Sashe 52
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
RUFAIDA
AbdulMalik da shigowarsa falon kenan ya idanunsa suka sauka ga Yasir yana zaune shi ka'dai a falon sallama yayi Yasir da yake game a waya ya dago kai yana murmushi yace
"Wa'alaikumus salam,oyoyo Dady Malik"
AbdulMalik yace
"Ina Mamarka AbdulMalik yayi maganar yana kokarin zama a kujerar falon
" taje kitchen ta zubo min abinci"
"Oh kaifa ina ka baro ci ina zaka ci ne"
Yana cikin maganar Rufaida ta dawo falon da plat da abinci a ciki idonta ya sauka ana AbdulMalik AbdulMalik ya sakar mata murmushi itama murmushi tayi masa ta mikewa Yasir abinci ta nemi guri a kasan carpet ta zauna tare da cewa
"Sannu da zuwa Yaya Malik,ba dai harka dawo ba?"
"Yawwa Rufaida,Eh nadawo yau kinsan friday"
"Au nama manta,bari na kawo ma ruwa,a'a bar abinki,na biya gidan Aunty Zainab daga can ma nake nayo Zaria"
"Ok"
"Baki tanbayeni labarin,mai kama dake ba,munfa sake haduwa yau nagansu ita da Auntyn ta a unguwarsu Aunty Zainab"
Murmushi Rufaida da mamaki tace
"Dan Allah fa"
"Yace
" serious har magana mu kayi"
"Please ka bani labarin ya akai kuka hadu"
Murmushi AbdulMalik yayi yace
"Bayan na fita daga gida naje gurin aiki shine nayi kokarin biyawa gidan Aunty Zainab,kafin na shiga Layin su Aunty Zainab na ganta tsaye kofar wani gida a bakin titi shine na tsaida mota ta a kusa da gidan na fito na karasa gurinta na mata sallama,bata yi min magana ba sai dai naga alamun amsawar a labbanta ina cewa Ranki ya dade wata mota ta karaso ta shiga shine na bi bayansu a mota ta har saban kawo" jin yayi shiru yasa Rufaida cewa
"Uhmm ina jin ka"
"Ke kinga kofar gidan da motarsu ta tayi parking kuwa,ina ganin kyau da tsarin gidan nasan dole yarinyar tayi jin kamshi indai gidan ya kasance gidansu ne,ina gani aka bude musu gate din suka shiga ya rufe ni kuma ina ganin haka na fito a mota ta na kwankwasa kofar gate din maigadin ya leko yace min was nake nema nace masa budurwar da suka shigo nan gidan yanzu a mota,maigadin ya kalleni sosai yace na shigo,gurin kallon gidan na 'bige Rufaida"
Rufaida tayi dariya tace
"Yanzu akwai gidan da zai rudaka Yaya Malik,bayan kuma gidanku mai kyau ne sosai"
"Ke ana miki maganar gaba fa da gabanta akace fa,kuma kinsan komai gareka akwai wanda ya fika haka rayuwa ke tafiya
"Eh hakane To cigaba da bani labari na kagu naji koda sunanta ne"
Ya cigaba da cewa
"Maigadin ne yayi wajensu da har sun fara fitowa daga motar ita magana naga yayi wa wadda nagani din kamar ba zata zoba naga wata mata ta mata magana,sai gata ta biyo bayan maigadin,maigadin daya rigata karasowa yace min cikin girmamawa " yallabai gatanan"yana barin gurin ta karaso tayi min sallama muka gaisa"nace mata Suna na AbdulMalik da wata kanwata dama naga suna kama shine na mata magana"tace min
"Ok nagode,amma yanzu ina sauri ne wani lokacin saika hadaDariya kanwarta ka ko a waya ne nace to ai bani da number dinta"shine ta samin ta fadamin sunanta Safiyya amma fa yarinyar batajin Hausa?"
