Sashe 36
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ABDULWAHID
"Hajiya Jamila ta zauna gefen gadon da ta samu Wahid kai ta cije le'benta na katsa
AbdulWahid da tunda ta shigo dakin bayan ya amsa mata sallama yake kallonta saboda yasan babban abu ne zaisa Ummantasu shigowa dakinsa da yake kwana,maganarta ta maidoshi daga wancen tunanin da take
" Nasa Abdussalam yayi min kiranka 'dazu yace yazo baka nan"
Cike da nuna girmamawa yace
"Eh Umma naje gidan su Gwaggo Zainabu ne"
"Gurin Rufaida ko"
Hajiya Jamilar ta yi maganar ta kuma cigaba da cewa
"Wahid maiyasa kakeson abinda raina zai baci"
Da sauri ya 'dago ya kalli mahaifiyar tasa
Kai ta daga masa ta cigaba da magana
"Kwarai kuwa Wahid da bakaso da baka yi gigin kwatanta koda son Rufaida ba bare har kaso aurenta,kana sane da buku dace da juna ba ta kowacce fuska,wannan tunanin da nake yana kara batamin rai idan naji ita kakeso ka aura bayan kai masa nine akan komai,tun farko har zuwa yanzu,ga uwa uba kasan halin munafurcin Hauwa'u da mai goye mata bayan Gwaggo Zainabu shiyasa banasan ka aureta saboda....
"Haba Umma maganar duk ta mecece hakan ,dukdan akan nace inasan Rufaida"
AbdulWahid yayi maganar yana kokarin katse maganganun da mahaifiyar tashi keyi.
"Murmushin alamun cin nasara da take ganin ta farayi tayi daga visa ni tace
" to naji zan daina amma sai kamin alkawarin zaka janye maganar aurenka da Rufaida,ka amince ka auri Rukayya yarinyar nan tana sanka gata mai hankali ga iya zama da mutane,kuma kana sane da irin soyayyar da Yaya Sha'awa(wato mahaifiyar Rukayyan keyi ma tana sanka kamar 'dan cikinta
Shiru yayi yana tunanin maganganunta da duk ba gaskiya a cikinsu kafin ya ce
"To Umma zanyi tunani"
Da fara'a akan fuskarta da jin maganar da yayi tace
"Yawwa Wahid Allah yayima albarka amma dai kayi tunani mai kyau" da haka ta mike ta tura masa daki
Bayan fitarta ya kwanta yana tunani ,tabbas yasan yanasan Rufaida bayaji zai iya rabuwa da ita,kuma idan ya rabu da ita yasan babu lalle a wannan zamanin ya samu tanada halayya mai kyawun gaske, yasan kawai dan kiyayyar da Ummansa ke musu yasa take alakanta su da munanan zantuka,gaskiya bayaji a ransa zaibi maganar mahaifiyarsa ,saboda nufin Alkhairi ya keson yi,toma idan bai aureta ba Rukayya da takeso ya aura shifa basanta yake ba da aure,batayi masa ba a irin matan da yakeson aura,bata da kunya ga raina mutane to ma shi mai zai kaisa yayi sure a dangin mahaifiyarsa da duk halayyoyinsu daya yawancinsu musamman ma Aunty Sha'awa mahaifiyar Rukayya da ta takasu rashin mutuncin,yana sane da kallon wulakancin da Aunty Sha'awa keyi musu idan sukaje Nasarawa Ummansu tace suje gidanta kasancewar mai kudi take aure ,wanda saida mahaifinsu yayi kudi ta dawo tana kaunarsu,shine yanzu akeso a makala masa Rukayya saboda sunga shima ya dago da arzikinsa,dukda Ummansu batasan wulakancin da Aunty Sha"awa ta riqa musu ba idan sunje gidanta saboda basa fadamata amma su suna sane busu manta ba ,da wannan tunanin ya kwanta ba tare da ya kira Rufaida ba da ya fadamata zai kirata idan ya koma gidan da yana dawowa Umman tasu ta shigo ta tare sa da wannan maganganun.
KANO
Abba Aliyu da ya fada'da fara'arsa da shigowarsa cikin falon ya tarar da iyalansa guri guda zaune suna fira shima fasa fitar da ya fito da niyyar yi yana kokarin zama
"Abba sannu da fitowa" yaran suka hada baki gurin fadar hakan.
