← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 57

Sashe 45

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

****
Marhabin da manyan baki wallahi sam ban tsammaci zuwanku ba"Rufaida ta furta hakan tana kokarin matsawa daga kofar falon da ta bude
Luba da ta shigo da Yusuf data riqewa hannu tace
"Ai dama haka zaki ce,uwar cika alkawari"
Ta karasa maganar tana hararar Rufaida
Rufaida tace
"Ayi min afuwa matar likita bokan turai kinsan Yasir baiji dadi ba yau kwana 2,yanzu dai ku zauna na kawo muku ruwa"
Luba ta zauna kujera tana cewa
"Var ruwan nan daga gida muke yanzu Abban Yusuf ya saukemu ya wuce asibiti"
Rufaida da take kokarin zama kusa da kujerar dasu Luba kekai tace
"Kai Yaya Kabir yana kokari, su likitoci kullum aiki kamar agogo ace har weekend ma"
Luba tace
"Hmm kedai bari kawai,yanzu aka kirasa waya patient garesu kuma ana bukatar yaje asibitin ya dubashi cikin gaggawa shine muka fito tare"
Rufaida tace
"OK Allah yabada lafiya"daganan ta maida dubenta ga Yusuf dake ta zaro ido tace
"Yusuf zo mugaisa mana ko kula ni yau bazaka yi ba"
Kafada Yusuf din ya make ya kwanta jikin Ummansa
Rufaida tace
"Au bazaka zo ba ko?"
Luba tayi dariya tace
"ai kema kinsan bazai zo ba tunda yaga baiga Yasir ba,yana inane ko jikin ne yayi zafi"
Rufaida tace
"Ai na fahimta,yanzu suka fita shida Abbansa,kinsan mara lafiya da kwalama ice cream yakeson sha"
Luba tace
"A lallai kuwa,nifa na dauka lafiyarsa kalau ashe da gaske baiji dadin ba"
Hararar Luba Rufaida tayi ta na kokarin furta wani Abu sukaji sallamar Wahid a falon amsa masa suka yi ya karasa shigowa Yasir da ya hango Yusuf yayi saurin sauka a hannun Abban nasa yayi wajen Yusuf 'din suka fara wasa
"Sannu da zuwa" suka yi kokarin hada baki duka gurin ce masa
"Yawwa,wa nake gani haka kamar Maman Yusuf hala makuwa kikayi ko?"
Wahid yayi maganar da murmushi kan fuskarsa
Luba tace
"Ai nafi matarka ita ko makuwarma yaushe rabon da tayi tazo gidanmu"
Wahid da yake kokarin zama kujerar gefensu yace
"Kuma tanbayarta kiji laifinta ne ba nawa ba"
Rufaida sai lokacin tasa baki tana dan hararar mijin nata ta wasa tace
"Kaji ka da wani zance,dan dan dai banasan tone tone amma da saina ce,anfi kwanan wata ina tanbayarka zani baka bani amsa,sai shekaran jiya kace.min naje,sai Yasir ya tashi da ciwo/a ranar zuwan namu"
Wahid ya kalli Rufaida yace
"To yanzu duk wannan dogon bayanin,me kikai inba tone tonenba"
Dariya sukayi gaba daya
Luba tace
"Oh Dadyn Yasir bamu gaisa ba hira tayi dadi,ina yini,ya aiki"
Wahid yace
"Gaskiya kuwa,lafiya Alhamdulillah ya abokin nawa dafatan yana lafiya"
"Alhamdulillah,tare muka fito ma yanzu zai karasa asibiti ne"cewar Luba
"Ok,sufa aikinsu babu hutu"fadin Wahid
" wallahi kuwa,yanzu muka gama maganar da Rufaida,gwara aikinku sosai"fadin Luba
"Kai Maman Yusuf babu wani gwara mutum ya fita tun safe shida gida sai yamma"Rufaida ta sa baki a hirartasu,gurin fadin haka
Luba ta rike baki tace
" iye mai miji yaushe kikeso ya dawo to?"
Harararta Rufaida tayi tace
"So nake 2ma tayi masa a gida"
Tsaki Luba taja mata
"Rufaida ta kalli Wahid tace
" Dady kaji ta harda tsaki ko nayi laifi ne?"
Ya 'dan rausaya kai yace
"A'a baki laifi ba,kinga bari nakira Kofur Musa ya karo yawan Ice cream din nan"
"Rufaida tace
