Sashe 11
Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajin da ya hargitse da surutu kasancewar babu malami 'daliban wasu duk suna saman benci kowa surutu yake maza da mata ko ina an hada group group Rufaida da Samiha da suka hada rukuni na musamman su da suke a gaban layi jin Sallamar Class masters su yasa kowacce daliba rugawa cikin kiftawar ido bencinansu dan sunsan halin Sir Nura wato class mastern su amsa masa sallamar sukayi ya shigo shida wani bakuwar fuska da zai kusa tsarar Sir Nuran ne kallo 'daya Sir Nuran yayi musu ya fahimci basuda gaskiya gashi nan sai kokawa suke gurin gyara zamansu a benci kuma sunayowa birandar ajujuwan sukafara jiyo surutu kuma yasan daliban ajin nasa ne dan yasan duk sunfi rashin ji saidai a ajin bazaice dukansu ba amma dai ana masa kuka da ajin koma malamai,Sir Nura ya 'dan hade rai yana amsa gaisuwar da daliban ke musu shida sabon malamin bayan sungama ya kalli duk daliban ajin kafin ya nunamusu mutumin da suke tare yace"Wannan sunansa AbdurRahman shi 'dalibine a jami'ar BUK yazo Teaching practice yana shekararsa ta Uku a matakin karatu Yana karantar Biology Education yanzu haka...."yana cikin maganar ya jiyo sautin muryar wasu daga cikin daliban tsayawa yayi da maganar yanasan jiyo muryar su waye Rufaida da 'kafa take ta'bo 'yan bayan layin nasu da sune suke surutun alamun suyi shiru amma babu wacce ta fahimta Sir Nura da yagane Su waye masu surutun da busu sam ma yayi shiru ba Sir Nuran hankalinsu nacen wajen hirarsu ya kira sunayensu "Hauwa'u Umar ,Nasiba Abubakar,Ku fito waje Ku fadamin mai kuke fa'de" Cikin rawar jikin suka fito su biyun suna ayyano hukuncin da Sir Nura zaimusu dan baida mutunci ko 'daya a gaban allo suka tsaya suna kukkushe fuska,Tsawa Sir Nura ya dakamasu yace"wato saboda kun raina malamanku ina magana kunayi ko? Kuma bako ma saikun nunamasa halayyarku, to kufadamana muda sauran 'yan aji mai kuke cewa"hakuri suka shiga basa shi kuma ya kafe akan sai sun fadamasa mai yake cewa"nan Nasiba tace Sir cewa nayi sabon malamin da aka kawomana Yana kama da Yayan Rufaida Aliyu Bukar shine Hauwa'u Umar tace itama taga kamar"tsaki yaja Sir Nura bayan ya gama ji yace"Nasiba wato rashin mutuncin naki haryakai ina aji na kawo sabon malami kintafi can yimin hirar kamarshi da wani kin dauke hankalin masu San gane inda maganartawa ta dosa,yanzu haka ma ba haka kikace ba?"Nasiba tace wallahi Sir haka nace,kuma Hauwa'u kawai na fadawa yan aji da sunajin diramar da ake wasu Allah ya kara sukewa Nasibar dan dama duk tafi 'yan ajin rashin kunya da raina malamai da kyar ma idan hakan tace ba fara sawa malamin sunan banzan da dalibai suke sawa malamansu ba to yau ta hadu da Sir Nura dan sunsan yau Allah ne kadai zai kawo silar kwatar Nasiba daga hannun Sir Nura dan bashida mutunci bazai rangwantamata ba Sir Nura yace "su fita waje su tsaya harya fito sukarbi hukuncinsu"karasa maganar yayi da cewa shine zai riqa daukarsu Biology da ayanxu basuda malamin ya tafi karo karatu Sir Nura ne ya fito daga ajin yabar AbdurRahman yana musu tanbayoyi don yaji daga ina zaifara kasancewar dalinan SS3suke sune masu fita a shekarar Sir Nura yana fitowa daga ajin Sir ya kali su Nasiba yace" sakarkaru kawai da bususan darajar malamansu ba bako ma yazo saikun nuna halinku na rashin mutunci tun ba'aje ko ina Ba"nuna Hauwa'u Umar yayi yace" wato kema ina ganinki mai mutunci ashe kinbi sahun wannan sakaryar kawartaki"Nasiba da ranta ya fara 'baci kan kawai tace Sir