Sashe 53
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin maganar Hajiya Jamilar ta dago ta kalleta ta goge hawayenta tanaji yau bazata hakura a cigaba da fadar aibu akan mahaifiyartaba ai uwa uwace ko ya take kuwa, ta dan yi murmushi mai ciwo ta soma fadin
"Umma kenan kalmar karuwanci da kike fada Ummin tayi ,mantawa kikayi kece uwar dakinta a can wajen karuwancin"
"Hajiya Jamila jin karashen zancen Rufaida yasa ta mike a fusace tana fadin
" Allah ya rabani da karuwanci,ni zaki hada da wannan kalmar shaidaniyar yarinya"tana fadin haka tayo kan Rufaidan zata doketa da sauri Hajiya Kubra tasha gabanta
"Laifin mai ta yi miki zaki doketa,kina tunanin ko jikar kice zaki riqa fadar wani abu kan mahaifiyarta tun bata tanka wa ai kinsan wata rana dole ta mayar miki da martani,bare ma yarinyar nan ta kawar dakai fiye da tunani"fadin Hajiya Kubra
" ki matsa min a hanya na ko muyi fatarta ni da ke,yar da na haifa zata hadani da kalmar karuwa,karuwa fa!,bama karuwa ba nufinta nice uwar karuwan" fadin Hajiya Jamila ta karasa zancen tana nuna kanta
Dariya Aunty Amarya tayi da shewar ta kuma ja tsaki
"Dan Allah matsa ki bata gurin Maman Umar,naga karyar haukan matar nan,tazo ta tabata idan ban 'balla banza na zubar ba,banda ke din banza ce ai maganar Rufaida ba karya a cikinta,indai bake ce uwar karuwan ba ina kika san Ummi Hauwa'un tayi karuwancin,indai ba an taba yawata duniyar ba kema"fadin ta tana sake cigaba da wata dariyar
Kan Aunty Amaryar Hajiya Jamila tayo a fusa ce tana fadin
" Amina ni kika samu damar fadawa magana"daganan ta soma kokarin rike hannunta zasuyi danbe
Shekeke Aunty Amarya tayi tana kallonta ta janye hannunta daga na Hajiya Jamilar
"Kinga malama karki sake hannunki ya taba nawa ma bare harkiyi kokawa dani,don mijinki da kika raina shine dai-dai dake bani Amina ba,don ni ko maganar banza kika fadamin sai kinyi dana sani wallahi,ke kanki kin san niba ajinji bace,dana san haka kike karya da banyi gigin hada gida da keba wallahi,fitinanniya duk halarcin da mijinki ya yi miki ya debo 'yan uwanki ya rike bai ishe ki ki zauna dashi lafiya ba sai kin masa kinwa 'yan uwansa"
Hajiya Jamila jikinta duk yayi lakwas don tasan duk da Aunty Amarya ba girma gareta ba sarai zata iya doketa tayar da ita abanza don ita dama ba karfin gare ta ba,kuma ko magana sai Aunty Amarya ta caba mata wadda bata yi tunani ba,don ita dama wanda ta raina take wa wulakancinta
Su Hajiya Kubra da suke tsaye circirko Aunty Amarya da take jiran taji Hajiya Jamila ta fada mata wata maganar ganinta tayi shiru kamar gunki, yasa su kokarin fita raka Rufaida harabar gidanku inda zata shiga mota da Rufaida yanzu take jin zuciyarta wasai kamar ta cire dutse a zuciyarta ta,don koba komai yau ta maida martani inda ya dace ace ta dade da mayarwa.
AbdulMalik da yake tsaye bayan kujerun falon da tunda aka fara maganganun yake tsaye yana jinsu shi wata maganar ma dariya ta rika basa ya gimtse dariyarsa ya karaso inda suka bar Hajiya Jamila tsaye kamar gunki ya dafa ta yana fadin
"Kiyi hakuri Umma ki zauna"
Hannunsa ta cire daga kafadarta
"Ka gama dariyarka kenan?"
Ya dan zaro ido da mamaki kan fuskarsa shi baisan Ummantasu tasan yana gurin ba
"Umma dariyar me?"
