← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 57

Sashe 39

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan wanne irin aure ne Gwaggo daga zuwan mu yau ace yanzu za'a daura"Momy Maryam tayi maganar bayan Malam ya fice daga dakin
Gwaggo da ranta ya fara baci ita ma
"To ya za'ayi Maryam yadda suka tsara haka za'ayi"
"A'a Gwaggo kuma fa kuna da hakkin magana akan 'yar nan ai ba 'yarsu bace su ka'dai,ya daga zuwanmu za'ace yau daurin aure gaskiya babu alamun gaskiya a auren nan"
Momy maryam tayi maganar
"A'a maryam kar kice haka,mudai yi musu fatan zaman lafiya"
Cewar Gwaggo
Ummi Hauwa'u bata ce komai ba tana zaune tana saurarensu har suka gama firarsu
*******
"Rufaida Dan Allah karki nunama yayyenki ko a fuska akwai abinda ya faru dazu"Harira tayi maganar tana dafa Rufaida da suke daki zaune itada harirar tun da su Aunty Samina suka karbi aikin
" Harira ke ma kinsan halina a 'dan zaman da mukai kinsan bazan iya fada ba,abinda kuma Umma tayimin lokaci ne watarana sai labari"
Cewar Rufaida
"Harira ta nisa tace
" nifa matarnan ta bani mamaki kai kace mahaukaciya ce ,kikama 'yar mutane ki shage,shegiyar mata kodaddar banza ita banda farin tama wazai kwasheta mai bakin hali,ai wallahi dan sunga kece shiyasa zasu hadaki aure dashi da wata fitsararriyar suka samu ai bazata yarda ba a rabani da dan arziki a hadani da irin tsiya....
"Kai kai Harira wannan surutu haka kinata kwashe mata zunubi kina dorawa kanki ta hanyar zaginta"
"Ai matar ce na lura da cewa cikin dabbobi Kafin asamu irinta za'a yara"
Rufaida tayi dariya jin maganar Harira

Aunty Samira da take tsaye bakin kofar dakin dasu Rufaida ke ciki azo kiran Harira ta tayasu aikin da suke tayi niyyar shigowa taji suna wannan maganar bata shiga ba ta dawo inda suke aikin tana jinjina lamarin aranta ashe shiyasa suka ga alamun damuwa a gidan da suka zo har Rufaida bata wani nuna murnar zuwansu ba,lallai akwai matsala a wannan auren amma yaza suyi itada ko kusa bataso auren nan Rufaida ba koda ma ba wata matsala dan tana son Rufaida kamar Samiha.
Aunty Samina ta kalli Samira tace
Yadai Samira maike damunki
"Kedai bari kawai Yaya ashe 'dazu surikar Rufaida ce tazo tayi wa Rufaida duka ta shake wuyanta ta kusa kasheta"
Maganar suka cigaba da tattaunawa saida Harira ta karaso wajen sukayi shiru

*****
Sallamar Abba Bukar a falo yasa kowaccensu amsa masa da kokarin yi masa Sannu da zuwa ya amsawa matan nasa da ko wacce da maganar dake bakinta ga mijin nata ganin vaidawo yadda ya saba dawowa ba dan har hudu ta gota yanzun daya shigo,maganarsa ya dawo dashi daga tunaninsu
"Yadai kowacce tayimin kasake kamar nayi tafiyar shekara ba wadda ta iya koda mikewa ta kawon ruwa" yayi maganar da murmushi kan fuskarsa
Hajiya Kubra tayi hanzarin cewa
"Abban Wahid ka manta yauba girkin daya daga cikinmu na Maman Wahid ne kuma tunda ta fita har yau bata dawo ba"
"Kinga Ku share zancen ta"
Abinda ya faru ya sanar musu,ya kuma sanar dasu an daura auren Wahid da Rufaida da azahar a babban masallacin Zariya, kowacce ta jinjina lamarin,
Ya sake cewa
"Har yau babu mai kawan abincin da ruwan"
Hajiya Kubra ce ta mike ta kawo masa abincin da ruwan kadan yaci ya aje yakallesu yace
"Kayan lefe suna gidan ,Baba Ashiru kuje ku dauka akai musu,nayi wa Wahid magana asabar zaizo ya dauki matarsa kayan dakin kuma acan za'a siya ayi komai"
"To Allah ya sanya Alkhairi", suka fada badan sukansu sunji dadin wannan auren ba,da wadannan tunanukan suka shiga ciki su kara shiryawa busu jimaba suka fito suka yi ma Abba bukar sallama da har lokacin yana falo yana yiwa Ubaidullah wasa da shi baya bukatar a kara shiryasa Aunty Amarya ta daukesa suka fita a motar Hajiya Kubra suka fita taja su zuwa gidan Baba Ashiru

