← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 57

Sashe 12

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SADIYA KHALI✍🏽*JININMU DAYA*
By Sadiya Ibrahim Khaliy(Sadiya Khaliy)

11

Rufaida Aliyu Bukar Hafaffiyar garin Zariya ce da aiki ya dawo da mahaifinta Aliyu Bukar cikin garin Kano yana aiki a babbar makaranta wato jami'ar Bayero University dake Kano wato BUK inda yake zaune a gidansa mallakin kansa dake Rijiyar Zaki shida matarsa 'daya wato Hauwa'u da suke da yaransu shida AbdurRafi shine babba sai Rufaida mai bi masa sai AbdurRashid,Rumaisa,Rafi'a,Ra'is shine karaminsu.

Samiha Hashim Sarki 'kawar Rufaida ce tun daga primary har zuwa Secondary da suke tafiya tare aji 'daya benci 'daya dalili mai karfi da ya jawo amintarsu harta zama sun zama kamar 'yan uwa hatta iyayensu wasu 'yan makarantar tasu ma 'daukarsu 'yan uwa ne Samiha hafaffiyar garin Sokoto ce aiki ya maido mahaifinsu Kano Unguwar Nasarawa GRA da mahaifin nasu yake kwararran likita a asibitin Nasarawa matarsa 'daya Hajiya Maryam da yaranta Samira,Samina da sukayi aure,Samir,Saudat,Samiha,Samin,Samima.da a yanzu haka Hajiya Maryam ta aurar da 'ya'ya biyu Samira da Samina kowacce da 'danta 'daya,Sai Samir da yake aboki ga AbdurRafi da suke babbar makaranta Jami' a Yusuf Maitama Sule Northwest dake nan Kano wannan kenan

Samiha da take kokarin sa'ba Jakarta a baya ta dubi Rufaida tace "malama ba kyaji antashi kuma kinsan yau juma'a a gidanku zanyi hutun karshen mako" Rufaida da murna batasan sanda tazari jakarta ba saboda murna Aminiyarta zatayi hutun karshen mako a gidansu mikewa tayi tana cewa"Nifa bansan dagaske kike ba"Samiha ta harareta tace"aikema kinsan bana miki karya irin wannan"da haka suka fito ajin da suka hadu da sauran 'yan class dinsu suna firar yadda Sir AbdurRahman ya iya koyarwa suna gane lesson dinshi da shine malaminsu na karshen period yau da wannan firar suka fito zuwa kofar makarantar inda suka hangi motar Abbansu Rufaida dasu yake jira suka karasa sunayiwa abokan tafiyartasu sallama"sauran 'kannen Rufaida har sun shige bayan mota su Rufaida gaban mota suka shige Abba da yake kokarin tada motarsa ya kalli Samiha da take gaishesa ya amsa yacigaba da cewa"wato Samiha mungane saboda kawarki kike zuwa gidanmu duk hutun karshen mako kike yi mana acan?"murmushi Samiha tayi kawai dan tagane Abba ya gano saboda Rufaida take zuwa gidan Abban hutun karshen makon dan ita tana matukar son kawarta da a yanzu take jin Rufaida kamar 'yar uwarta ta jini dan ko Saudat da Samihar ke binta bata saba da ita kamar Rufaida ba ,Samiha ta canza maganar tace "Abba ya maganar Jamb 'din namu" Abba da ya maida hankalinsa ga tuki yace "oh Samiha anfara ne"Rufaida anan tasa baki tace" Wallahi Abba ba'afara ba Samihan ce batada hakuri kofa yau saida ta tanbayi wani malaminmu" Samiha tace" eh mana dole kice banda hakuri tunda ke bakyasan cigaba da karatun yanzu idan bama tunawa Abba har a gama bamuyi ba"Rufaida tace"ba wani nan wallahi ai kinsan Abba baya mantuwa a harkar karatu barema harda Yaya Saudat za'ayi kinsan tunda tayi candy bazai manta ba,ke dai azalzalar kice,"Abba murmushi kawai yake yana jin firar tasu yadda sukeyi wanima sai ya rantse ya da kanwa ne ko 'yan biyu saboda halayyoyinsu da sukazo daya a fisgema har yanayi suke da juna yanason wannan abotar yaran nasa da ta zama yan uwantaka bama gasu ba harga su iyayensu sun hada aminci tsakaninsu kai kace 'yan uwa ne a yanzu haka idan ba har an baka labari ba,Abba yana saukesu d ,yace zaije gurin abokinshi yaje ya dawo su fa'dawa Umminsu a dawo lafiya suka yi masa ya amsa da amin yasakan motarsa yabar gidan su kuma suka shige cikin gidan a fall suka sami Ummi suka yi mata sannu da gida Ra'is mai shekaru biyu yana ganin Samiha yayi gunta da yasaba da ita saboda yadda take masa wasa daukar Ra'is 'din tayi ta haye dashi sama tana mass wasa yana dariya Samiha kaya kawai ta canza ana Rufaida dan girmansu daya hakama kayan sawarsu iri daya ne yawanci saboda yadda iyayensu suke aminta sosai kaya ma kusan tare suke dinka musu Rufaida data fito daga bandaki da towel jikinta ta watso ruwa ta kalli Samiha tace "ya haka ba zakiyi wanka bane" Samiha ta dafe cikinta tace"yunwa nakeji nayi anjima "Rufaida tace" ba wani anjima ,bakyasan yin wanka sai dole kike 'daya badan kinso ba haka Ahmad 'din zai aureki ki bakyason yin wanka wallahi ya daukeki kazama"da Rufaida da tasan sunan Ahmad saboda labarinshi da Samiha take basu nashi kullum indai sun ha'du a makaranta to indai kana ajinsu sai Kasan labarin Ahmad saurayin Samiha a bakin Samihar "Samiha tace to"yi maza ki fadamasa"Samiha ta fice tana jiyo dariyar Rufaida

