← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 57

Sashe 43

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Komai ya sauyawa Ra'uf soyayyar Rufaida koda yaushe ita ke nuqurqusar zuciyarsa sai dai ganin bazai sameta ba yasa shi maida lamuransa kacokam ga ayyukansa yasa kwazo fiye da nada akan aikin nasa,A yanzu haka sunsha hidimar bikin abokinsa Shureim da matarsa Inteesar,da Ra'uf din ne silar auren shi ya shigar da Shureim gurin Inteesar,dan abaya da Ra'uf yaje gurinta kafin ya sanar da ita son da Shureim.ke mata tayi tunanin Ra'uf din ke sonta kamar yadda take sonsa sai taji zance yasha banban ganin bazata iya nunawa Ra'uf batason Shureim ba shi take so,don Ra'uf a matsayin yayanta ta daukesa saboda kawarta Safiyya yasata hakura dan Shureim tasan baida wata makusa,don fannin kyau da kudi Shureim yafi Ra'uf sosai

Bangaren Samiha kuwa suna london abinsu acan ta haifi 'yarta mace ,wanda taso kafin haihuwar su dawo gida saidai yanayin karatunsa bai kammala ba a lokacin,shi kuma bayason ta taho kaduna ita kadai ba tare da shiba dom yasan ba wata kulawa 'yan uwansa zasu bata ba tunda yasan a kaduna zata zauna,haka Ahmad din ya nuna bayason wani yazo,ranan suna yarinyar taci sunan Rufaida wanda Samiha ta bukaci Ahmad ya samata yako biye mata yasa mata,don ya fahimci bada wasa Samiha ta dauki Rufaida a zuciyarta ba hakama ya fahimta a bangaren Rufaidan ma haka ne,haka ya jinjina wannan soyayyar tasu sosai a ransa babu wani kusanci na kusa kona nesa tsakaninsu amma suke wannan zumuncin har takai ga sa wa 'ya sunan kawa lalle abun babba ne,koda Ahmad ya fadawa Ra'uf sunan Rufaida yarsa taci ba karamin dadi ya jiba don yakasa mantawa da Rufaida a zuciyarsa har zuwa lokacin ya kuma kasa kula wata ta zama makwafinta a zuciyarsa,takakka yayi ya tafi London daga Delhi shida Sophie da Husna da Husnan ta soma karatunta a Delhi,dukda da yace bazai samu zuwa ba amma jin sunan da Ahmad yasa wa 'yarsa ya sashi tafiya da kayan jaririya masu yawan gaske suka tafi da duk yawan wanda Ammi da Dady suka hada mata saida yakara wasu saboda murnan abinda yayi na saka sunan Rufaida da Ahmad yayi ji yake kamar don shi yasa sunan ga murnar karuwar da suka samu don Ahmad ya wuce amini a garesa, Ammi da ita a lokacin ta ma manta da sunan Rufaida yasa mata fahimci murnar Ra'uf ba,sai tunaninta ya bata saboda Ahmad ya haifi yarinya yake murna don kowa yasan yadda suke da Ahmad din shi yasa babu wanda yakawo komai,bayan shi kuwa murna biyu yake yi

RUFAIDA
Haka take cigaba da rayuwa da uwar mijinta da Rukayya abun babu dadi,kuma har lokacin Abba Bukar baisan wannan zancen ba,taje Kano tayi Kwana biyu da dakyar Wahid ya barta taje ganin tanada ciki a lokacin shi da kansa Wahid din ya kaita Kanon da shima zaije wata seminar kanon ,bakaramin murna daganinta suka yi ba,ganinta dauke da ciki da kuma ganin babu alamun damuwa a tare da ita don har kiba cikin yasata yasa hankalin Ummi Hauwa'u kwanciya , saida ta zaga gidajen kawayenta ta kuma je gidan Momy maryam tayi kwana daya sannan suka juyo
Murnar sawa Rufaida takwara sosai Wahid yayi da Ahmad yake sanar musu bayan dawowarsu Kano da kwana biyu bakaramin kudi Wahid ya tura ba a siyawa baby kayan sawa Rufaida kuwa ranar kwana tayi da farin ciki ta kuma karawa Samiha matsayi a zuciyarta sosai,hakama a bangaren su Ummi Hauwa'u da Momy Maryam sun sallama irin kaunar dake tsakanin Samiha da Rufaida sai da jikin Rufaida yayi wata takwas Abba Bukar yaji labarin zaman da Hajiya Jamila da Rukayya keyi a gidan Wahid da AbdulMalik ya sanar masa da yaje wani aiki abujar yaje gidan,dukda Abba Bukar bayason dawo da Hajiya Jamila don bakaramin dadin zamansa da sauran matansa yake ba tare da Hajiya Jamila ba dama itace damuwarsa,badan yaso ba ya maido da ita ya kuma maida Rukayya nasarawa,saboda yana bukatar zaman lafiyar su Wahid da Rufaida

