← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 57

Sashe 50

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bukar ya kalli Rufaida yace " Rufaida mai ya hadaku da Ruqayya?" Idon Rufaida ne ya ciko da hawaye Abba Bukar yace "Kiyi min bayani ina sauraranki,banaso wani hawayen banza kiyi laifi kizo kina hawaye" Jin maganar Abba Bukar yasa Rufaida goge hawayenta ta zayyana masa duk abinda ya faru Abba Bukar yana gama ji ya dubi Ruqayya cikin bacin rai yace "Yanzu Ruqayya dama baki da mutunci ina ganin kamar zaki fita daban a cikin 'yan uwanki,shiyasa ma ke na amince ki zauna na lokacin da Jamila tace min zaki yi wato ashe har kin fisu ma,dama zaman danki kuntatawa Rufaida kika ce zaki yi" Rukayya tace "Abba dan Allah kaya hakuri ba haka nake ba Aunty Jamila ce take cewa na rika yi mata" Abba Bukar ya jinjina kai yace "Wato ita ke baki labaran karya da karai rayi akan Rufaidan ma ko?" Rukayya ta girgiza kai tana kallon Hajiya Jamila da take girgiza mata kai kar tace ita ce "Ki fadamin gaskiya bana son karya ita ke baki ko kuwa kifadamin wake baki" Abba Bukar yayi maganar yana kallon Hajiya Jamila yadda take girgiza wa Ruqayya kai Rukayya da duk ta tsorata tace "Eh Abba ita ce,tuntuni take bamu wannan labarin" Abba ya jinjina kai ya kalli Hajiya Jamila ya soma magana "Jamila kin bani mamaki amma ba abun mamaki bane nasan fiye da haka ma zaki yi saboda bakya tunani kafin ki aiwatar da abu sannan zai wuya idan kinyi badaidai din ba kiyi danasani,amma nasan akan wannan maganar tabbas zaki yi dana sani koba yanzu ba,sannan babu wani matakin da zan dauka akanki amma tabbas ranar dana sani zata zo miki,sannan yau ba sai gobe ba inaso Rukayya ta barmin gida na dama mahaifinta yayi min waya yanaso Rukayya ta koma gida saboda maganar aurenta da zai aurawa dan abokinsa ita da kune kuke ziga yarinyar karta yarda da auren,batun Rufaida kuma baza ta bar gidan nan ba sai sanda na tsara zata bari" Da wannan maganar Abba Bukar ya maida kallonsa ga Abdulmalik yace "Malik nasha fadama kai ba mace bane ka daina shiga fadan mata,banason karajin irin haka ta faru" Abdulmalik yace cikin ladabi "To Abba zan kiyaye insha Allah" amma a ransa baya tunani zai hakura muddin yaga ana kwarar Rufaida don shi mutum ne da bayason zalinci Da haka Abba Bukar ya bar gurin Abdulmalik da Rufaida suka take masa baya Hajiya Jamila jikinta duk yayi sanyi ta kama hannun Ruqayya,Ruqayya tayi saurin fincikewa daga rikon da Hajiya Jamillar tayi mata ta bar gurin don gani take duk Hajiya Jamila ce ta jawo mata koma mene yanzu ba ta da wata daraja a idon kishiyoyin Hajiya Jamila dama Rufaida ga uwa uba Abba Bukar,da gatanta da komai bawai arziki za'a nunawa mahaifinta ba bakomai ba amma ta ja an yi mata wulakanci har haka kum AbdulMalik ne yayi mata suma sauran matan gidan sumi sumi suka bar wajen aka bar Hajiya Jamila ita kadai ita mikewa tayi ta bar gurin.A daki ta samu Ruqayya tana hada kayanta Hajiya Jamila ta dafa Rukayya tayi saurin cire hannun Hajiya Jamila daga jikinta ta soma magana "Kinga Aunty don Allah ki kyaleni,kinsa an cimin mutunci,nima kuma kina zuga ni na ciwa wata,dama nina gaji da zaman gidan nan koda ba'a koreni ba,tafiya zanyi,gwara naje nabi