← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 57

Sashe 33

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

35
*****
Kukan da take ta tsayar ta maida kallonta ga wayarta ganin number din Samiha yasata saurin daukar wayar da sallamarta saida suka gaisa Samiha tayi gyaran muryar ta soma magana
"Rufaida banji dadin abinda su Abba suka ma danginsu Ahmad ba sunsan tun farko yaya Ahad sukeso su aura suka boye masa,bakiji haushin da Ahmad yaji ba dan sai alokacin da aka hana Ra'uf aurenki ya fahimci bamuda alaka dake"
Rufaida jin Samiha tayi shiru yasata kokarin cewa
"Ni kaina Samiha banso abinda aka ma danginsu Ra'uf ba ga uwa uba inasan Ra'uf amma iyayena sun rusamin burina,batare da nasan dalili ba, sun fadawa Ummi maganganu mara sa dadi sai kace itadin Ba jininsu bace akan kawai suna zargin da hadin bakintama Ra'uf yazo neman aurena,gashi suna kokarin tilastani auren Yaya Ahad dakema kina sane da irin kiyayyar da Umma Jamila ke gwada ma...kukan da take makalewa ne ya kufce mata,Samiha da takejin kukan kawarta ta har saman kanta ta soma rarrashinta
" Haba Rufaida kukan meye haka nima Iran kinayi wallahi nima yi zanyi ke kawatace danike jinki a jinin jikina wallahi son danake miki ko Yaya Sauda bana masa kwatankwancinsa yi hakuri daina kukan kinji kawata dan Allah"
Kukan Rufaida ta tsayar Kafin ta cigaba da magana
"Samiha busu kyautaminba nida Ummi sun rabani da mutumin Dana fara so a duniya akarshe sun yiwa Ummi kazafi sun muzanta ta muna kallo bayadda muka iya nima suna kokarin hadani da wani tashin hankali Abba yanaji bai hana Abba Bukar yanke wannan shawararba gaskiya bazan iya....Samiha bata bari Rufaida takarasa maganar da takeson yiba tayi saurin dakatar da ita da cewa"
Haba Rufaida karki furta wata mummunar kalma ga iyayenki dukda nasan busu kyautamiki ba kiyi kokari ki manta komai ki tuno da abubuwan da suka miki tunda ga haihuwarki har zuwa yau sine suka maidake cikakkiyar mutun suka baki tarbiya da har Ra'uf ya ganta tattare dake yaso aureki karki manta hakan ki fadi mumnunan kalma garesu ,nasan abinda suka yiwa Ummin busu kyautaba amma ya zakiyi ita ta suce,saidai fadan ne da sukai mata ni mamaki ma ya bani itada bata sansu ba amma sai a huce akanta amma komai sukayi mata tasu ce dai,sannan batun auren yaya Ahad ki fahimci bad Umma Jamila zaki zauna ba sai kinje inda take ko wani Abu yakawota gunki zata fadamiki wata magana tunda yaya Ahad nasanki ai shikenan.
Rufaida da.maganganun Samiha suka shigeta
"Gaskiya nagode kawa tagari"
Babu komai kinfi ganan Rufaida ke kamar jinin jikina ce"Ahmad da ya samu Samiha a falo yaji tana cewa Rufaida ya fahimci da ita suke wayar ya umarci ta bata wayar su gaisa danshi bayida haufi akan Rufaida yasan bata da laifi
Bayan sun gaisa da Rufaida da kamar da zata cewa Samiha karta basa wayar sai kuma taga bata kyautaba tunda shi da akamusu laifi bai kullaceta ba sai ita,jin muryar Ahmad yasata dawowa daga tunaninta
"Amaryar Ahad,ashe dama yayanki zaki aura shine aka mana kora da hali ko?"
Yadda yayi maganar yasa Rufaida ta fahimci bai dauki zafi ba shi,yasa itama cikin wasa ta mayar masa da amsa
"Kai Yaya Ahmad ba laifinmu bane laifin 'Danbata Family ne"
Zaro ido yayi baiyi mamakin jin sunan a bakinta ba saboda Samiha
"To ke kuma ya sunan naku Family da sainace sune masu laifin"
"Tafida, yaji ta fada da tana fadar hakan ta yanke wayar ta daga Koran Ummi da take mata
" to sune masu laifin"Ahmad ya fadi hakan,jin bata amsa ba ya sashi duba wayar ganin takatse kiran Samiha ya mikawa wayar
"Ungo kawarki ta katse wayar ta soma fahimtar munfisu gaskiya" ya karasa maganar yana murmushi ya shige ciki.
Suna gama wayar da Ummi da kannenta da suke fadar yadda sukayi kewarta sakar zuci tafara ta yadda komai ya sauya mata lokaci kankani tunanin Ra'uf shine dankare a zuciyarta sai dai kuma an raba wannan soyayyar data ginu a tafarkin gaskiya tanason ta kirasa taji muryarsa sai dai idan ta kirasa mai zata ce masa ba wani zata aura idan ta kirasa ya daurar kanta zatayi
Da wannan tunanin barci ya dauketa
***********
Kajan yo ma zuriyarmu wulakancin da babu wani bil adama dan cikin zuriyarmu daya taba janyomana face kai Hajiya Hanne ce take fadar maganar cikin bacin rai wacce take zaune a durowar gefen gado wanda wanda take maganar danshi ke zaune kan gado yana kokawar sa agogon hannunsa