Da yawwa ya amsa ya zauna kujera yana sauraron firarrakin nasu da kusan duk na yayarsu ne da sai yanzu ya tuna bai fadamusu bikin ta saura sati uku ba da shima jiya Abba Bukar ya kira yake shaida masa dukda baiji dadin abinda Abba Bukar yayi akan 'yar tasa ba ace babu ko shawartarsa a ce za'ayi aure asa biki sati hudu saikace bazawara dukda dai ana hakan amma bawai yanzu ba saboda idan ya shirya shi Uban 'dan to shi bai shirya ba,ga dadin bacin rai shida 'yarsa ba'atashi fadamasa bikin ba sai saura sati uku,saidai inda hankalinsa ya kwanta Abba Bukar din yace shi zai mata komai,shine zuciyarsa ta daina ganin laifin Abba Bukar din,sai dai yanzu zulluminsa guda yadda Hauwa'u zata dauki lamarin da har yau zullumin sanarmata bikin yake,dukda yasan bata kyauta musu ba amma yanzu yana ganin sunfita rashin kyautawa koda ita Rufaida 'yar rikoce gare ta abinda sukayi busu kyauta ba asa ranar 'yarta ba'anemi shawarar ta ba aka zartar da hukunci,sallamar Ummi Hauwa'u ta maidosa daga wancen tunanin nasa,amsa mata sukayi shida yaran suna yi mata sannu da zuwa Rafi'a ta fado jikinta tana yi mata oyoyo
Sauran yaran suna dariya suna cewa
"Kamar Ummin ta shekara a wani gurin"
Hauwa ta hararesu ta riqe hannun Rafi'a suka karaso cikin falon
"Ai tafi ku sona ne kuda ko murna bangani kan fuskarku ba"
Rumaisa tace
"Wallahi Ummi munfi sonki kinga yadda mukai kewarki tanbayi Abba kiji hirarki data Yaya kawai muke tunda kika fita ya jikin Ra'is din namu"
Ummi Hauwa'u ta murmusa tana zaunakujerar da mijin nata ke kai sannan tace yana gurin yayanku yaji sauki"
"To Allah ya kara sauki" cewar AbdulRashid.
"Amin ya rabb
Kallonta ta maida ga Abba Aliyu ta dan dubesa ganin fuskarsa babu walwala ba kamar yadda suka barsa ba,gashi bayasa baki a firar tasu.
"Abban Abdul anya lafiyarka kalau kuwa"
Sai da yaji muryarta sannan ya fahimci ashe harta zauna kusa da shi baisani ba yanacan yana tunani murmushi ya ka kalo
"Me kika gani,bayan nine na fara yi miki sannu da zuwa,ina Ra'is din ya jikin nasa"
"Hmm,akwai abinda ke damunka nake tunani gashi baka walwala,yana hannun Abdul yanzu zasu shigo a rubuto masa magunguna ,anyi masa allurai,sai dai kudin daka bayar busu isa an siyosu duka ba,ni kuma babu kudi a gu...
Bata karasa maganar ba sallamar su Abdul ta katse ta da ya shigo,sabe da Ra'is a kafada da Ra'is din ke shan alawa,daya hannunsa kuma rike da ledar maganin,sallamar suka amsa masa dukansu,kannensa suka masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera ya sauke Ra'is shima kan kujerar yaran suna yima Ra'is ya jiki
Abba Aliyu yayi gyaran murya ,ya kalli Hauwa'u yanasan sanar musu lokacin ranar Rufaida da Abba Bukar yasa,dan boyewar batada anfani tunda Allah ya gani ba shida laifi shi,magana ya soma
"Jiya da nayi waya da Yaya Bukar ya shaidamin sun saka ranar Rufaida wancen satin yau saura sati uku nan gaba"
Abdul da yaji maganar kamar dirar aradu
"What Abba mai kake fada Rufaidan za'ayiwa wannan auran biki wata guda kamar wata bazawara aiko masu kudi da suke tada kai dasu basa irin wannan auran sai....
Abba cikin bacin rai ya soma magana bai bari Abdul ya gama tasa maganar ba don batun yau ba ya fahimci Abdul wata rashim kunya yake ji dashi ma yi masan zaiyi.