umarnin Abba da na cigaba da zama anan,ki riqa gulmata na tare a gidan ki bayan wanda nake so dinma baya duniyar,amma kinsa ni na zauna ina goga kishi da matarsa bayan ita bata damu da muba" Hajiya Jamila da ranta ya fara 'baci ta kalli Rukayya tace "Kinga Rukayya a haife dai kinada tabbacin nayi 'yata hudu ma dake,ba zai yiyu ki zauna kina jeramin magana ba nina jawo miki dukan?ince dai ke kika jawo wa kanki,sannan dama fa ba wanda ya rike miki kafa kuma karki min sharri ni bance ki zauna a gidana ba,dama a zagwaigwai dinki ne yasaki zama a gidan nan,amma sanin kanki ne na nuna miki banaso saboda nasan baki da hankalin iya zama da mutane,baki iya rufe sirri ba,kinzo ni kin hadani da miji na cikin kishiyoyi kin kwance min zani" "Au haka zaki ce,kin mata harna hada kayana kila kika ce na zauna,ke ai abinda kika yi na fada nifa kinsa danki ya kwance min zani a kasuwa ya kuma yimin shegen duka kika zaunar dani" "Karfa kimin rashin kunya Rukayya ni zan sa AbdulMalik ya doke ki bakin halinki dai yasa ya doke ki" Dariya Rukayya tayi tace "Su bakin hali manya rashin kunya manya,aishi dama gwano bayajin warin jikinshi,nifa bari kiji baki isa ba wallahi ki fadamin magana na kyaleki,idan kina yiwa Rufaida tana kyaleki,to ni baki samu wannan damar ba ba kuma zaki sameta ba" Haka dai suka cigaba da musayar kalamai tsakanin Ruqayya da Hajiya Jamila saida Hajiya Kubra ta jiyo tazo ta yi musu magana ta kuma shiryawa Rukayya kayanta haka aka rabu da Ruqayya da Hajiya Jamila kaca kaca harda su gore gore (to dama ba dan Allah aka shirya zaman ba) Da Ruqayya ta fito saida ta shiga dakin Rufaida ta shiga da sallamarta Rufaida ta dago da kanta daga kallon wayar da take ta yi murmushi ganin Rukayya ce ta amsa mata sallamar jikin Rukayya a sake ta karaso inda Rufaida take zaune a kujera itama ta zauna kusa da ita ta kalli Rufaidan ta soma magana "Rufaida don Allah ki hakuri ki yafemin abubuwan dana rika yi miki Wallahi Umma ke zuga ni" Murmushi Rufaida tayi tace "Haba Rukayya karki bata bakinki nidama ban taba rikonki da komai ba" "Yawwa Rufaida nagode" "A'a ki daina yimin godiya,yanzu yaushe ne bikin naki ban taba jiba ko a firarku keda Umma" "Hmm kedai bari nice dama banason auren da tuni ma anyi har ankawo kudi fa jin yaya Wahid zai yarda da auren my shine naki yarda asa ranar,to jiya Abba ya kirani yace na shirya na dawo gida,shi bazan bashi kunya ba yasa bikina nanda wata biyu masu zuwa" "Allah sarki,a ina zaki yi auren?" "Adamawa ne" "Lah kinga inada kawa tana aure acan, zan hadaku insha Allah" "OK 'yar inace?" "Kano" "OK,ki bani Lambarta" Rufaida ta duba wayarta ta fado mata lambar Nasiba tasa a tata wayar tayi saving daganan Ruqayya ta amsa ta Rufaidan taayi saving da haka Rukayya ta mike tana cewa "To Rufaida nizan tafi,sai kinzo biki na nasan sannan kin dade da fita takaba tunda yanzu ma baifi saura kwana goma ba ki fita" "Eh hakane,amma kinsan indai na koma Kano ba lallai Abba ya yarda" "Nasan zai yarda insha Allah,sai dai.idan kece bazaki zo ba zaki ce" "A'a zanzo dama yardarshi nakewa kokwanto " "Idan lokacin yayi zan kira ki ki hadani da Ummi kinga saita fadawa Abba" "Murmushi Rufaida ta yi mata tace " to shikenan" "Kinga zan tafi va muyi