AbdurRahman yana kama da Yayan Rufaida za'abi a fara cin mutuncinta ita sai yau ta kara tabbatar da rashin mutuncinsa yakai haka ita dai ana cemata"Acid and Base baida mutunci,sunan da aka sa masa kenan saboda tsabar rashin mutuncinsa a makarantar juyar dakai Nasiba tayi tana harare harare ya dakawa Nasiba tsawa da cewa "juyo ki kalleni mara kunyar banza wadda bata da tarbiyya cikakka" AbdurRahman da ya fito daga ajin yace masa Dan Allah ka kyalesu haka daganan Sir Nura ya kyalesu yayi gaba AbduRahman ya dubi Nasiba yace "yanzu abinda kuke baidace ba malami yana magana kuna magana bazasu bari yakai sakon da yakesan isarwa ba yanzu girmankune ace anfito daku waje ana ci muku mutunci bayan kuma duk kune kuke jawa kanku baza kuyi abinda malamanku suka ce kuyi ba" Nasiba tace"Wallahi Sir ba karya muke ba kuna kama da yayan Rufaida A Bukar"AbdurRahman ya girgiza kai ganin su bama tunaninsu sunyi laifi ba yace" waye muke kamar ne " Nasiba tace"wallahi Sir wani yayan 'yar ajinmuce muce Rufaida A Bukar "AbdurRahman yace"a'ina yake fa"Hauwa'u cikin zumudi tace Rijiyar Zaki farko mun dauka ma zakace mana kai 'dan uwansa ne"AbdurRahman yace"Allah sarki a'a kawai kama ce kinsan Khalid Bashar Majiya?"suka cemasa"A'a Sir akwai dai wata 'yar ajinmu a unguwar da yake take kai 'dan sane?"AbdurRahman murmushi kawai yayi batare da ya basu amsa ba ya 'Dora da cewa "amma zanso na ganshi mai kama dani 'din na gani ko haka ne"su Hauwa'u ganin karsu kuresa yasa busuce ya amsa musu ba dole dan daganin AbdurRahman 'dan manyen mutane ne kuma ga sunan mai kudin da aka sanshi sosai tunda manyan kamfanunuwa garesa ya kuma ce ko sun sanshi da gani yanada alaka da Khalid Bashar Majiyan sunmafi tunanin 'dan sane suka ce"wallahi Sir kuna kama daga nesa ma kai kace shine nan makarantar ma ya gama"yace " ok" yasa kai yabi Sir Nura dan shi bai fiye san surutu ba kuma ganin Sir Nura su shiyake jira Sir Nura ya dubi AbdurRahman da suke tafiya yace masa" ai yarannan idan zaka kwana nasiha basaji ko 'daya sunfiso aci nutuncinsu"murmushi AbdurRahman yayi yace"wallahi Sir ni dasuka ce ina kama da wanine ya 'dauremin kai"Dariya Sir Nura yayi yace"lallai AbdurRahman bakasan halin yarannan ba karya cikinsu ba'a magana"suka bada hira yana basu labarin halayyar dalibai ,suko su Nasiba suna shigowa ajin aka fara kus kus ana maganarsu Nasiba ta haye saman bencinsu Rufaida Hauwa'u takoma bencinsu ta zauna Nasiba tace kewai Rufaida bakiga kamar wannan gayen da yayanki ba "Rufaida tace " keni fa bangani ba"Hauwa'u da take baya tace"ke Nasiba ki kyaleta mana kema kinsan Rufaida batasan abin arziki ba,amma yanzu waye zaiga wancen malamin meyema sunanshi kuma ace basa kama da AbdurRafi",Samiha da maganar take cinta ,dan tasan bazasuyi da Rufaida ba, Samiha tace"ke Hauwa jiddah Allah nima nagani ,shiru dai kawai nayi"Rufaida dai tana jin kaya kaya dinsu batace komai ba dukda itamadai taga 'yar kamarsu amma bawai kama suke maiyawa ba amma tasan inta tayasu har atashi ana abu daya fitowar break shine ya watsa group 'din da suka ha'da Samiha ganin anfito Break tace "malama ki fito mufita mai take gaskiya"Rufaida ta dan tabe baki tace" gaskiya yau bazan fita Break ba,ke maii nayi ne na take gaskiya"Samiha tace "hakanan kiri -kiri kince mana sabon malamin nan baya kama da Yaya AbdurRafi bayan nasan karya kike"Rufaida tace" ai nasan halinku da cewa nayi suna kamar da tuni group din nan bai waste ba yanzu kuwa gashi bakowa amma aini ma naga kamar"Samiha tayi