Samihan kai tsaye kitchen ta nufa ta samo abincin rana da miya taliya kawai tagama sai miya da take kan wuta da shigowarsu Ummi ta zuba markadan kayan miyan gurin datasan ana aje ragowar miya ta bude ta diba ta fito kai tsaye babban falo ta karasa bayan fitowarta kitchen din da ta samu AbdurRafi shi ka'dai ta masa sallama AbdurRafi ya amsa mata ya maida dubensa ga kallon ball din daya kori kannensa a falon yanayi ganin ancanza masa tasha ya juyo ya 'dan kalleta da ta zauna a kujerar dake gefen tasa ta tankwashe kafafunta akan kujerar ga remote tana dannawa tana lalubo tashar da takesan kallo yace cikin ha'de rai " waike Samiha ina kallo ya zaki canzamin tasha"Samiha tace"ai kaine Yaya AbdurRafi ko gaishe da nayi kaki amsawa kana can hankalinka yana kan kallon ball"AvdurRafi yace"ke Samiha banafa son karya a ina kika gaishe ni sallama kawai naji kinyi,ke dai kawai kinzo ki takurawa mutane indai kikazo gidan mutum bashida kata'bus"Samiha tace"kai Yaya AbdurRafi gaskiya bakayimin shaida maikyau ba amma bakomai nakusa daina zuwa ai"tsaki AbdurRafi yayi yace"yaushe ai sai dai in anyiwa wadda kike zuwa gunta aure ko an yimiki"Samiha tace"kai nifa Yaya AbdurRafi kadaina maganar idan munyi aure zamu rabu da Rufaida ga gida ga gida zamu zauna"AbdurRafi yace"Ku auri miji 'daya kawai zaifi"Samiha tace"kai Yaya"AbdurRafi yace"eh mana zaifi ai"Samiha ta canza firar da cewa "wai niko Yaya Rufaida ta baka labarin wani saban malaminmu da kuke kama yazo TP da ake turo masu Degree?" Tsaki AbdurRafi yayi yace "ke nifa kinga banasan shirme wallahi ni ka'dai Ummi ta haifa kuma ni ni ka'dai ne bada wanda nake kama a duniyar nan ma gaba 'daya kawai kuje Ku jajubo wani bakusan shi waye ba kuce ina kama dashi?" Samiha tace"haba Yaya AbdurRafi wannan dogon turanci haka daga nace kana kama da wani Allah ya baka hakuri,kuma ka masan shi waye 'dan Khalid Bashar ne" AbdurRafi yace"ke nifa Samiha ki dainamin maganar shi banaso,dama dan haka kikashemin kallon ball din danake"Samiha tace"Allah ya baka hakuri,amma nidai Allah naga kamarku"AbdurRafi ya mike yace"sai kiyi tayi ni kinga tafiya tama yayi gaba ya fara tafiya"Samiha da taga yana kokarin ficewa a falon da taga bayaso ace yana kama da kowa ta tsokanesa tana cewa "Yaya AbdurRafi Allah kuna matukar kama" murmushin mugunta yayi yana tuna abinda zai mata ya karasa ficewa daga falon gaba daya"Samiha ta bishi da dariya Ummi data