SadiyaIbrahimKhalil❤️
*JININMU 'DAYA*
BY Sadiya Khalil

44

*Duk abinda ka rubuta baya gogewa a littafinka koda kai ka goge shi a zahiri*

RUFAIDA
Bugun wayarta da take ji yasata katse aikin da take na shirya kayanta a drower da take da tsohon cikinta a lokacin ta mika hannu gefen gado ta dauki wayar ganin Samiha ce akan layin yasata saurin dauka da Sallamarta tasa wayar a handsfree ta cigaba da aikin da take ta soma da cewa Samihab
"Mai jego ina 'diya ta,takwarata"
Samiha da take riqe da Rufaida karama a hannu ta kurawa Rufaidan ido tanaji kamar Rufaida Aminiyarta take kallo ido ta lumshe ta bude kafin ta soma magana
"Wato babu wata gaisuwa tsakaninmu ko,bare tanbayar lafiya ta sai tanbayar 'yarki ko?saboda takwararki ce,shiyasa Ahmad yace karna sakawa 'yata sunanki,saboda yasan yadani zakiyi soyayyar da mukewa junanmu ta koma ke Rufaida zaki riqa yiwa"
Dariya maganar Samiha ta bata don bata tunanin akwai mahalukin da zai canza soyayyar dake tsakaninta da Rufaida
"Au dariya ma kike"Samiha ta fada da ta jiyo dariyar a cikin wayarta
Rufaida tace"yi hakuri yar uwata amma wallahi soyayyar da nake miki a jinina take,soyayyar da zanwa Rufaida duk saboda ke zan mata,badan kinmin takwara ba
Samiha tace "to naji nima wasa nake miki,ai idan kikaso Rufaida tamkar ni kikaso ne,fatana na rayu da ita domin koda muna nesa da juna dana kalleta na tuno dake"
"Hmm to naji 'yar uwata ina godiya da kaunar da kikemin fatana na wanzu gurin yi miki,koda bakya raye zan kula da duk abinda kika mallaka fiye da yadda zan kula da nawa"
Rufaida tayi wannan maganar
Samiha tace" haba 'yar uwata babu godiya tsakaninmu,ya Yaya Ahmad da baby na Allah dai yasa ki haifi namiji Rufy tayi miji"
Dariya maganar taba Rufaida tace
"To shikenan,Yana lafiya yana gurin aiki amma nasan yana hanyar dawowa ma baby kuma yana gaisheki,amma ni baby na ba zata auri kaninta ba gaskiya ki bari dai shi sai ki haifar masa mata nan gaba"
Murmushi Samiha tayi tace
"Aiko ni babyn cikinki na yiwa mata tun kafin yazo duniya,don haka babu fashi, indai namiji kika haifa shine mijin Rufaida,kuma tsiran nasu ba zai kasance mai yawa ba"
Rufaida tace
"To shikenan wai ma dakata ina Yaya Ahmad din ne"
Samiha tace
"Hmm ya tafi raka Yaya Ra'uf da su Husna wani store,kinsan su Ra'uf din sunzo daga Delhi,dafa baiyi niyyar zuwa ba yanaji ansa wa baby sunanki yazo,wallahi banyi tunanin har yanzu kina zuciyar Ra'uf ba sai da yace zaizo da kuma ganin kayan da ya siyowa Baby gaskiya ya kashe kudi,Ahmad yace tunda yaki fidda mata tunda kuka rabu yanzu sai ya auri Rufaida karama"
Rufaida tayi murmushi kamar tana ganinta tace
"Allah sarki,nifa na dauka yayi auren ma,amma ai bazan ba 'yata tsoho ba"
Samiha tace
"Da yayi aida na sanar miki har yau baiyi ba tunda ya rasa ki ya fidda tsarin aure a ransa tunda idan an masa maganar auren sai yace ba yanzu ba,shi kwata kwata ba tsarin aure yanzu a tare da shi,da Ahmad yace masa ko dai saboda ya rasa ki ne shine yace ko daya yasan dai ya soki amma dai yanzu tunda kinyi aure shikenan,shi dama halayyarki ta rudesa yasa har yaji yanasan yayi aure a baya auren ma kuma ya aureki,tunda kuma iyayenku ke da shi suka nuna basaso ya hakura"
Rufaida da maganganun Samiha suke shigar mata zuciya sosai jin Samihan ta dakata da maganarta yasa tace"Kinga aiki nake yanzu zan kiraki anjima"
Ba tare da taji mai Samiha zata kara cewa ba ta katse wayar da suke,don baza ta iya jure a rinqa yi mata maganar tsohon saurayinta ba ana tuno mata baya ne da har yau takasa mantawa da ita bakin cikin rayuwarta har yau ya kasa gushewa bawai son Ra'uf take har lokacin ba don yanzu soyayyar ta ta Wahid ce ba ta saka kowa a zuciyarta da sunan so idan ba mijinta ba, sai dai takasa manta yadda suka rabu da iyayen Ra'uf da nata,don tanada yakinin da kalmar karuwa da wasu daga cikin dangin Umminsu ke kiran Ummin nasu dashi a kayi anfani gurin ruguza wancen maganar auren nata,aka hadata da Wahid saukinta guda mijinta na kaunarta,matsalarta a gurin wasu daga cikin 'yan uwansu take da kuma surikarta sa'arta guda ce tayi nisa dasu sai dai duk ranar da suka zo habaici kam ta bani da shi samun daukinta kadai su tafi gida
Samiha da take ta magana a wayar jin bata ba ta amsa ba yasa ta duba taga ta katse kiran murmushi tayi ta aje wayar itama tana nazarin dalilin saurin CE mata zasuyi waya anjimar da tayi bakomai bane illa maganar Ra'uf da tayi mata tunda akayi haka ta fahimci Rufaida batasan a yi mata maganar Ra'uf din kwata,koda yake tasan halin Rufaida tun suna 'yam mata bata damu da maganar namiji ba,kota Yaya Abdul ne da Yaya Samir ma ba'ayi take ba su da suke matsayin 'yan uwanta,bare kuma ta saurayi gashi kuma yanzu tana da aure don haka itama Samiha ta dauki alwashin bazata kuma yiwa Rufaida maganar Ra'uf ba idan ba ita ta sako, bare kuma tasan za'a yara kafin tayi maganarsa
Chapter 43 · 0% Book details