 2 da rasuwa a lokacin shekarunsa goma sha shida wani makwafcinsu da yake zuwa neman kudi Kaduna anan ya bukaci da zai koma a bashi Mamuda ya tafi dashi ya rika tayasa kasuwanci,kasancewar mutumin abokin Malam Jauro mahaifinsu Mamudan ne tundaga yarinta a lokacin ganinsa a matsayin maraya yasa shi sha'awar daukarsa haka Malam Audu ya tafi dashi wannan tafiya ita ta zamewa Mamuda silar arzikinsa

Hadiza tana isa aure ta samu mijin ta cikin Danbattan da take kai tallar fura suka hadu a nan da yake dan cikin garin Danbatta ya aureta
sai Salamatu da itace karamarsu

Mamuda da kudi suka fara zauna masa ya yanke shawarar zaiyi aure kuma ya yanke shawarar diyar Malam Audu da yayi sanadiyyar samun arzikinsa zai aura mai suna Hajara ,yana zuwa da maganar auren da yayi niyyar auren 'yar wajen Malam Audun dangin mahaifinsa suka ki yarda suka ce saidai su zaba masa mata a cikin 'yan uwansa ya aura bazai aure a dawa ba aka aura masa Hanne,ya tafi da ita Kaduna da zamansu shida Hanne daga auren nasu ya fahimci bata da mutunci ko kusa,bata ganin girmansa har suka shekara biyar da aure a lokacin tanada yara uku,Suleiman da suke cewa sule sai yasaka sunan mahaifin Mamudan Malam Jauron da sunansa Bello da ake kiran yaron da Bello sai Inna wuro da asalin sunan Inna wuron Fatima ake cewa da yarinyar Fati
Daganan ya yanke shawarar kara aure ya yanke shawarar auren Suwaiba da take 'ya ga kanwar Inna wuro mahaifiyarsa da suma yan uwan nasa basu hana saba hatta dangin Mahaifinsa don kowa yasan halin Hanne a lokacin

Suwaiba ita macace mai hakuri da kawaici aurensu da shekara daya ta haifi danta namiji yaci sunan Ubangidan Mamuda da Malam Audu da sunansa cikakke AbdulRa'uf da ake ce masa Abdu Suwaiba ta yi kiransa da suna Babban Mutum,

Gwaggo Salamatu a lokacin ciki ya bullu a jikinta hankali dangi duk ya tashi,aka tsareta da tanbayar wanda Yayi mata cikin taki fada,sai da abun yakai da bugunta ta fada Sunusi dan uwan Hanne da suke uwa daya uba daya shine yayi mata da yana jin an fara tuhumar waye yayi mata cikin ya gudu yabar garin ,koda ta fadi Sunusin ne yayi mata babu wanda ya yarda a cikin 'yan uwan nasu dukda sunsan ba ji Sunusin yake ba amma sunyi shaidar baya iskanci da yaran mutane bare ma haryayiwa Salamatun kuma ma sunusin yanzu bama ya garin,acewarsu ita dai ta rasa wanda zata yiwa kazafin ne ta yiwa Sunusi taje wajen tallar furarta amma ta ciki zata zo ta yiwa Sunusin Sharri dukda kasancewarsa dan uwanta,tuni mutanen gari da 'yan uwan Salamatun suka shiga goranta mata,da binta da bakaken maganganu da habaice habaice indai zasu ci karo da Salamatun,wannan bakin cikin yasa Salamatu barin garin su don gujewa maganar mutane akanta da 'yar da zata haifa ko da idan Allah ya nufa

Wannan labarin batan Salamatun,ya ba kanta ran zuriyarsu Mamuda ciki harda Mamudan da nai man duniya yayi wa kanwarsa bai sameta ba harya hakura,da saida bacewar salamatun aka sanarmasa dalilin batan kanwar tasa har kuka yayi jin irin kaddara da ta samu kanwarsa kuma ma Sunusi shine yayi mata wannan aikin da shi yanada yakinin Sunusi ne,amma Sunusin ma neman duniya an yimasa ba duriyarsa.

**********
Suwaiba a haka suka cigaba da haihuwa kusan a tare da Hanne da Suwaiba Suwaiba nada 'ya'ya biyar a shekarar da bata fi 10 da aurenta ba
Abdu,Hamidu,Salamatu,Adam,Karima
Hanne tana da yara shida
"Sule,Bello,Fati,Jabir,Usman,Asiya
Dukkansu kansu a hade yaran suke kasancewar Hanne ke juya gidan shine dalilin zaman yaran inuwa daya Suwaiba kuwa macace mai kawar dakai halin Hanne data sani shiyasa su zama lafiya a gidan kuma matsayin Hanne na 'yar uwarta bazata so su rika hayaniya ba
Batun dukiyar Mamuda kuwa kullum bunkasa take yi a lokacin yaje Makkah yakai matansa ma

******
Malam Basiru da matarsa Saude 'yan asalin jihar jigawane karamar hukumar Taura da zama ya kawo su garin Kaduna shida matarsa da Malam Basiru ke sana'ar dukanci a babbar kasuwar Kaduna Central Market rayuwa suke cikin rufin asiri da yaransu uku
Aliya,Amina,haladu,daganan haihuwar ta tsaya musu

Aliya da itace Babba tana da shekara sha hudu da ta kasance kyakkyawar macace,
Samari suka fara nuna aha'awar aurenta amma dukta kisu sai wani mai suna Tijjani da yake kasance dan asalin sokoto sana'ar gini ta maidosa Kaduna,anan Allah ya hadasa da Aliyar da yake a unguwarsu harda shi a masoyan Aliyar da Aliyar duk cikin manemanta shine yafi kwanta mata a rai,dandanan ya fito ganin Aliyar ta amince dashi aka yi musu auren so da kauna
Chapter 56 · 0% Book details