← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 57

Sashe 48

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

RUFAIDA
Rufaida tana kokarin fitowa daga kitchen taji yo muryar Yasir daga daki yana cewa
"Mami,Mami Samiha na waya"
Dakin ta shigo da tasa mu Yasir da wayar a kunnensa yana kokarin fitowa kawo mata wayar wayar ta amsa tasa a kunne ta gabatar da sallama Samihan ta amsa tare da ce mata
"Oh kin barni da surikina yana ta zuba min gwaranci ko little Rufaida ta fisa iya magana,ina kika je ne"
"Dama ina zai hada kansa da.wannan 'yar taki kamar ta saida mutane,wallahi na shiga kitchen ne"
"Au haka zaki ce,keba 'yar ki bace,tunda dai takwarar kice ai ba damuwa"
"Ato ai ni bana da damai surutu,tunda da 'ya tace bazatayi surutu ba,ya babyboy yanzu shine 'dana yana lafiya,an masa suna yau,naga baki kirani kinji sunan yaron bama"
"Sorry Samiha,kokarin da nake kenan dana baro kitchen din sai kuma naga kin kira,ya sunanshi?"
"Sunanshi AbdulRa'uf"
Jin sunan yasa Rufaida tuno da wancen Ra'uf din Allah sarki rayuwa,jin tayi shiru yasa Samiha cigaba da magana
"Ahmad ne yace sunan Ra'uf zaisa tunda nima nasa sunanki,kuma yace yanaso Rufaida da Ra'uf wadannan suyi rayuwa babu rabuwa sai mutuwa tunda sun fito ciki 'daya"
Rufaida jin maganar Samiha yasa ta sakin murmushi kamar tana ganinta tace
"Gaskiya,bansan irin kaunar da kuke mana ba,a tsawon rayuwarku"
"Soyayya ce dan Allah,ina Yaya Wahid din ne ko ya fita aiki ne"
"A'a baya jin dadi ne"
"Subhanallah kice ina gaidashi,ga Rufaida ku gaisa
Little Rufaida da take da surutu ta amshi wayar data matso a bata dama ta fara magana
"Mami,ina kwana"
"Lafiya kalau,Namesake,ya baby boy"
"Gashi nan,yanzu Mami ta daina daukata sai dai ta dauki,Little"
Dariya Rufaida tayi tace
"To ai yanzu kin zama babba yanzu"
"A'a mami ban yarda ba" ta karasa maganar kamar zata yi kuka
Dariya Rufaida tayi tace
"Ga Yasir nan na miki dariya,Rufaida tayi maganar tana bawa Yasir wayar"
Sun jima suna hira akarshe suka yi sallama jin turo kofar dakin nata yasa ta maida kallonta ga kofar dakin ganin Wahid ne ya shigo da shirin fita aiki yasa Rufaida kallonsa da mamaki tace
"Badai aiki zaka fita ba ko?"
Yayi murmushi ya rungume Yasir da rugo gurinsa yace Dady zan bika
"To my son jirani a falo na fito" don yawanci duk fitar da Wahid zeyi da Yasir ne hatta da gurin aikin yana fita da shi lokaaci lokaaci jin Yasir din ya fita ne ya sashi kallonta yace mata
"Eh mana My wife ko karna je"
"Eh mana,kasan baka jindadi"
"To ai nasamu sauki"
"A'a gashinan dagani kowa yasan bakada lafiya nasan karfin hali kawai zakayi don Allah ka hakura"
Kai ya girgiza yace "kiran gaggawa nasamu a office"
"To naji kabari nayi ma driving karkayi da kanka"
"A'a my wife kibari na kira kofur Musa yazo ya yii min driving 'din"
"Badai kaso nayi kawai zaka ce"
"no my wife banaso ki wahala ne,kinsan kece silar haskaka zuciyata fa kinga wazai so hasken rayuwarsa ya wahala"
"Hm kaga ma dadin bakinka dai"