"Ta gidanku ko nace ta ubanka,da ya gama bata ni gurin matansa,nufinka banga sanda kazo nan bane Malik kenan kanaji ana cin mutunci na,maimakon kazo ka shigarmin saika tsaya yimin dariya,saboda baka dauke ni uwaba ko?"
Kai girgiza yana cewa
"Ko 'daya Umma ai ita uwa uwace,amma dai ni kinsan bana goyon bayan rashin gaskiya tunda ke kika jasu tunda basu saki a maganarsu ba kika shiga,shigarma da kika yi ba Alkhairi kika fada a maganar ki ba,sannan Aunty Amarya ba karya ta fadaba abinda kike wa Abba ta fada kuma a gaban kowa ma yi masa kike,kuma ba ruwan Abba bashi ke fadamusu ba gani suke kinayi"
"To Ubana tsare ni kamin fada,wallahi Malik bansan wanne irin da na haifa ba da baya kishi na....." Jin ta fara sababi yasa shi saurin barin falon ya fice harabar gidan da ya tarar Rufaida har ta shige gidan baya Yasir a gaba ,Hassan da da Hussain ne zai kaita suka tafi wata unguwa da Abba Bukar,yana wajen Boot din motar yana kokarin rufewa alamun ya gama zuba kayan Rufaida dana Yasir sai tafiya
AbdulMalik ya riko hannun Hassan da yake kokarin bude kofar mota ya masa ra'da Hassan ya dago fuskarsa ya kalli Rufaida yana fadin
"Kace ta kusa zama Auntynmu" AbdulMalik ya maka masa a baya duka yace"kaifa matsalarka ba'a sirri dakai
Su Hajiya Kubra suka yi dariya
sirrin mai za'ayi dani kuwa bayan abin alkhairi ne ya samu,Aunty kinsan mene ya faru"fadin Hassan
Aunty Amarya ta girgiza kai
Hassan yace na hannun damar Yaya Malik ne Yaya Zahraddeen,yaga Rufaida yace ya 'kyasa idan ba ita ba sai rijiya"
Gaba 'daya suka sa dariya banda Hajiya Kubra da Hussain ya sameta da maganar shifa yanason ya auri Rufaida kuma ita ma ta basa goyon vayan hakan saboda yarinyar akwai nutsuwa da sanin yakamata ga rashin hayaniya kuma uwa uba 'yar uwarsa suce ,to kuma yanzu ga wannan ta fara kunno kai duk da tasan baza'aki na gida aba na dawa ba inba daurowa tayi ba,zata fada Hussain yaje mata da soyayyarsa gare ta ko zai dace,ko a ina ma Zahraddin din yaga Rufaida oho Hajiya Kubra tayi wannan tunanin
Rufaida da take jin abunda suke fadi ta danyi murmushi kasan ranta tana tuna kamannin Zahraddin kyakkyawane ba laifi,gashi da son barkwanci,sai dai bataji a yanzu zata iya sa wani a zuciyarta guri kusa saboda tayi babban rashi da haryau bata gama jinyar zuciyarta ba ta rasa miji nagari a rayuwarta,saidai tunowa da Nasihar da Samiha ta mata jiya yasa ta kauda wannan tunanin sai dai zatayi addu'ar Allah ya yi mata zabin Alkhairi a rayuwarta jin Hassan ya tada motar da bata ji shigowarsa ba yasa ta dawowa daga tunanin da ta tafi da addu'a su Hajiya Kubra,Aunty Amarya, AbdulMalik suka bisu dashi suna daga musu hannu har ya fara tafiya ya karasa wajen bakin gate maigadi ya bude musu gate din motarsu ta fita ya bisu da addu'a
[9/29, 7:00 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
51
RUFAIDA POV
Jin Hassan ya taka burki yasa Rufaida 'dago kai ta kalli gefen titin da takai kallonta gasu Hassan da ya faka motarsa da Yasir keta barcinsa tunda sukaf fara tafiya shi dama Yasir baida wuyar barci ta soma da fadin
"Yaya Hassan ya naga ka tsaida motar,a gefen titi lafiya kuwa?"
