← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 57

Sashe 51

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

waya daganan su kayi sallama suna gama wayar kiran Ahmad ya shigo wayarsa ya daga Ahmad yana jin Ra'uf ya daga yace "Oh kodai da budurwa kake waya ne,ina ta kira ana suna nuna min user busy" Ra'uf yayi Dariya yace "Ni budurwa,Safiyya ce muke fira" "Ok sun tafi Nigeria ko?" "Eh mana,kai yaushe zaka koma ne,kaje garin mutane kayi zamanka" "Wallahi sun hanani tafiya sun riqeni" "Oh kai tafiyarka mana" "Eh dama haka kawai za muyi shiryeye muke, Ni kaina nayi kewar gida over" "To yanzu ya little Rufaida ban tanbayeta ba" "Tana lafiya wato bazaka tanbayi little ba sai Rufaida" "Eh mana,ai ita takwarar masoyiyar farko ce,ko zaku bani aurenta tunda na rasa waccen Ahmad yayi dariya yace "Tsohon zan bawa 'yata sai dai kaje kayi zawarci gurin Rufaidan" "Ina ma za'a bani ita yanzu da sai naje wallahi" "Lallai Yaya Ra'uf bazawarar zaka aura,sun hana ka aurenta tana budurwa yanzu kawai tana bazawara kaje ka nemi aurenta" "Eh mana dama Allah yayi bani zan fara aurenta ba ne,kuma laifin fa su Abba Sule ne sune silar da aka hanani aurenta" "Haka dai kake tunani,amma dai sunyi niyyar dama aura mata dan uwanta ne kawai" "Karkayi wannan tunanin Ahmad,haka Allah ya tsara dama" "Haka ne kam,wallahi Yaya Ra'uf Rufaida abar tausayi ce,gaba daya abinda 'yan uwanta ke mata basa kyauta mata gashi Umminta bata isa tayi magana ba,Samiha tana bani labarin komai,kwanaki ma har kudi Samiha tasa na turawa Rufaidan ni na rasa meye matsalar" Ra'uf da jikinsa yayi sanyi yace "Maike faruwa ne Ahmad kayi min bayani ba Rufaidan na kano ba" "Ko d'aya tana Zaria" "Amma su iyayenta sun manta da abubuwan da suka rika faruwa suka barta acan" "Zumunci suke tunani shiyasa suke yin shiru nake tunani" Cikin bacin rai Ra'uf yace "An taba zumunci da zalinci,ni wallahi mutane mamaki suke bani don da bana ka bane idon yana tare dakai kaita zalintarshi" Da haka suka cigaba da tattaunawa akan maganar
Chapter 51 · 0% Book details