Fadan ta cigaba dayi batare da tsayawaba nidai tun lokacin da zuriyata ta hadu da ta hafsatu babu ranar da farin ciki ya wanzarwa zuciya ta iyayenku sun shanyemin 'ya'ya na guda biyu dalili mai karfi da yasa shima dan uwan naka yaje ya auri wadda babu sanayya ko guda daya da na sani game da ita shiyasa kai dinma kaje neman auren irin su saiga irin cin fuskar da kai da karen kanka kajanyoma a halin naka ca nake kai dakanka kafi kowa sanin irin soyayyar da karima ke kokarin gwadama amma kaidin da karan kanka kafurta bakasan 'yar uwar jininka wadda kai kanka kasan tafi yarinya irin mayu aini dai sam banyi sa ar surikai ba daga uwar taka har hannatu yau kimanin shekaru akallah 4 rabon ubanka da zuwa inda nike kuma baidama niyyar zuwa itako uwar taka rabonta da zuwa kaduna tun barinku kasar nan amma inajin labarin bata shekara biyu bata zo taga uwarta ba saboda ni bata daukeni uwa ba duk irin halaccin dana yimusu daga ita har hafsatun wadda a kaf zuriyarmu babu wadda nayima abinda nayima hafsatu a matsayinta na yar uwata mafi kusanci a gareni amma yau ga irin abinda kajanyo ma kanka ka janyo ma zuriyar ka haba *Abdur ra'uf* .jin ta tsagaita maganar tatane yasa shi mikewa yana fadin haba Hajiya duk mai ne ne anfanin fadin haka inji AbdulRra'uf din da yamike yana kokarin daukar wayarsa ya cigaba dacewa tun a lokacin da abun yafaru yakamata aman ta da maganar.hajiyar ce ta kara dacewa naki mantawa da maganar idan kai bakasan ciwan kan zuriyar ka ba aini nasani nasan tozarcin da akamana nidai hada ji'bi da zuriyar hansatu bai kareni da komai ba wato ma kawai nabar maganar . saurin ficewa daga dakin yayi danshi dayasan kalaman na hajiyar yana da cikin mizanin muni nada ga gareshi da baiyi jimirin zama a 'dakin nashiba shidai sam kalaman hajiyar sun masa matukar munin da bazai sake son jinsu ba wadda shidai sam hajiyar bata kasance macen da zai duba amatsayin uwa ga mahaifinsa ba domin da hakan yakasance yasan tabbas bazata zamanto
Mai sake kokarin jefa zuciyarsa tasa bisa ga kangin damuwa ba duba da irin kiyayyar da aka nuna masa a bangaren gidansu Rufaida wanda shi yasan ko da bai san dalili ba Ahalin nasane silar rugujewar farin cikin nasa a karo nafarko yarasa yarasa masoyiyarsa mai matukar son farin cikinsa wadda tarbiyyarta ce silar son cigaba da zama da ita na tsawon har abada yana cikin tunanin ne yakarasa bude kofar wani daki yashiga da sallamarsa. Gefen sallayar da yasamu dattijuwar matar fara yazauna yana fadin ammi sannu tasbahar hannunta ta ajiye akasa tana mai amsa masa sallamartasa dafadin yawwa *RA'UF* kafin tadora dacewa sarkin a zama har naga kashirya tun a subar fari tafada tana mai kau da kanta daga kallonsa *RA'UF* 'din ne ya kalleta yana fadin tuba nake *Ammi* tun 'dazu nagama shirya komai wannan rigammiyar tsohuwar ce ta tsaidani nagama shirina ta tsaidani *Ammi* ce ta dubesa tace kaidai kasani yawwa *Ammi Ra'uf* ya anbata dama har yau Hajiya na nan da fadan ta mara karewa idan ta fara Dariya abin yabawa *Ammi* tace sai hakuri zama da hajiya. Ina fata dai ka kammala shirya kayan naka eh ammi danladi ma har yasa su a mota.