sallama da yasir ba" "Eh wallahi babu rabo hakanan suka jashi Tahfiz yau din" "Babu komai Idan kunzo biki zan gaji da ganinsa ma indai da zan iya hakan" Dariya Rufaida ta yi tace "Oh saikace idan munzo din shekara za muyi" Da haka Rukayya ta fito sukayi sallama da Rufaida Rukayya tana sake rokar Rufaida ta daure tazo bikinta Bayan fitar Ruqayya Rufaida ta dan goge kwallar data taru a idanunta bata taba tunanin abubuwa zasu sauya lokaci kusa haka va,yanzu ko a mafarki idan aka ce mata Rukayya zata sota sai ta Musa saboda irin kiyayyar da Ruqayya ta rika nuna mata,lallai Allah shine mai juya al'amura tana da yakinin watara na komai zai zama tarihi,insha Allah kamar yadda kiyayyarta da Ruqayya ta zama labari.[9/25, 10:23 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA* By Sadiya Khalil 49. RA'UF POV "Ammi na yunwa nake ji" Ammi Asma'u ta juyo ta harari Ra'uf ta cigava da tafiyar da take "Ammi magana fa nake,ina jin yunwa,ki samamin abinci na ci" Ra'uf ya sake maimaita maganar Sai sannan tace "Ni zan kawo ma abincin kenan,kana kwance sai dai ayi ma komai" "Oh Ammi yanzu ba zaki kawon ba,shiyasa banso aka tafi da Safiyya ba da tuni ta kawomin" "Ita ce zata jure dama" "Au banda ke Ammi,shikenan bari na kira Dady a waya na fadamasa" "Au Da Dadynku zaka hadani yaro ka dade baka hada muba". Da ganan ta bar gurin Ra'uf ya saki murmushi ya tashi zaune daga ki shingidar da yayi jikin kujera ,wayarsa ya jawo ya danna ya kara a kunne a ringing biyu aka dauka muryar Safiyya ta shiga kunnensa da ta soma magana da yaran indiyanci da kuma turanci "Assalamu Alaikum,my Yaya" "Wa'alaikumus salam,kanwata ya gida da kowa da kowa" "Lafiya kalau" "Ya Nigeria,ina daru Hajiya" "Tana lafiya,amma Hajiya fa ta rage daru,muna zuwa ta fara korafi kai yaushe zaka zo" "Kina nufin bata bata ranki ba" "Eh tanbayarta taka ce kawai muna zuwa" "Kai amma naji dadi" "Yaya ysushe zaka zo,wallahi sun damu kazo Family 'dinka,gaskiya suna sonka sosai, dana ga yadda suka damu dakai nima sai nakeji ina ma ace watarana na hadu da nawa Family..." Ra'uf da hawaye suka tarar masa jin maganar da Safiyya keyi yace "Haba Sophie maiyasa kike da son dawo da abinda ya riga da ya wuce,mune familynki a yanzu haka,dan Allah ki cire komai a ranki" "To shikenan Yaya insha Allah" "Yawwa kanwata,yanzu kina ina ne" "Ina gidan Aunty Malika a can na sauka" "OK ina Auntyn" "Ta shiga kitchen" "Oh shine ba zaki je ki taya ta aiki ba" "Oh yaya kasan nafi iya abincin nan,karna mata jagwalgwalo tace ba dadi" Yayi dariya yace "Oh Safiyya idan kinyi aure fa,kuma kinsan dai a gida za'ami ki aure gwara tin wuri ki sauke wa kanki iyayi" "kai Yaya ba fa iyayi bane" "To menene" Canza maganar tayi tace "Yaya jiya munje asibitin daka gina da Abba ,yayi kyau sosai ni ban dauka yayi kyau haka ba dana gansa a waya sai da naganshi a fili" Dariya Ra'uf yayi yace "Ya kikaga sunan asibitin yayi kyau kuwa" "Sosai ma RJM DANBATTA" Dariya Ra'uf yayi yace "Yawwa kanwata idan zan sake gina wani,SJM DANBATTA zansa" "Kai amma naji dadi Yaya" "OK yaushe zaki tafi Kano" "Abba yace tare zamu tafi,sai ranar Asabar ta sama zai kaini 'danbatta nayi kwana biyu" "Ok Allah ya kaimu" Sun jima suna
Chapter 50 · 0% Book details