← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 57

Sashe 35

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ina Rufaidan ne yaran nan sai jiranta yake ta shanyasa banda da dare ne ai sai ya bushe"
Gwaggo tace
"Kwalliya ai take masa karya 'dauketa budurwar kauye yace ya fa....
Gwaggo da bata karasa maganar ba Rufaida ta karasa fitowa daga 'dakin da cikin shigar atamfa riga da siket da hijabinta iya gwiwa da hasken lantarki ya sa Gwaggon hangota daga inda suke zaune itada Malam suna fira
Inda suke ta 'karaso tana cewa
" kai Gwaggo mai naji kina cewa,Yaya Wahid 'din zan tsaya yi ma kwalliya,kamar bako"
Gwaggo tace
"Bama dole ba yarinya kar yace ya fasa, kuma ni da ku'di aka ha'dani bazan iya nemo wancen dan kasar turawan yaron ba "
Ba tare da Rufaida ta sake furta komai ba tabar wajen su Gwaggon da ko saita dawo bata tsaya ce musu ba dan an ta'bo mata abinda take kokarin mantasa a babin rayuwarta dukda tasan da kamar wuya kaunar Ra'uf daga jininta yake ba daga zuci ba,tasan zata iya auran wani amma kuma bazata iya manta Ra'uf ba dan ya zama kamar 'dan uwa a gareta take ji a ranta
Tana jiyo maganar Malam da yake cewa
"Haba Zainabu ke maiyasa kika fiye kato 'barar zance kamar yarinya tunda batun yaron nan ya riga da ya wuce"
Ba tare da taji mai Gwaggon zata ce ba ta karasa zauren gidan da haske ya gauraye sa sallama ta masa da ta samesa tsaye cikin shigar wando da riga na yadi tazarce kayan isassu ya har'de hannunsa saman 'kirjinsa da ya soma yanke tsammanin fitowar Rufaida dukda bawai lokaci ne ya kure ba sai dai sanin wancen dalilin da yake tunanin zai iya hanata fitowa sai kuma yaga akasin tunaninsa aje wancen tunaninsa yayi ,ya amsa mata sallamar da tayi ya kuma kasa dauke kansa gareta harta karasa shigowa cikin zauren nesa dashi sosai ta tsaya
Murmusawa Wahid yayi kafin yace "barka da fitowa Matata Insha Allah"
Cikin zaro ido Rufaida ta 'dan kallesa lokaci guda da ta maida kanta 'kasa
"Eh mana bikisan ansa ranar bikin mu ba"
Cewar AbdulWahid da yaga kallon da Rufaida tayi masa alamun kamar bata yarda ba.
"Ina yini" Rufaida tayi maganar tana son a bar waccen firar haka
"Lafiya Kalau,amma ya kika canza mana fira,amma dai na kyaleki ko tanbayi Gwaggo idan kin koma ciki"
"To" kawai tace kafin Wahid ya maida dubensa ga Rufaida sosai
"Rufaida ina sanki tun kafin nayi girman da zan fahimci menene so da kauna nayi tunanin so ne irin na 'yan uwa na jini sai a karshe na fahimci bawai hakan bane,tun tuni naso furta miki sai dai fargabata Umma ya zata dauki lamarinki zata amince dake kuwa,ganin shurun zai soma cutar dani yasani sanar da Abba da ya amshi zancen hannu biyu harma yace naje na nemi soyayyarki indai kin amince shikenan shima ya amince,a lokacin da nazo sanar miki a waccen ranar na tarar wani ashe ya rigani furtawa nayi kukan zuci a wannan ranar karshe dai na hakura na barwa Allah lamura na,saidai bawai bana kishinki ba a lokacin amma hakanan a waccen ranar na yava da zabinki tundaga kallo daya dana masa tabbas nasan idan kika kasance matarsa da inada yakini da kin kasance cikin farin ciki saboda naga alamun kaunarsa a fuskarsa fiye da yadda ni nake kaunarki saboda in 'din mai raunin zuci tamkar wata macen i,hakanan naji a raina,sai dai kuma bansan yadda gobe zatayi ba,wanda zan iya hakurta ma raina ke indai yadawo zai aureki saboda inasan farin cikin kanwata matuka ko ya kikace ya karasa zancen yana sake duben Rufaida
Murmushi tayi masa tana son Wahid fiye da son da take tunanin tana masa a baya kasancewarsa dan uwan nata halayoyinsa masu kyaune bayida son kansa sa'banin sauran ahalinta,shi mutum ne mai tsage gaskiya a duk wani hukuncin da zai yanke tuni batun yau ba,tasan tana san shi amma zulliminta 'daya ummansa wannan mataki zata dauka akanta matukar ta aurar mata 'da
Jin shirun ya soma yawa yasa AbdulWahid magana
"Ya kikayi shiru kin barni na gama zuba zance"
Maganarsa ta maidota daga tunanin da take yi
"To Yaya Wahid mai zance"
Murmushi ya dan sake yi
"Au baki san mai zaki ceba,to yardarki nake bukata kin amince dani"
Yakarasa maganar yana nuna kansa
