Sashe 15
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ummi Hauwa'u da take zaune bakin gado tana canzawa Ra'is kaya Rufaida ta turo dakin bayan taji Ummi ta amsa masa sallamar da tajira ta amsa tukunno kai dakin Rufaida da Rafi'a mai kusan shekaru biyar ko shida a hannunta ta dubi Umminnasu tace"Ummi nagama shiryawa kudin Napep zaki bamu mu tafi" Ummi Hauwa'u ta dubeta bawata kwalliya fuskarta dan Rufaida ba mace bace mai son kwalliya mai yawa bama taga Rafi'a ba tace"karasa shiryamin Ra'is to na daukomiki "badan tasoba ta zauna gefen gado dan ita macace mai son gayu bataso tayi wanka taga kayanta duk sun cukurku'de sau tari Ummi nace mata zata daina ne data haifi data fara tara yara amsar Ra'is tayi ta fara kokawar sama sa wando Rafi's tana masa wasa ummi Hauwa'u tana kallon yadda take 'bata rai tanasa masa wando sai alokacin ta lura da Rafi'a ta duba inda ta aje kudin tace"har kin shirya Rafi'a ne naga kamar baki mata wanka ba kuma kinsan dai bazata bari ki tafi gidan Momy Maryam ba banda ita kimayi kokarin shiryata kafin ku tafi ko kuma ki tafi da Ra'is" Rufaida tace"Momy biki ga nayi mata kwalliya ba,ai momy gwara yawo ma da Rafi'a dukda surutunta dadai kukan Ra'is yataramin Jama'a ace na satosa"Ummi Hauwa'u tace"ke banfasan wulakanci 'dan autan nawa kike cewa yana kuka ,ta mika mata kudin data dauko taceni anshi kudin ki wuce ku tafi"Rufaida ta dungurar da Ra'is gado ta amshi kudin Napep dari biyar kuka Ra'is ya fara "Ummi wannan mai kai kwal uku shine Autan Ai ko zakiyi auta kyakkyawa ne ""Ummi Hauwa'u ta daukesa tana lallashi tace "ke karfa ki jiwa 'dana ciwo yanzu da akasa yake da tuni ya ji zafi koma yaji ciwo" Rufaida tace"yanxu Ummi daga dungurarwa sai kice da akasa ne saiyaji ciwo tace"eh man baki San tsautsai ba ,kuma ma Ra'is dakike fa'dar muninsa dake yake kama" Rafi'a ta kunshe baki da dariya ta tahomata,Rufaida tace wallahi yarinya kikamin dariya fasa zuwa zanyi dake"Ummi tace"haba yarinya ai baki isa ba kuwa tare zaku itama taje taga kawarta Samima "murmushi Rufaida tayi dan hirarsu da Umminta bata karewa takama hannun Rafi'a suka bar dakin suna cewa da Ummin sun tafi addu'a ta bisu da ita tana kara jin kaunar wannan zuriya tata da Allah ya azurtata da samu*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khaliy
Page 15
ASuna isowa bakin titi suka tari adaidaita zuwa Nasarawa GRA a flyover wajen bada hannu suka tsaya saboda go slow suna tsayawa Rafi'a da ta fara kalle kalle ta hango wata mota dake 'bangaren hagunsu motar akwai daukar ido sosai matashin cikin motar Rafi'a ta soma nunawa Rufaida tace"Yaya kalli waccen Ash din motar kiga mai kama da Yayanmu"Rufaidsa da take ji mai tace tayi banza da ita dan inta daka ta Rafi'a saita ja musu zagima yanzu saida ta kuma maimaitawa sannan Rufaida ta doke hannunta ta kalli motar da bata kalli na ciki ba tace" nagani wadda bata iya gani ta kyale aike dama matsalar zuwa unguwa dake kenan surutu da kalle kalle yanzu idan mai motar yaga kina nuna safa ba kisan koshi waye ba haka kurum kijamin"Rafi'a tace"Yaya Allah da gaske nake ki kalla mai tuka motar sosai kigani"Rufaida da ranta yafara baci tace naji zan kalla amma kinsan Allah naga akasin haka wallahi saina dokeki idan muka koma gida ko kuma nadaina fita unguwa dake kinyarda "Rafi'a tace "Eh"motar da take nunawa Rufaida ta zuru kanta waje taga matukin motar Kallo 'daya Rufaida ta masa ta fahimci kamarsu sosai da AbdurRafi harma tafi wadda ake ganin AbdurRahman malaminsu yanayi da AbdurRafi