Sashe 6
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da sallama ya isa falon gidan da yaketa kamshi wandaa Key da wayoyinsa suke a hannu sai sakon Ammi da yake hannun nasa"Safiyya da take falon da Pakistan riga da wando a jikinta da dankwalin kayan akanta ta amsa masa sallamar da cewa "a'a Yaya Ra'uf sannu da zuwa kaga yadda kayi kyau kuwa kamar rana bata dokeka ba" Hararar ta yayi yace"banasan raini fa naje aikin na dawo ki fadi haka"tace Allah Yaya dagaske make"yace "to naji ina Ammi" tace masa" tana ciki"da haka ya aje sakon da wayoyinsa anan yace yana zuwa zai watso ruwa Safiyya tana ganin shigewarsa ta 'dauki wayarsa da tasan ba pattern tsaron waya ta fara kiran kawayenta da suka jima busu gaisa ba saboda hutun dasu keyi sai da taji alamun saukowarsa daga saman bene ta ajemasa wayar ta cigaba da kallon da takeyi dashi da Ammi suka sauko inda Ra'uf ya kalli Safiyya ya harareta yace" da ganin fuskarkin kowa yasan kinyi laifi"Ammi ta kallesa tace" kai Ra'uf kadaiji tsoron Allah mai kuma Safiyyar tayi"labari yake bawa Ammin har suka karasa gurin cin abinci suka inda suka fara cin abinci Ra'uf suna cikin cin abincin yace "Ammi yanaga Dady bai dawo ba" Ammi tace "yana hanya nafi tunani" Ra'uf yace "bari dai na kirasa naji ke Safiyya daukon wayata na kira Dady"Safiyyance ta mike daga cin abincin da take ta dauko wayar ta mikawa Ra'uf da hannu biyu da tuni tafara tsorata dan tasan ta cinyewa Ra'uf katinsa
Ran Ra'uf inyayi dubu ya 'baci ganin ya kira Dady sun shaidamasa ba kudi shiko yasan da kudi ya aje wayarsa Safiyya ya fara tunanin tacinyemasa kudin duben Safiyya yayi ya ha'da rai yace" wa kika kiramin da waya"cikin tsoro Safiyya tace Yaya kaya ha'kuri 'kawayena ne"yasake cewa "ban hanaki ta'ba min waya ba ke kwata kwata bakyajin magana" cikin tsoron hukuncin Yayannata tace" kaya hakuri bazan kara ba"Ammi tasa baki tace to bata baka hakuri ba ai saika hakura kasa wasu"Ra'uf yace" amma Ammi kina gani fa ta mikon wayar na fara kira maimakon tacemin babu kudi amma taki fa'damin saboda ta rainani"Ammi tace"ai tunda ka kiyin aure 'yar Safiyya ma sai tazo ta rainaka bama Safiyyanba"Safiyya da 'kiris ya rage tayi dariya ganin Ra'uf ya tashi daga gurin yasata yin shiru tana jin bata kyauta ba ganin itace taja abinda ransa ya'baci Safiyya tace cikin Sauri"Yaya kaya hakuri bazan 'karaba" ganin zai karasa matakalar bene murmushi yayi batare daya juyo ba yahaye been ya karasa 'dakinsa kawai ya zauna bisa 'daga cikin kujerun dake falonsa ya jingina kansa da kujerar yana tunanin mikin da aka dasama zuciyarsa babu kwakkwaran hujjar dasawar kuma har yanzu har abada kuma bazai iya mantawa da bigiren ba har wayau kuma bazai ga laifin bigirenba koda duk duniya kowa zai lankaya laifi gashi bigiren ba an shiga rayuwar daya dade yana mafarkin samu ba tareda sanin hujjaba kawai anyi anfani dason zuciya gurin cusguna masa tabbas akwai zalinci mai yawa a wannan rayuwar da ake yi to ta ina zaiyi wata rayuwar da yasan zalintar duk wadda zata zauna dashi zaiyi,babu aure a yanzu haka a tsarinsa koda zaiyi bayanzuba kasancewar yasan tun asalinsa shi bamai sa'a bane da wannan tunanin barci ya daukesa koda dady ya tanbayi Ra'uf Ammi tace da kanwarsa ne ita tamasa laifi ta bashi labari fa'da sosai Dady yama Safiyya tace idan ya fito anjima zata sake basa hakuri da haka hirarsu ta kasance kasan zuciyar Ammi yana tunano wani lamari daya maishe da ',dan nata haka mikin da ya harbi zuciyarsa abunda yafi kama da nuna iko da har yau takasa fahimtar wannan dalilin ikon da aka nuna ga gudan jininta da akai anfani dashi gurin zalintar zuciyarshi da danamasa mikin da har yayi tsamarin da batayi tunanin zaikai haka a zuciyar 'dan cikin nataba.*JININMU 'DAYA*