Bata da wani zabin daya wuce ta amince don tasan da yardarta ko babu aure dai sai an'daura ita da AbdulWahid indai suna raye tunda iyaye sun shiga lamarin auren,bare itama dai bazata ce bata sansa ba dama dai zulliminta guda mahaifiyarsu wahid Hajiya Jamila hakan yasa ta 'daga masa kai
Yayi murmushin jin da'di
"ina godiya kanwata Allah ya bani ikon riqeqi da amana"
A iya fatar bakinta tace Amin ba tare da ta furta ba
Ya sake cigaba da magana
"Nasan yanzu dai zulliminki Umma ko ki kwantar da hankalinki yanzu Umma ta zubda makaman ya'kinta tabarwa Aunty Amarya da Mama Kubra"
Murmushi ta 'danyi ka'dan dan tasan AbdulWahid ya fa'di maganar dan yaji da'din bakinsa zatace banda haka inasu Mama Kubra suke da wani kata'bus a gidan da umarninta ake bi a gidan matukar Abba Bukar yasakai yabar gidan kuma a jiya fa tagama jin maganganun da tayi masa akanta,haka itama ta tabbatar da ta shiga dakinta gaida ita ,shima dai kokarin sa take gani da yau yazo gunta bayan mahaifiyarsa vatasanta bataso ya aureta akan wani shirmen zancen da take da tabbacin baida wata makama dan kawai kanin mijinka yayi aure saika dauki kiyayya ka dorawa matarsa ita ba kishiyar kiva bakomai ba.
"Kodai nayi laifi ne kinki sakin jiki muyi fira yau"
Maganarsa ta katse tunaninta
"Ko 'daya"
Agogon hannunsa ya duba ya 'dago da kansa ya dubeta
"To shikenan bari zanje gida ni naga lokaci ya fara ja tara tayi harma ta gota kuma gobe nakeson komawa abuja,zan kiraki zuwa anjima"
"To Allah ya kiyaye hanya" tayi maganar tana 'dago kanta daga kallon kasan da ta ke.
Cikin jin dadin addu'arta ya amsa da "Amin"
Da haka sukayi sallama ya tafi Rufaida jiki ba kwari ta koma cikin gidan
Da sallama ta shiga cikin gidan inda ta bar su Gwaggo anan ta same su.
Amsa mata suka yi
Gwaggo tana cewa "wannan zancen haka daga zuwa kodai korarsa kikai ne"
"Kai Gwaggo kona koresa ai kinsan bazai tafi ba,tunda gidansu ne"ta karasa maganar tana kokarin cire takalminta ta shige daki
Ganin hakan yasa malam gyaran murya
" Rufaida zonan"
Rufaida da taji maganar malam yasata maida takalminta ta karaso wajen da suke ta zauna
"Malam gani"
Sake gyaran murya yayi ya soma magana
"Rufaida dalilin kiran dana miki shine na sanar miki sa ranar bikinki da iyayenki sukayi sun yanke hukunci nanda wata guda za'ayi,dan Allah kar asami matsala daga gareki ki mika lamuranki ga Allah,Allah yasa hakan yafi zama alkhairi"
Gwaggo ta dan dubi Malam ta soma magana
"Malam yaushe akasa ranar bikin kuma banida wani labari a matsayinka na uba ga Hauwa'u hatta nima bansani ba,maisu Aliyu da Bukar yaran nan suka maida kansu ne,ace komai isu isu zasu rika yi
Malam ya murmusa yace
"na samu labarin gurin Ashiru to ni nafadamusu suyi komai saboda kinsan dazu na shiga Kaduna"
Rufaida da haka ta mike ta shige daki ta zauna gefen gado ta soma tunanuka mabanbanta a ranta ace har ayi maganar aurenta Malam mahaifin Umminta ba'a fadamasa ba hatta Gwaggo itama da take tasu basu fadamata koda a waya bane takanji labarin matsaloli a cikin Family amma bata ta'ba cin karo da irin nasu matsalolin ba a cikin wadanda takeji ba banda su Gwaggo ta haifi 'ya to da danginsu babu mai saurararsu da komai to yanzu ma gashi sunada 'yar ana kokarin yi musu yadda akaso da 'ya'yenta dukda suke jikokinsu ace hidimarsu ta soma tashi ba'a sakasu a ciki ba suda suke matsayin kakanninsu amma da rashin mutunci ne dangin Abbannasu da Umminsu sunfi kowa yi musu ,dan ba suda banbanci abinda yayi Abbansu shi yayi Ummin nasu duk dangi guda suke dan bata mantawa da Gwaggo da mahaifin Abbansu uwa daya uba daya suke sai dai ita Umminsu mujiya ce a cikin dangin nasu kodan ita ka'dai ce gurin iyayen nata abu saiya taso a danginsu aki fadamata sai Gwaggo taji ta fadamata idan kuwa taje a dinga jifanta da bakaken maganganu tun da suka fara tasowa suke fahimtar haka, suma yau su Gwaggo gashi a aurenta an nuna musu iko.
Ganin tunanin ba zai fishsheta ba yasata daukar wayarta ta 'dan nemo littafi ta karanta kota ji sauki a ranta

*TEAM OF RUFAIDA*
*TEAM OF ABDULRA'UF*
TEAM OF ABDULWAHID

Ko ya zata kasance dai muje zuwa😊😊😊..ku biyo ni🚶🏽‍♀️🚶🏽‍♀️

More comment's more typing
*JININMU 'DAYA*

BY SADIYA AL-KHALIL

38.
Chapter 35 · 0% Book details