dan ita saitace ita bama ta taba ganin kamar AbdurRafi da AbdurRahman ba kurum su Nasiba ke haukansu da Samiha take tayasu,amma wannan matashin na cikin motar banda yanayin shekaru da shi wannan na motar zai iya dara Yayan nasu shekaru ba da kuma yanayin hasken fata da wannan ya 'dara AbdurRafi yayansu haske da sai tace shine ma yayansu" maganar Rafi'a ta dawo daga tunanin data tafi tace"Yaya kema kingani ko ki masa magana koma yayanne"Rufaida tace"banda abin Rafi'a daga kama sai ace lallai wanda kasani ne"Rufaida batayi aune ba taji muryar Rafi'a tana dagawa na motar hannu tana"yaya,yayanmu"Rufaida da zata finciko hannunta mai tuka a daidaita sahun da ya gani ta cikin maduni ya juyo da yake jin duk hirarsu kawai shi bayason shiga hurumin da bana shiba ne "yace haba 'kyaleta mana kikasani ko yayan naku ne"Rufaida da takaici ya fara isarta cikin napep din ta maido kanta tanajin haushi abinda Rafi'a keyi tana kwalawa bawan Allah kira da suna Yaya aranta tanaji ba zata kara yawo konan dacan da Rafi'aba karta dinga jawomata abin magana sai da Rafi'a taga ya juyo ya mata murmushi da shima saurayin matashin maganar da Rafi'a keyi ya fara isarsa har yafara tunanin dashi ake shine dalilin waigowarsa ganin karamar yarinyace mai zubin Hausa Fulani ya sakar mata murmushi ya tada motarsa ganin an fara yi masa horn a baya ma'ana danja ta kawo kenan,Rafi'a ta shigo cikin motar ta sannan mai napep din shima ya tayar Rufaida tace"kingama shirmen naki kenan,zuwa dake kuma unguwa yayi kai ko zanyi sai an dade mai napep din da yake tu',kinsa yace"haba ke kuwa yayanta fa ta gani take kiransa,kinsan harkar yaro sai ana hakuri ,dukansu ba wanda ya kuma tofa alif itama Rafi'a tsoronta kar takuma wani laifin da za'a daina fita unguwa da ita gaba 'daya suna isa Nasarawa GRA ya shiga Latin Khalid Bashar Majiya ya danyi tafiya a layin kadan ya kuma shiga wata kwana nan ya tsaya ya Rufaida ta mikamasa kudinsa bayan ta fito tace " gashi bamu canji"amsa yayi ya duba aljihunsa ya mika mata canjin yayi gaba Rufaida hannun Rafi'a ta kama tanata mata fada akan suruntunta yayi yawa kofar gate din gidansu Samiha suka tsaya suka kwankwasa mai gadi ya karaso kofar yace"waye"Rufaida tace"baba su Rufaida ne"ya bude kofar jikin gate din da ake wucewa yana cewa "ah'ah yau kuma antuna da zumunci kenan" Rufaida da suka shigo ciki race"ai Baba dama munayi ko sati ba'ayi ba da zuwa na aka cemin kaje kauyenku ,yaronka baya jin da'di"yace"wallahi jikata jikin yaron ne usaiba yaki dadi da yaji sauki sai ciwo ya dawo to yanzu dai da sau'ki nazo dashi asibitin cikin birni an dubashi ance typhoid ce da aka rubutan magani Abbanku ne ma ya siya yanzu dai jiki ya fara warkewa"Rufaida da taga ne nufinsa Abba Hashim Abbansu Samiha wato yake nufi" cikin nuna tausayi tace"Baba Allah ya kara lafiya,shi kuma Abba Allah ya kara masa budi"yace amin amin 'yata"Rufaida tace au Baba bamu gaisa ba gaisawar sukayi Rafi'a ma ta gaishesa daganan suka cigaba da tafiya cikin gidan aranta tana tausayin talaka dukda su 'dinma ba masu ku'di bane can dan albashin mahaifin nasu tasan a gurin wasuda yawa masu kudin kudin kashewa ne na siyan kayan kwalliya da kayan saws dukda yawan kudin wasu ma sai an karo linkinsu amma dai sai tace sudai Asirinsu a rufe yake mutum ashirin ma zasu iyaci a karkashinsu da wadannan kudin albashin nasa shima Abbansu akwai tausayin mabukata yana da alkhairi Allah Rufaida take kara godewa da ni'imar da suke a ciki ita a koyaushe na kasa dasu take hanga