← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 57

Sashe 8

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Samiha data sauke wayar jin Rufaida ta yanke,yasata kurawa wayar ido,tana tunanin mai ake da wacce rayuwar ta baya banda kaddarori mai zaisa ta baro aminiyartata da aka shiga hakkinta gurin lalatamata mafarkinta,kuma akaki sanar da ita dalili dukda batasaniba amma akaran kanta tasan har ya'u akwai tabo a zuciyarta,an zalinci wancen ran,sai dai a yanzu fatanta inganta rayuwar amintacciyarta ta,mai dunbin muhimmanci a rayuwarta tundaga kuruciya har kawo yanzu dukda nisan zangon da sukayi da juna bawai mota ba a'a nisan har tafiya banbancin kasa dake tsakaninsu,Rufaida dataci sunan Rufaida ta fado dakin da take tafa'da jikinta tana cewa Mom Dadynmu yadawo"cikin harshen nasara take maganar dashi suka fi iyawa a yanzu haka,Murmushi Samiha tayi tace to sannunsa da dawowa,Ina Little din"yarinyar ta dan ta'be baki tace yana hannu Dady ni yaqi daukata murmushi Samiha tayi tace mata banda abin Rufaida aike kin girma baki ganki kinkusa fina girma ba" Rufaida ta saki dariya tace Mom ashe nima Little ya kusa fara kirana Mom"tace "sosaima"tana dariya sallamar Ahmad ce ta katsemusu firar sannu da zuwa Samiha ta masa ya amsa da yawwa da murmushi fuskarsa ledar dake hannunsa ta ansa harzata shigar da ledar Kitchen yace tadawo ta zauna zama tayi tsakiyar yaran,da Little ya mika hannu ta daukesa murmushi Ahmad yayi yace" habawa yaro zaka nemi na daukekane nima naki"ya fada yana dungurekan Little yafara alamun kuka ganin haka Rufaida tasa dariya ganin hakan da little yayi 'yar uwarsa tana dariya shima yafara dariyar,suma su samihar dariya abin ya basu ,Ice cream din dake ledar Ahmad yace Samiha ta ciromusu susha ta dauko suka fara sha shida yaran da Samiha tace ita ta koshi,ganin haka yasa Ahmad barwa yaran susha Rufaida itake bawa Little a baki,Kallo Ahmad yabi Samiha dashi jin tace batasha ganin baigano komaiba yasa yace"Samiha maike damunki? kefa kikace da zantafi na tahomiki da Ice cream dinnan" Samiha tace "Eh nice" Ahmad yace "to fadamin maiyasa kikafasa sha" ta dan canza fuska alamun damuwa kafin tace" Dadyn little yanzu mukagama waya da Rufaida da alamu bayan rasuwar mijinta tana cikin damuwa"ya 'dan gyara zamanshi yace "Inajinki damuwa kamar tame"ta basa labarin wayarsu da Rufaida ta kara da cewa masa "nafahimci kamar takuramata ake gidan Abba Bukar" Ahmad da mamaki yace"dama bata Abuja"Samiha tace"Eh kasan Barrack ne gidan ba wanda ta sani sosai acan shiyasa Abba Bukar yace ta zauna harta gama takaba takoma gida"Ahmad yace to gidan iyayentafa ko 'yan uwansu na Zariyan,aita zauna a can badai gidan nasu AbdulAhad ba"Samiha tace"kamanta Abba Bukar yayan Abba ne saidai nikaina saida nayima Momy magana yaza'ayi abarta gidan surikai tayi takaba sai kace batada gidan uba koma gidan Gwaggo ai gwar a takoma Ahmad yace "to tunda duk gidane ai ba matsala kuma kwana nawane"Samiha tace "hakane" nan Samiha ta yanke shawarar turawa Rufaida ku'di ta account koda ka'danne dan itama basu gareta ba dan business din datake nema kudin ke shigo mata"dubu 20K ta turamata acewarta sunyima Rufaida ta wuce karfin kyautar 20k dubu ashirin a wajenta,amma dai tasan sun isheta wasu 'yan bukatun ,dan ita kanta Samiha tasan komai dangane da wannan gadaddar kiyayyar daga Hajiya Jamila,shiko Ahmad tausayin yarinya karama yake kai tsaye batada sa'a a rayuwarta ta 'bangarori da dama zaikirata ,shi kansa da basa tare gari daya abubuwa da dama yasani harma auren nata da AbdulAhad da wani abokinsa Habib yake basa da suke unguwa daya dasu AbdulAhad din"saidai yana mamaki da wuya ko ita Samiha Rufaida ta fadamata abinda akayi mata saita tutance yarinyace mara hayaniya,yana tuno wancen shekarun da yakeji kamar shine a cikin waccen rayuwar

Jin karar wani kiran yasa Rufaida yasata duba mai kiran dan tasan idan Samihace bazata dagaba dan tasan tanbayoyin da zata yi mata sunada yawa akan damuwarta itako batasan dagawa aminiyarta hankaki ganin Luba ce mai kiran yasa Rufaida da sauri daga kiran bayan yin sallama suka dan gaggaisa tana tanbayar Luba na tanbayar Rufaida kwana 2 matsalar caji tafadawa Luba Luba da tasan Zariya akwai wuta kawai jin Rufaida tayi dan tasan akwai dalili babba da ita kanta Luba a dan zaman da sukayi da Rufaida tasan zaman hakuri take da surikarta da yan uwan surikartata dukda ba labari take bata ba amma dai tana fahimtane kuma Abban Yusuf wato Kabir yana dan bata labari wani abun kila wayar suka anshemata duk Luba ke wannan tunanin lokaci guda haka dai suka cigaba da gaisawa har zuwa wani lokacin sukayi sallama,jin karar message suna wayar yasa suna gama wayar ta duba mumushi yayi ganin sakon kudin da Samiha ta turomatane ,Allah sarki Samiha Rufaida ta fada a fili tana gama dubawa ta yanke shawarar kiran Abdulmalik ya tawo mata da charger tunda da kudi a account dinta saitamasa transfer da yake tukinsa hankali kwance yaji karar motar ya tsayar ya duba mai kiran ganin Rufaida yasashi katse kiran yabi saida suka kara gaisawa ta fadamasa sakonta da to kawai yabi Rufaida a yakatse wayar yana fadamata tuki yake a ransa yana tunanin Rufaida tasan tanada bukatar wani abu amma bazata fadaba saidai tace a siyo ta bada kudin haba yayima Rufaida siyayya tabasa kudin ai badai shi Abdulmalik ya amsa ba,shi tunaninsa Rufaida tanada komai bakuma zata nema ba shiyasa bama ya siyamata,itako Rufaida tunaninta idan ta tanbayesu mutanen gidan wani abu kamar bata kyautaba ganin batasan aljihun kowannensuba,Kuma ita idanma ba dole ba batasan tayi tanbayar abata abata dukdai Jini daya suke.*JININMU 'DAYA*

Sadiya Ibrahim Khali
(Sadiya Khali)

8
Chapter 8 · 0% Book details