Kaya kam sunyi kyau da tsari kala arba'in ne akwati 6 su Momy Maryam busu kushe kayan ba sai dai auren ne basa so ko daya da su Aunty Samina suka fada musu abinda ya faru da Aunty Samira taji su Rufaida suna tattauna maganar da Harira, sun bawa masu kawo kayan tukwici mai yawa daganan masu kawo kayan suka tafi da tarin kayan soye soyen da aka hada su dashi da lemuka da Abdul ya siyo musu aka basu.*JININMU 'DAYA*

By Sadiya Khalil

41.

yanzu Gwaggo Lariya inaji ina gani 'dana ya zai auri irin tsiya"
Hajiya Jamila tayi maganar bayan cire hannunta daga abincin da Gwaggo Lariya ta kawo mata.
Gwaggo Lariya ta kalleta tare da cewa
"Eh to muddin ki ka zauna ba,amma da zaki tashi ki rabawa malamai kudi sai kiga aiki,tunda dai bakyason auren"
Hajiya Jamila tayi murmushi tare da cewa
"Lariya ke nan kina tunanin kan auran nan nawa ne ban kashe ba,da naji shiru na dauka asirin nawa ya fara aiki amma ashe lamfa lamfa aka yi min"
"Gaskiya kuwa dan nima abin ya bani mamaki danaji kai kayan shiyasa na fara shakku akan saninki dan nasan vazaki yarda ba,dan koni ma vazan yarda inaji ina gani surajo ya auri Rufaida ba bare kuma ke"
Gwaggo Lariya tayi maganar dan ta sake tunzura Hajiya Jamila
Hajiya Jamila tace
"Wallahi kuwa Lariya munafuntata sukayi,yanzu nama rasa mafita dan a dazu so nai nakashe banza"
Gwaggo Lariya ta jinjina kai daga bisa ni tace
"Yanzu dai tunda har yau ba'a daura auran ba yanzu zan hadaki da wata aminiyata tana da shige shigen malamai,nima tana yi min tayin naje nace mata bani da kudin biyen malamai"
Hajiya Jamila cikin murna da doki tace
"Yaushe zamu je gidan nata,kinga gobe zan tafi Nasarawa da sassafe"
Gwaggo Lariya ta nisa tace
"Ki bari anjima baban Surajo idan ya dawo saina tanbayesa muje gidan nata"
Da haka suka cigaba da fira kafin wayar Gwaggo Lariya tayi kara wayar dake gefenta tasa hannu ta 'dauka ganin mai kiran nata Gwaggo Hajiya yayarta yasata saurin 'dagawa da sallamarta Gwaggo Hajiyar ta amsa saida suka gaisa Gwaggo Hajiyar take cewa"
"Ki kira mijinki ki fa'da masa zaki gidan Yaya Ashiru,anjima zamu hadu gurin daurin auren nan Rufaida da Wahid,kuma za'a kai lefe
Gwaggo Lariya tayi saurin cewa
" Yaya Hajiya ina ce sai wani satin aka ce"
"Eh da hakane amma matar Bukar 'dazu tazo 'dazu tayi wa mutane Hauka a gidan Yaya Zainabu,ta kusa kashe 'yar mutane aini bansan munafunki da ya kai mata zancen ba"
Gwaggo Lariya ta shiga zaro ido jin zancen Gwaggo Hajiyar harda kiranta munafuka to da tasan itace ta fadi hakan fiye da munafuka fadamata Gwaggo Hajiyar zata yi,da haka dai sukayi sallama da cewar sai tazo
Daidaita nutsuwarta tayi bayan katse wayar dan kada Hajiya Jamila ta fahimta da take can daddana wayarta jin Gwaggo Lariya ta gama wayar yasa Hajiya Jamila dago kanta ta kalleta da cewa
"Naji kamar unguwa zaki fita"
Gwaggo Lariya da sauri tace
"Eh wallahi zanje gidan Yaya Hajiya,zamu tafi wata unguwa,amma ba zamu Dade ba zamu dawo yanzu yaro zanyi kira yaje wajen aikin su Baban Surajo ya fada masa",dan tasan muddin ta kuskura bata jeba zarginta za'ayi harda hadin bakinta Hajiya Jamila ta san zancen tunda itama kiri kiri take nuna kiyayyar su Rufaidan,da haka ta mike ta fita daga dakin zuwa wani ba jimawa ta fito kasancewar batada karamin da yanzu haka cikin adonta na kure adaka ta fito ta dawo dakin da tabar Hajiya Jamila data sameta tana waya wayarta ta dauka tana cewa Hajiya Jamila saita dawo ta fice Hajiya Jamila data bita da kallo a ranta tana ayyana tabbas babban abu ake tunda taga Gwaggo Lariya ta caba wannan adon baki ta tabe ta cigaba da wayar da take saida ta gama ta lalubi lambar AbdulWahid amma a kasheta ta sameta dan haka yasa ta hakura da kiran dan tuntuni take kira suna sanarmata akashe wayar take.