shigo falon tana lallashin Ra'is da yake kuka taji Samiha na dariya tace"dariyar me kuma kike kuma kike kinje kin bawa yara yaro na sun yarmin dashi shine kike dariya ko?"Samiha tace"Ayya Ummi wallahi Rumaisa ce ta anshe shi da muka hau sama"Ummi Hauwa'u tace"to gashinan dai kin basu yarona sunyi fa'da da Rafi'a sunyarmin dashi,na 'daukama dariyar kike masa"Samiha ta anshi Ra'uf a hannun Ummi Hauwa'u tana lallashinsa tace"Haba Ummi ya kinsan nida Ra'is da amana,Yaya AbdurRafi nakewa dariya saboda nace yana kama da wani malaminmu yake jin haushi bayaso ace yana kama da wani"Ummi Hauwa'u tace"au wai saboda ance yana kama da wani yaji haushin Allah ya kyauta"Samiha tace"Amin dai Ummi" Samihan ta fara lomar abincinta data zubo tana bawa Ra'is Ummi ta wuce kitchen ta cigaba da aikin abincin da take Abba Aliyu ne yashigo gidan da motarsa ganin AbdurRafi ya budemasa gate "yace ya shigo ya shirya su tafi masallaci kasancewar yau Juma'ah yana shigowa falon yayi sallama,Samiha ta amsa masa takuma ce "Abba sannu da zuwa yace" yawwa Samiha ina sauran mutanan gidan" Samiha tace"Suna ciki Ummi kuma na kitchen"Ra'is da yaga Abbansu ya sauka daga hannu Samiha ya tafi gurin Abban nasu,Abba Aliyu ya daukesa yana cewa"nifa Ra'is shirin masallaci zanyi amma bari na tafi dakai na bawa ko Rufaida kai ne ko Rumaisa tunda kunfara batawa da yayartaka" murmushi Samiha tayi kawai ta harari Ra'is da haka Abba Aliyu yayi saman bene dashi 'dakinsu AvdurRashid kai tsaye Abba ya shiga yace ma AbdurRashid yayi shirin masallaci ya bawa Rumaisa Ra'is daya sameta a falon saman AbdurRashid yana fitowa daga dakinsu saboda tafiya masallaci yaga Samiha a falo da kwanon abinci a kan teburin tsakiyar falo tagama ci tana lashe hannu yace" uwar ci 'yanci kawai"Samiha tace"naji dai da ulcer ta kama nifa"AbdurRashid yace"ba wani aike cinki yayi yawa kuma ci babu kuf kullu jiya i......"jin karar takalmi yasa AbdurRashid kin karasa maganr yamayi had ficewa daga falon kar wani ya shigo yaji yana yiwa Samiha rashin kunya Samiha tace zaka dawo kasame nine mara kunya ganin AbdurRafi ne ya shigo falon ya wuce ko Samiha baikula ba tana kunshe dariyarta ganin wai shi ala dole yayi fushi da ita Rufaida tana zura kaya barci ta haye gado barci ya 'dauketa kasancewar basa taya Ummi abinci da rana saboda makaranta.

SADIYA KHALIY✍🏽*JININMU 'DAYA*♦️
By Sadiya Ibrahim Khaliy💞

Page 12
Chapter 12 · 0% Book details