"To ba kicemin nine haskenki ba?,koda yake nasan bani bane inaji a jikina zaki zauna da mutumin da zai zama sanadiyyar haska rayuwarki"
"To ai ba wani bane bayan kai ni Kaine haske na"
"Kinga ban yarda ba bani bane"
"To waye nidai nasan kaine" yana kokarin cewa wani abu yaji karar wayarsa ya ciro wayar a aljihunsa ya duba ganin lambar kofur Musa yasa Wahid cewa kinga bari naje Kofur Musa ya iso nake tunanin shike kirana yanzu
"To Yaya Allah ya kiyaye ya tsaraminkai take care bye"
"Amin ya rabb my wife take care too"
Da haka ya murda hannun kofar zai fita ya juyo ganin tana zaune yace
"Oh yau babu ko rako"
"Eh fushi nake dakai"
"Baki ya dan tabe yace kina fushin dani kika yi dogon fira dani"
"Ke dai kawai bakyason fita waje zaki ce"
"Kaje yana jiranka fa?"
"Shi waye mai jiran nawa?"
"Kofur Musa mana"
"Shikenan take care" ya fada da murmushinsa ya fice"
Itama kallonta kofar yayi bayan ya FIFA da murmushi akan fuskarta sai tace batajin a yanzu tana da sauran damuwa ta samu miji na gari mai kaunarta damuwarta daya sanin mai Umminsu tayi ta zama saniyar ware a cikin danginsu har ake mata kazafin karuwace don tana da yakinin shine ya ruguza waccen maganar aurenta,sai kuma son da take tasan mainene alakarsu da Danbatta family,dukda wannan yasa take rayuwa da Wahid bawai don soyayyarsa ta mamaye zuciyarta ba illa iyaka yayi mata halarci ya kauda kansa ga wancen abubuwan da ake fada akan mahaifiyarsu ya amince ya aureta dukda yadda ake fadar Umminsun takasance,wasu hawaye masu dumi ta goge wannan shine kawai damuwar da tayi saura a zuciyarta
*****
"Ra'uf
Koda maganar saka sunansa da Ahmad yayi ga dansa ta riske sa bakaramin farin ciki yayi ba a ransa yana ayyana cewa Rufaida da Ra'uf sun hadu a wata duniyar da babu wanda ya isa ya rabasu saboda sunzo a ciki daya tabbas yasan san Rufaida da kaunarta ba zasu gushe ba a zuciyarsa har zuwa ranar da zaiyi numfashi na karshe ya rasa gane wannan soyayya wacce iri ce,sai dai yace Allah ne ya hadata kawai bawai mutum ba,Dukda yadda iyayensa keso yayi aure yaki yi sam,gani yake baida lokacin ma tsayawa kula wasu 'yammata don gaskiya aure ba shine a gabansa a lokacin ginin asibiti da ya fara a Nigeria yanzu shine a gabansa ba maganar aure ba yanzu abinda ya damesa ya bunkasa kasarsa ta hanyar cigaba ta kowanne fanni shi kuma aure yasa a ransa lokaci ne,yanaso daya kammala gininsa ya koma gida ya samu ya sami nitsatstsiyar mata a kasarsa ya aura don shi gaskiya baya kawo wa ransa zai auri Rufaida saboda tayi aurenta ita tuntuni harma yaga kyakkyawan Baby boy dinta a Dp din Samiha daya na gani yaga kamar yaron da Wahid da bai manta kamanninsa ba shekarun baya da suka wuce ,Husna ta koma Nigeria a can zatayi bautar kasarta,data gama kuma za'ayi bikinta zata auri cousin dinsu Bello,Hajiya tayi tayi Ra'uf yazo Nigeria yaki sam bayajin son zuwa kuma koda ma zashi don su Yakumbo da Mama suwaiba zashi ba dan itaba
Chapter 48 · 0% Book details