Ko a jikin motar da hajiya tafito yi musu rakiya ita da sauran mutanan gidan fadan ta hau yi tana fadin idan kakoma kasar fararen motar ka mutu babu aure kannen ka kuma baza su fasa aure ba kamar yadda dai Ahmad yayi kafin tajuya ga Ammi tana fadin ke kuma banaso kodai da rana daya kisake zuwa daga ke har dan nawa dakika shanyeshi kubari sai mutuwata kuzo.ita dai Ammin ba tace ko mai ba sai kanta dake kallon kasa Baffa Alhaji da sai yanzu yasa baki da take gefen hajiyar ne yace haba hannatu kedai sam bakya iya hakuri ne da harkar duniya komai bazaki mikasa ga Allah ba sai kin nemi wani abu da zaki fada akanshi maine laifin yaran nan jabiru bata tsaya jin karshen maganar ba ta bar gurin Mama Suwaiba tace to babban mutum Allah yaki yaye hanya amin umma Ra'uf ya fada yana murmushi dukda yadda zuciyarsa bata masa dadi amma yanajin dadin sunan nan da Mama ke kiransa dashi anan motar ta tasu ta tashi duk zuciyoyi babu wani dadi ba daga shiba har ga zuciyar Ammi da take mahaifiyarsa suna barin gidan Malika suka nufa daganan suka nufa dako zama busu yiba Safiyya ta fito da Jakarta da take ja Aunty Malika da yaranta suka fito musu rakiya harabar gidansu.
***
Wayarsa yake dannawa da yake kwance a falon gidan Bello dake Abuja sai dai wayar kawai take dannawa amma tunaninsa naga Rufaida fuskar Rufaida ita yake gani a idanunsa,shi kansa yasan bakaramin so yakewa Rufaida ba
Bai saurari lemukan da Bello ya shigo musu da suba ya mike yabar musu falon ya shige ya cigaba da tunaninsa yanasan kiran Rufaida saidai idan ya tuno wayarsu da Ahmad a dazu da yake shaidamasa aure za'a yiwa Rufaida zata auri cousin dinta saiyaga babu anfanin kiran idan yakirama bazai anfanesa ba kiran dalilin da yasa ya hakura yayi kwanciyarsa da addu'o'in kwanciya barci a bakinsa.
[8/24, 7:48 PM] Sadiya Ibrahim Khaleel: *JININMU 'DAYA*

By Sadiya Khalil😘

*Afuwan masoyan littafin jininmu 'daya kuyi hakuri bisa tsaikonsa ya Allah ka bamu ikon rubuta abinda zai anfanemu duniya da lahira*

*Note ABDULAHAD shine ya koma ABDULWAHID*
36
Chapter 33 · 0% Book details