Dariya Rufaida tayi tace"sai kaita mata turanci"
"Au van dake,anjima zan hadaku a waya"
"To Allah ya kaimu lfy"
Daganan suka cigaba da firarsu zuwan Hajiya Jamila falon shiya tsaida firarsu,Rufaida ta mike taja hannun Yasir suka zasu bar gurin da ta fara ganin hararar da Hajiya Jamila ke aika mata tun kafin aje ko ina,don tunda abin da ya faru dasu da Rukayya komai ya kara sauyawa don habaici zagi bakar magana shan su take gurinta,da yanzu yau kawai ya rage mata tabar gidan zuwa gobe
AbdulMalik ya tsaida Rufaida da cewa
"Ina zaki ne,muna fira"
"Firar me kukeyi kuma,nifa AbdulMalik vangane maka ba fa"Hajiya Jamila tayi maganar rai bace tana kokarin zama
Jin haka yasa Rufaida saurin barin gurin tana ji AbdulMalik na cewa
"Kamar ya Umma vaki gane minba"
Daganan dakin Hajiya Kubra suka shiga aka bude faifan fira
Sadiya Khalil🥰
[9/26, 9:37 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
50.
Masoyan wannan littafin ina godiya gareku,Allah ya hadamu da alkhairan dake kunshe cikin wannan littafin.
RUFAIDA POV
"Wallahi ina murna yau matuka Samiha
Rufaida da take kwance kan gado da waya a hannunta take furta hakan
Wayar da take a handsfree Samiha tace
" to fa murnar me kike yi"
Tsaki Rufaida tayi
"Kiji 'yar rainin wayau kin manta gobe zan koma gida"
"Na shafa'a 'yar uwa sorry,ke dawa zaki tafi ne?"
"Ba muyi maganar da Abba Bukar ba bai shigo gida ba"
"Ok to ko Yaya Samir na masa waya ya biyo tanan daga sokoto yazo ku tafi tare"
"A'a ki barshi nafi tunanin Abba zaisa Yaya AbdulMalik ya kaini gida"
"To badamuwa Allah ya jikan Yaya Wahid yasa can ta fiye masa nan,Rufaida!na rokeki ki cire duk kan damuwar mutuwar nan a ranki duk da nasan dole ki damu tsawan lokaci amma ki tuna da cewa ubangijin da haliccesa yafi ki sanshi shiya karbi kayansa,haka dukkanmu lokaci muke jira shida ya tafi vaiyi gaggawa ba mu da muke raye amu yi jinkiri ba"
Jikinta duk yayi sanyi ta fadi
"Hakane Samiha,Allah ya sa muyi kyakkyawar cikawa"
"Amin kawata, sannan sai maganar aure don Allah idan kin samu miji kin tabbatar da nagartar halayyarsa ki auresa ki zauna gidan mijinki kiyi hakuri bana so rayuwarki ta cigaba da kasancewa kamar ta yanzu inaso ki samu cigaba ko yaya ne"fadin Samiha
" Hakane kawata nagode da nasiharki"Rufaida da hawaye ya taru idonta ta fadi haka hakika ita tasan taronsu da Samiha na da ban ne,Samiha ta dace a kirata kawa ta gari,batun yau tasan da hakan ba a'a tuntuni kafin su kai ga aure bayan sunyi saboda kaunar da take mata tasa wa 'yar cikinta sunanta ba tare da tasa na mahaifiya ko 'yan uwa gare ta ba,lallai duk inda kawa ta gari takai Samiha takai harma ta zarce,maganar da Samiha keyi ta katse tunaninta
"Godiya ni dake Rufaida ai babu ita,yinta sabo ne fa,idan baki sani ba"
Jin maganar Samiha ta karshe yasa murmushi subuce mata tare da cewa
"To shikenan kawata,ina takwarata"
Batare da taji amsar Samiha ba ta jiyo sallama a falo
"Kawata zan sake kiranki anjima" daganan ta katse wayar ta ajiyeta saman drower din gadon ta yafa mayafi ta fito falon tana amsa sallamar Umar ta gani 'dan wajen Hajiya Kubra ya rissina tar da cewa
"Yaya Barka da dare"
Murmushi tayi
"YawwaUmar"
Umar yace
"Abba ke kiranki yana bangarensa"
Tace masa