" Sai Ubanka kome zaka ce ,dan uwarka yarinyar ta samu miji yana santa sai aki aura mata shi,so kake atasa ta a dunga kallo,kota dinga yi mana jajibe jajiben samari wawaye da busu san darajar dan adam ba"
Ummi Hauwa'u da take jin maganarsu saidai ta kasa tsaidasu saboda yadda ita ma ranta yake bace a wannan lokacin,ita da 'yarta a dauke mata ita kan kuskuren da ita bata ma gansa ba,dan zuwa yanzu ta fara gajiya da halin Aliyu komai za'ayi baza'a shawarce taba saboda son kai irin nasa
Abdul ya dan sassauta murya ganin mahaifin nasa kalaman da yayi masa sun bata ransa har yana zaginsa da kafin kaji Abban nasu yayi zagi to tabbbas zaka dade
"Amma Abba ai karatu zata cigaba dayi da mun kyaleta,aure lokaci ne ai koda ma ba karatun zatayi ba, mu ba zamu gaji da ganinta ba dadai auran Yaya Wahid da zatayi gwara ta shekara goma ba aure, kota auri wancen saurayin nata dukda ba'a sansa nake ba,haba Abba maiyasa kake kokarin manta kiyayyyar da Umma Jamila ke gwada ma..."
Cikin zafin nama Ummi Hauwa'u ta taso daga Inda take ta rufe bakin Abdul ta wankesa da mari,dan idan tabarsa dukda ita ma ranta a bace yake da Abba Aliyu amma tasan Abba Aliyu uba yake ga Abdul bazata bari ya cigaba da sa'insa da Ubansa ba,dan bats yimasa irin wannan tarbiyyarba ita bata tana sa'insa da Abbansu a gabansa ba,dan yau kenan ka haifesa ne amma baka haifi halinsa ba,gashi a gaban kannensa,hannunsa taja da karfi zuwa upstairs tana magana cikin fada
"Abdul baka da hankali mahaifinnaka kake fadawa haka,kamanta duk karkashinsa muke yanada ikon zartar da hukunci akanmu...."
Da wannan maganar suka karasa hayewa Upstairs din da Abba Aliyu ya bisu da kallo da ransa ke masa tukuki yanzu ace Abdul shike fadamasa bakaken maganganu har haka gaban sauran kannensa dukda yasan ya musu laifi amma dai abinda Abdul yayi masa ya bata ransa matsayin Abdul na dan cikinsa koshi sa'ansa ne sai haka ,baya tunanin Hauwa'u tanada laifi wajen lalacewar yaran da yake nema yayi yanzu,saidai zai yiwa tufkar hanci,kofa yayiya mike ya duba magunan Ra'is da suke leda ya dauki kati yaje ya ciko masa ragowar magunan da aka rubuta masa
Yaran da babu wanda ya shiga maganar da tsoro fal ransu ,dansu basu taba cin karo da wannan matsalar ba bare su saba da ita tunda suka taso a gidansu ba akwai girmama juna atsakaninsu amma lokaci guda gashi ana musayar magana tsakanin Abbansu da Yayansu busu san meke shirin faruwa da suba Ra'is da kowa yaki kulasa kuma yaji hayaniya da baisa ba da jiba ya rushe da kuka Rumaisa ta daukesa tahau lallashi dan ko kusa bata yi gigin kaisa gurin Umminsu ba dan a yadda taga bacin rai a ranta ta iya dukanta ma"
Team of Rufaida ,team of AbdulWahid,team of AbdulRa'uf
Team of Ra'uf
Anya ba za'a yiwa AbdulRa'uf sakiyar da ba ruwa ba koda yake dama dai anmasa saidai ya rungumi sorry
Team of Wahid
Ya kuke tunanin zata kasance idan Hajiya Jamila taji labarin.wannan bikin anya zata yarda kuwa?kai akwaifa gwarama a gaba nake tunani. Nidai na fece bani na fada ba😂😂🚶🏽♀️🚶🏽♀️🚶🏽♀️🚶🏽♀️
A suburbudo ruwan comments aga typing nagama sa ayau😂😂 basai gobe baFJininmu 'daya
By Sadiya Khalil
Page 39