BY Sadiya Khali
6
Bugun 'dakinsa da yaji anayi shine yasa shi farkawa da anbaton Allah a bakinsa,duk jikinsa yayi masa nauyi dan koda can a baya da rayuwar bata kai haka ba jindadi ba shi baisa ba da kwanciya a kujera ba,koda a yanzu tunani yasoma tu'kewa a zuciyarsa har yake neman shafar jin da'di rayuwartasa baisa ya saba makamancin rayuwa Irin wannan ba,jin muryar Ammi tana cewa"wai bazaka bude min kofar ba" ya danyi mi'ka ya mi'ke yana cewa "Ammi a bude fa take" yakarasa jikin kofar ya bu'de matsawa yayi ta karasa shiga ciki ya maida kofar ya rufe kallon Ra'uf Ammi take har tanemi guri saman kujera ta zauna shima kujerar da yatashi ya koma ya zauna
Nisawa Ammi tayi kafin tace"Ra'uf yanzu abinda ka za'barwa kanka kana tunanin ya yima kullum kai kenan ka rufe kofa ka zauna kayita tunani bayan komai na duniya hakuri ake dashi duk yadda al'amura suka tu'ke da wanzuwa", Murmushi kawai yayi kafin yacewa mahaifiyartasa"Ammi ni tuni na da'de da barwa Allah komai dukda har yau ban fidda rai ba ga samun waccen sa'ar da nake tunanin ada na rasa ta sai dai yanzu ina mafarkin samun abinda na rasa kona samu Wanda ya fishi" Kai kawai Ammi ta girgiza tana gwada maganganun Ra'uf ama'auni sai dai dukda ta gano abinda yake nufi baisa ta tada maganar ba dan ita ba maison tayadda abinda ya rigada ya wuce bane tun fil azal,Sauya maganar tayi da cewa,"To yanzu maganar aure na lura sai dai an zaboma macen da zaka aura tunda gashi nan shekarunkafa tafiya suke"dan jim yayi kafin ya ce "Ammi ni yanzu banida wani za'bi kiyi duk yadda kikaga ya dace zan amince",Murmushi tayi tace" to Allah yasa karka kara bani kunya,Kamar wancen lokacin Murmushi yayi mai sauti kafin yace"A'a Ammi ai wancen karanma inada dalili mai karfin gaske"ta 'dan murmusa tace"ni banga laifin Intisar ba kai dai kawai kaki ta sai gashi abokin ka ya aureta"yace yawwa Ammi kin gani ko,Inteesar dama tuntuni Shureim yake fadamin son da yake mata kinga kuwa ni din baikamata na cusa kaina ba gwara dai dana barwa aboki na ya muradinsa ya fa'da yana tauna la'b'bansa na 'kasa yana sake tuno wancen mikin da baya kwana bai tuna shi ba abinda yafi kama da al'ajabi da tarin tanbayoyin da bazai gushe ba yana tanbayar kansa ,Ammi tace "to shikenan Allah ya kawo mace tagari" sake maida dubanta tayi ga Ra'uf ta tattara dukkan natsuwarta dukkan nutsuwarta gareshi da alamu maganar mai muhimmanci ce tace "amma Ra'uf mai zai hana ka amince da maganar Dadynku ka auri Safiyya",shiru yayi kana yace" Ammi bawai na'ki bane amma banaso yarinyar nan ta shiga wannan zuriya mai 'dunbin son zuciya da nuna fifiko zatasha wahala duba da ita 'din wacece baikamata nina zama silar cutar da wannan baiwar Allah 'din ba"Shiru Ammi tayi tana sake tunanin maganar Ra'uf datasan gaskiya ce itakanta Ammi ta fiso Safiyya tayi aure a inda zata huta da bazata fahimci ita 'din wacece ba koda har abada bazatasan wacece itanba, Da haka Ammi ta mi'ke da cewa to zan bincikoma tana duben agogon falon ta cigaba da cewa" Safiyya fa ta gama shirin tafiya gidan Shureim kai take jira"ya 'dan saki fuska yace "Ammi na manta gwara da kika tunamin danma banason nakasance mai sa'ba alqawari amma da bazanje ba bare naje da Safiyyan"Ammi tace bamai shiga fa'danku kai da Safiyya idan anshigama aji kunya" Murmushi yayi yace ai kuna gaf da daina jin kunyar "Ammi ta fice tana cewa"kanku dai akeji dai"