"To muji kawai"tare suka kira har bangaren Abba Bukar din sallama suka yi ya amsa musu tare da yi musu izinin su shigo a falon suka same sa zaune a kujera hankalinsa nakan wa'azin da ake a Tv zama suka yi a kasan carpet
Umar ya dago kansa ya kalli Abba bukar
"Abba ga yaya Rufaidan nan na kira ta"
Sai sannan ya dago kansa daga kallon wayar da yake yace
"Yawwa Umar"
Umar din yana jin haka ya mike ya basu guri
Ganin fitar Umar Abba bukar ya kalli Rufaida ya soma da fadin
"Rufaida duk kan mai rai mamaci ne nasan kinyi rashin miji nagari kamar AbdulWahid,sai dai hakuri,da kuma fatan Allah ya sake baki kamarshi ko wanda ya fishi,sannan jiya munyi waya da Kabir akan wani satin zai sa mota ta kawo kayanku kaf na Abujar,kuma ke nasan gobe zaki koma gida,don haka kayanki dana dakinki za'a kawo miki su,ha'de da tumunin takabarki da gadon Yasir duk AbdulMalik zai kawo muku,Abdul saiya cigaba da kularmuku da dukiyar ku tunda yayi girman da zai iya rike dukiya a hannunsa"
Rufaida kanta a kasa har sai da taji Abba ya gama maganarsa ta dago tace
"To Abba,Allah ya bar zumunci ya jikan wadanda suka rasu"
Cikin jin dadi Abba Bukar yake cewa
"Amin Rufaida,yawwa batun tafiyarki AbdulMalik yace baya jin dadi,Hassan ko Hussaini sune zasu kaiki Kanon"
"To Abba Allah ya kaimu lafiya,shi kuma Allah ya basa lafiya"
"Amin Rufaida,kije ki hada kayanki,kar dare ya cika yi"Abba Yayi maganar yana jin dadin yadda Rufaida take bata da fitina balle hayaniya,komai nata mai sanyi ne,shiyasa shima bai ki wa AbdulWahid auren Rufaida ba da ya nuna yana santa saboda yasan ita Alkhairi ce ga rayuwar 'dan nasa,maganar ta ta katse tunaninsa
" to Abba sai da safe"
"To to mu kwana lafiya"
Daganan ta fice tana tura masa kofar karo suka so yi da AbdulMalik da yake kokarin shiga falon shi kuma yayi saurin ja da baya yana dadin
"Subhanallah"
Daganan ya fara kokarin mur'da hannun kofar falon
Rufaida ta kallesa ganin abinda yake kokarin yi tayi saurin fadin
"Yaya Barka da dare"
Ya 'dan juyo da kallonsa gare ta
"Yawwa Rufaida ya Yasir,ya bangansa ba"
Murmushi tayi tace
"Tara tayi ai ya kwanta"
Ok kawai ya iya furtawa
Ganin yanayinsa kamar bayasan firar tayi kokarin barin gurin
AbdulMalik ya bita da kallo a ransa yana ayyana,anya zai iya barwa Zahraddin abinda yake so tuntuni tausayi da soyayarta suka wanzu a ruhinsa wato Rufaida,wata zuciya tana ayyana masa taya ma zai iya bari abokinsa ya auri Rufaida da shine tunanin Zahraddin da ya kirasa dazu ya fada masa, munufarsa akan Rufaida, saidai yana tunanin Zahraddin abokin sane tun yarinta sunyi rayuwa ta tausayawa juna hawayen idonsa da suka fara ta ruwa idanunsa ya goge yana ayyana yanzu indai ya amince shikenan,ya rasa farin cikinsa,fasa shiga gurin Abba Bukar din yayi ya nufi bangarensu
Washe gari
Rufaida ta karaso falon cikin shigar leshi ta riga da siket da hijabinta milk colour dogo har kasa da ya haska farar fatarta kyawunta na Hausa fulani ya bayyana sosai hannunta cikin na Yasir da shima ta shirya sa cikin shadda ruwan kasa mai haske sosai
"Badai har kun fito sai tafiya Ba,wannan sammako haka"
Hajiya Kubra da murmushi fuskarta take fadin haka
Hajiya Jamila ta saki dariya ta saka baki
"Ke ko Kubra tayi sammako mana tanaso taje ta tarar da karuwar uwarta"