" au dama buku siyo ba?"
"Eh mana da baki ga leda a hannu na,muna fita mukayi kicibis da Musa shine ya amshi key din daya motar na masa sautu dan banajin zuwa Shoprite a lokacin shi kuma har can zai karasa, mu kuma Unguwa muka zaga da Yasir"
Wahid yayi wannan maganar
"Ok,lallai kunsha aiki" Cewar Luba
Daganan suka cigaba da firarsu,Wahid ya mike bayan ya gama waya da Musa ya fito waje shida yaran ua barsu a falon suka cigaba da firarsu
Sai sannan Luba ta maida dubenta ga Rufaida kacokam ta soma magana
"Rufaida yanzu nakejin labari gurin,Kabir cewa AbdulWahid zai kara aure da wannan Ruqayyan da suka zauna da surikarki anan gidan amma Wahid din yace shi sam baya sonta"
Jin Luban ta kawo karshen zancenta yasa Rufaida kallonta,dukda bai taba fadamata zancen aurensa ba amma ta dade da sanin zancen Ruqayya tunma kafin suyi aure hakan yasa bata daga hankalinta da taji Luban tayi maganar yanzu kuma bata nuna mata rashin sanin taba tace
"Eh haka ne,Luba nidai indai zata zo da Alkhairi ina maraba da ita"
Luba ta jinjina kai tana mamakin jin wannan Kalmar daga bakin Rufaida don ita kanta tasan Rukayya ba alkhairi bace muddin ta shigo gidan Rufaida a matsayin kishiya bare kuma Rufaida tayi zaton haka,tun kafinma suyi kishin bata zo da Alkhairi ba bare yanzu da zasuyi zaman kishi,ita kam har mamakin Rufaida take lokuta da dama don gaskiya da itace bazata bari ayi mata haka ba,saboda tana samun wani labarin gurin Kabir mijinta ta dai yi kokarin kauda tunanin nata tace
"Hm Rufaida kenan,kina tunanin Rukayya ce Alkhairi,a zamanku kinadai sane da abubuwan da suka riqa faruwa a zamanku dake dasu,nima kuma ina ganin wasu da idona,kedai kiyi fatan Allah ya hadaki da abokiyar zama tagari badai Rukayya ba"
Rufaida tayi murmushi tace
"Don me za kice ba Ruqayya ba,bakya tunanin ta iya sauyawa idan anyi auren,shifa namiji ne shi zai saita gidansa"
Luba ta danyi dariya
"Au kina tunanin Rukayya zata canza lokaci guda,kintuna zagin da suka riqa yi miki ta uwa ta uba,da ita da surikarki,kuma ina gidan lokacin,karki yaudari kanki Rufaida, don hatta Abba Bukar yace bai amince da Wahid ya auri Rukayya ba,don shima kansa yana sane da komai"
Rufaida tace
"Duk da hakan da ya farun kinsan dai,Ruqayya tanasan Yaya Wahid zata daina koma meye,Abba Bukar kuma zai sauko"
Luba tace
"haka dai kikace,nidai kawai abinda zance miki ki cigaba da addu'a nima kuma zan cigaba da tayaki"
Da haka suka cigaba da hirarsu,da sai dare Luba ta bar gidan Rufaida don kawance suke sosai kamar sun dade da sanin juna kasancewarsu hatta a shekarun haihuwarsu daya shiya kara musu karfin kawancensu kuma kowacce ta yaba da halin kowacce"

Ayi manage don Allah kunsan yau da gobe sai Allah
Kardai ku manta mun dan waiwaya bayane amma next page insha Allah dawo Inda muka tsaya sai a dora insha Allah
Nagode masoya a duk inda kuke ina godiya Allah ya bamu iko anfani da sakon da littafin yakeson ya isar

Sadiya Ibrahim Khalil
(Sadiya Khalil)
*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil
46.
Ayi manage don Allah ba yawa kuyi min afuwa nace saura 1page adawo bayan da aka waiwaya yanzu kuma, saura 3page yanzu kuma saura 2page kenan ayi hakuri da spelling mistake

Sadiya Ibrahim Khalil
(Sadiya Khalil)
Chapter 45 · 0% Book details