"Eh inaji dai kamar tayar mu ce tayi faci,amma bari na fita nagani Ku zauna basai kunfito ba"yana gama fadin haka bude murfin motar ya fito
Rufaida na cewa
" to Allah ya tabbatar da lafiya,ya kuma kara tsare mu"
"Amin ya rabb"
Yana fadin haka ya shiga duba tayoyin motar tasa bai jima yana dubawa ba ya leko da fuskarsa cikin motar daga gefen titin yana fadin
"Kamar ko na duba dazu,tayar ce tayi faci ko"
"Subhanallah,To yanzu ya za'ayi gashi mun baro zariya"
"Zan kira wani mai yi mana gyaran mota sai ya hawo machine ya zo Inda muke da kayan gyaran,dama ban tsaya duba motar ba muka taho"yana fadin haka ya zura hannunsa a aljihu ya fito da wayarsa ya shiga dannawa ya lalubi lambar mai gyaran ya kira sa yayi masa bayani ya sake shigo da kansa cikin motar yace
"Ya ce min yana zuwa"
"To Allah yasa yazo da wuri"
fadin ta
"Amin"
Sunyi kamar Rabin awa agurin suna jiran mai gyaran amma babu ko alamunsa
Ta dan leqo daga cikin motar da Hassan yake waje har lokacin a gurin tana cewa
"Yaya Hassan anya zaizo kuwa?"
Nima abinda nake tunani kenan,bari na sake tabasa"yana fadin haka ya dauko wayarsa ya soma danna lambarsa
"A'a Yaya kawai dai a kira wani Yaya Hassan,yaci ace tun dazu fa yazo"
Dariya yayi ka'dan da cewa
"Kin ka gara dai,kije kika su Ummi ko?"
Murmushi tayi
"A'a kawai dai"
jin Horn din da ake abayansu yasa Hassan maida abinda yayi niyyar fada cikin bakinsa ya juyo ya kalli motar Prado baka"
Ganin ana kokarin fitowa daga motar yasa Hassan fasa karasawar da yayi,Dady Jabir ne ya fito daga motar a mazaunin driver da fara'arsa ya karaso Inda Hassan yake tsaye yayi masa sallama ya mika masa hannu,
Hassan da murmushinsa da baikai zuci ba ya amsa sallamar Dady Jabir ya mika.masa hannu sukayi musabiha ,daganan Hassan ya dan rissina cikin nuna girmamawa Hassan ya gaida Jabir din ganinsa matsayin babban mutum,kuma ya girmemasa Dady Jabir,don zai iya sa'an Abba Bukar duk a cikin tunanin Hassan
"Yadai 'dan samari maike faruwa, yanzu 'diyata ta hangoku ta cikin glass din mota" fadin Dady Jabir
Hassan da maganar ta katse tunaninsa ya dan sake sakin fuska jin maganar da Dady Jabirun yayi yace
"Eh dama Yallabai motar muce tayi,faci amma mun kira mai gyaran yace mana yana kan hanya,to mun jima muna jiranshi har yau bai kara soba"
"To Allah ya kiyaye gaba,amma wanne gari kuke shirin zuwa?"
"Eh kano zan kai kanwata ne"
"To Allah ya kara kiyayewa"
"Amin"
Har Dady Jabir ya juya baya ya soma tafiya ya 'dan dawo da baya yace
"Naji kamar kacemin kanwarka zaka kai"
"Eh yalla'bai"
"To kenan kai rako zaka yi kenan ma?"
"Eh to yalla'bai zan iya cewa hakane"
"To indai kana ganin babu damuwa,zamu tafi tare,in yaso kai kaje daukarta idan zata dawo"
Rufaida da take jiyo maganganunsu Dady Jabir da Hassan da mutumin da yayi mata kwarjini, wanda daga kallo guda idan kayi masa zaka tabbatar kudi da hutu sun ratsashi,haka ma a siffar sa zakasan bafulatani amma jin yace bata san shi ba yace su shiga motarsa ya kaisu Kano yasa jikinta yin sanyi,don yanzu dan adam ba abin yarda ba ne dukda akwai na garih amma sunyi karamci ta tsaya jin mai Yaya Hassan din zaice masa sai kuma taji Hassan din fadin
"Yalla'bai ayi haka kuwa,karmu dora ma nauyi mai garan ya kusa zuwa ai"