******
ABDULWAHID
Da farin cikinsa ya kasa boyuwa da albishirin da mahaifinsa ya tare sa dashi dan tun yana Abujar yaso sanar masa to sai ga matsalar Network baya samunsa a waya koda ya daga wayar ta katse ga wadannan kwanakin aiyuka sunsha kan AbdulWahid din kwana biyu

Saida aka shiryawa Rufaida gidanta sosai da kayanta masu tsada da Abba Bukar duk shi yayi komai sannan AbdulWahid ya dauki matarsa Rufaida suka tafi tare da wasu daga cikin "yan uwan Rufaidan su Aunty Samina da har kwanakin suna Zaria da zasu ganin gidan Rufaidan Ummi Hauwa'u da ba yadda ta iya ta hakura da irin auren da aka yi wa 'yarta da Gwaggo ta dinga yi mata ban baki kafin ta hakura
*****
Gwaggo lariya ta maida dubenta ga Hajiya Jamila
" Jamila kiyi hakuri an riga da an 'daura auren,Rufaida da Wahid sai dai mu sauya shiri,fitar da nayi 'dazu najiyo labari gurin Yaya Hajiya"
Wani kallo Hajiya Jamila ta yiwa lariya kafin tace
"Lariya wannan wanne irin magana kike min ta rainin hankali aure kuma aka daura kuma kicemin baki sani ba aiko a garin mahauta muke bazan yadda ba kikasan maganar kai lefe bare ta aure, ai a dazu na fahimci fitar tafiya kai lefe kikayi ashe ni zaki munafunta nufinki ban fahimci wayar da kikai bane"Hajiya Jamila ba tare da ta jira abinda Gwaggo Lariya ke fada ba ta zari hijabinta da makullanta ta fice tana kokarin ficewa daga gidan gaba daya da har zaure Gwaggo Lariya ta karaso tana bawa Hajiya Jamila baki amma taki koda sauraronta motarta da take kofar gidan ta shiga ta yiwa key tabar gidan ta nufi gidan wata aminiyarta da zata yi kwana daya a gidan daganan ta nufi gidansu nasarawa a ranta tana jinjina halin dangin miji
Chapter 39 · 0% Book details