tsaki tayiwa Rufaida tace mata kuma"yar rain in hankali kawai,Samiha ta 'Dora da cewa"keni ban shakamiki labari ba"Rufaida ta maida hankalinta ga Samiha tace"shakamin naji kawata"Samiha tace"keni nafasa ma"Rufaida tace "haba Hassanata shakamin dan Allah naji" Samiha tace"ke wani gaye muka ha'du dashi jiya ke kinganshi kuwa kyakkyawa kalar namijin da nakeson aure dogo kyakkyawa"tsaki Rufaida tayi tana dokin jin labari amma Samihan ta tsaya shirmen banza tace"ni fadamin a'ina kuka ha'du yimin bayani naji kinki yimin bayani yadda zan gane "Samiha tace " aike bakya cin ribar zance dama sai kin nuna kin gaji"Rufaida tace"naji dai nidai fa'damin" Samiha tace"na fito Momy ta aikeni gidan su Fahat Hassan na nan ajin"Rufaida tace"Eh naji dai na gane jeki zancenki"Samiha tace"gidan Aunty Ummi na bayani gidanmu a kofar gidan muka ha'du ya tsaidani da kamar bazan tsayaba sai naga baikamata na masa hakaba tunda naga Hanif din Aunty Ummi a hannunsa ,shine na tsaya,muka gaisa,Har yake shaidamin yana sona ganin bankulasa ba shine ya bini gidansu Fahat yacemin Auny Ummi cousin dinsa ce Baban Aunty Ummi da mamarshi wa da 'kanwa ne ,yace yana ganina a unguwar idan yazo yace har a gidan Auny Ummi ya taba ganina ni dake,danshi tunaninsa mu 'yan biyu ne ni dake amma zai shiga mota ya tayar zai fitamu shiyasa bamu gaisa ba dan alokacin mun shiga gidannevgaskiya gayen nan yayi a kasar waje UK yayi karatunsa yace min zaizo gidanmu yau idan ya shigo unguwar da wuri dan yace bays rabo da unguwar"Rufaida tayi murmushi tace "kai amma kawata na tayaki murna Allah ya tabbatar da akkhairi,saidai kibi a hankali karki cika nuna kinasansa ,kuma karki sakankance dashi sosai,ki rika abu da wayewarki" Samiha tace "haka ne " year uwata amma duk ina kikasan wannan sirrikan soyayyar keda bakyayi?i"Rufaida tace"a gurin su Nasiba kinmanta natafi yajin aiki bencinki"Nasiba Shehu Abubakar India batun soyayyah ne ko a ajin azo gurinta yanzu haka ma bikinta za'ayi"Samiha tayi dariya danta tuna sun ta'ba wani fa'da da Rufaida tabar mata bencin Hauwa'u Umar ta koma Samiha tace "kai Rufaida aji tsoron Allah bakya mantuwa kinsan da yanzu ne bazanyi fa'da kan yoghurt ba" Rufaida tace"naga alama fa nidai na baki shawara kibi a hankali ki tsare mutuncinki a gurinshi karki cika nunamasa sosai"Samiha tace"to shikenan kawata,Amma nifa koshi zan aura tare za'ayi bikinmu nidake banaso nayi aure nabark"Dariya maganar taba Rufaida ma tace"banda abin Samiha ai da Allah nima yakawomin kusan hadawa ma za'ayi,yanzu dai Da yaya Saudat za'a ha'daku tsaki Samiha tayi tace "kewai Yaya Saudat zan zauna jira inama saurayin nata ya ta'ba zuwa gidan mu kurum daga haduwa a bikinsu Yaya Samina tace lallai shi take so,ke kin ganshi kuwa kato dashi da gani ma ya fara tsufa" Rufaida tace"kai Samiha banda sharri fa?"Samiha tace"Allah da gaske nake dandai bakije Sokoto bikinba da kinganshi kato tsawo da kiba"Rufaida tace"koma dai ya yake ita tanasan kayanta bare ma dai nasan bahaka bane"Samiha tace"au shigarwa Yaya Saudat yau kike kuma"murmushi Rufaida tayi tace"Eh mana"da haka dai suka kara taba hira har aka dawo break da sabon malaminsu ya shigo Sir AbdurRahman ganin sabon zuwane yasa duk ajin akayi shiru sai yayi tanbaya idan sun sani su bashi amsa don basa so daga zuwan AbdurRahman ya fara fahimtar halinsu gasu Nasiba sun gwangwadamusu cewa shi 'dan babban gidane shiyasa suka fara ganin girmanshi dan Khalid Bashar Majiya ba laifi kam yayi suna a cikin garin Kano.