← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 57

Sashe 32

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma Ammi Su Abba Suleh sun fa'damiki wani abu ne da yasa suka hanani auren ta

Kai ta girgiza tace "a'a ko 'daya ba su fa'da mana komai ba sunce dai an yi musu wula'kanci da ni narasa kalar wula'kancin amma hajiya ta 'dauki zafi da haka sosai sai dai kayi ha'kuri"

SADIYA KHALIL🖊️😊*❣️JININMU 'DAYA*❣️
BY SADIYA IBRAHIM KHALIL

HAPPY SALLAH ALL MUSLIM UMMAH ALLAH YA MAIMAITA MANA🤲🏼

34.
34
*Rufaida muddin kikace bazaki bi Abba Bukar ba kinada tabbacin ni zaki jawa zagi bakowa ba,haka koda Aliyu bai kasance miji gareni ba duk abinda na mallaka suka nuna suna so nawa zan basu,saboda sun nunamin soyayya kamar wadanda muke ciki 'daya bare ke din mallakinsuce duk abinda suka yanke gareki bazance don meba"
"Rufaida da take zaune jikin mahaifiyarta saman gado da tagama jin kalaman Ummin nasu ta soma magana"
"Ummi naji zanbi Abba Bukar amma banason auren Yaya Ahad tunda sunqi aurena da Ra'uf naji na hakura amma wallahi banason auren nan Ummi ,nasan bazanyi auren farin ciki ba don Allah Ummi kice karsu auramin shi"tayi maganar tana fashewa da kuka
Lallashinta Ummi Hauwa'u ta fara da itama hawayen take zubarwa ita kanta batason 'yarta tayi rayuwa irin wadda tayi a baya,da tasan saboda Hajiya Jamila ne yasa batason auren na Ahad din badan tana kin Ahad dinba,saida Ummi Hauwa'u taji Rufaida tayi shiru ta soma magana
" Haba Rufaida ya kike abu kamar ba musulmaba bakida masaniyar ko Ahad shine zaifi zama miki Alkhairi a rayuwarki tanan gaba idan kina wannan maganar to kenan imaninki ya soma rauni kenan ko,kuma ki tuna da cewa duk Wanda Allah yaso da Alkhairi saikiga ya jarabceshi da wata musibar,idan bakiyi kokari kin cinye jarabawarki ba mai kikeso kiyi a duniya,ko kinfiso ke rayuwarki ta kasance kullum cikin jin dadi ki tuna da za'a tona zukatan wasu aji meke cikinsu da kinyiwa Allah godiya akan ke taki jarabawar,ki fahimci cewa Alkaluma sun riga da sun bushe babu wanda ya isa ya kauda kaddarorin rayuwarsa domin sun rubutu akan alkalamin da baya gogewa,kowa kika gani kafin ya samu abinda yakeso saida yasha wahala ,nasan kinason Ra'uf tuni batun yauba nasan da haka,amma hakuri zakiyi abubuwan da son zuciya ya zama silarsu ya farraqa soyayyarku,maza ki share hawayenki ki cigaba da kaiwa Allah kukanki.
"Dago ido Rufaida tayi tana share hawayen fuskarta ta ta jinjina lalle mahaifiyarta uwace mai girma a rayuwarsu lallai mahaifiyarta ta samu tarbiyya daga iyayenta gashi har tasamu nutsuwa da kalaman mahaifiyartata dole mahaifinta ya sota fiye da tunanin dukkan mai tunani da duk wanda ya tabata a dangi to sai Inda karfinsa ya kare dukda dangin nasu dayane,saidai abu daya daya shige mata duhu sanin waye 'Danbatta Family da zuriyarsu basa son haduwa da zuriyar Danbattan.
Murmushin karfin hali Rufaida ta qirqira ta dora ido ga mahaifiyartata
" Ummi na amince da dukkan maganganunki kuma na yarda da nasiharki gareni,kuma nayi alkawarun bin abinda kikace,saidai ki fadamin maiyasa don Ra'uf ya fito data zuriyar Danbatta bazaku auramin shi ba"
Murmushi Ummi Hauwa'u tayi ta dafa Rufaida
"Ni kaina bansan dalili ba mahaifinkine da Abba Bukar kawai suka sani amma ki dauka a ranki baki taba jin sunan 'Danbatta Family ba har abada,amma ni bance kimanta da masoyanki na gaskiya ba har karshen rayuwarki ba,kinga maza taso ki shirya kayanki mubar wannan maganar kinsan Abba Bukar bayasan jira.
Jiki ba kwari ta mike da tasan lallai akwai rina a kaba Ummince dai bazata Sanar mata ba itama kuma batasan tilastawa Ummin tasu
Da haka suka Shiga loda kayannata a trolley da Ummi Hauwa'u ke tayata sunayi tana sake yi mata nasiha
10pm
Motar Abba Bukar ta tashi da Rufaida take rungume da Umminsu da Rumaisa da take ji a ranta tamkar rabuwarsu kenan ,bazasu kara haduwa ba,shikansa Abdul kuka yake yanasan kanwarsa gashi an rabata da abinda take so za'a kaita inda ba'asonsu don zalinci ji yake aransa ina ma shi wani ne wallahi da bazata bisu ba hatta Umminsu da kannensa bazasu cigaba da zama a tare da Abbansu ba da sunaji suna gani ake fadawa mahaifiyarsu bakaken maganganu don kawai anga ita din mai hakuri ce.
Horn din da Abba Bukar yayi ne yasa Rufaida Shiga gaban motar ya tayar tana hange 'yan uwanta da Umminsu suna hawayen rabuwa da ita da dagamata hannu da hatta mahaifinsu ta hangi siririyar kwallar da dafito daga idanunsa Abdul Rashid daya bude musu gate din Hawayen yake da daga musu hannu har waje ya fito saida yaga baya hangen motarsu ya koma gida itama waigensa take har suna bacewa ganinta sunyi matukar sabo da da 'yan uwanta tare sukai rayuwa tun daga mara dadi har zuwa yanzu da suke ganiyar yin mai dadi da Umminsu take gine dasu ko yaushe akan nuna musu su kaunaci junansu tunanin baya kawai Rufaida ta lula tana hango komai kamar a mafarki.
2pm
Suka karaso Zariya da kai tsaye gidan Abba Bukar suka nufa inda yayi horn mai gadi ya bude musu gate din Abba Bukar ya dosa hancin motarsa cikin gidan mai gadi da take masa Sannu da zuwa ya dagawa hannu yayi parking inda aka tanada wajen aje motoci ya fito ba shiri Rufaida ta fito itama tana sake duban gidan da duk sanda ta shigo tarihin rayuwarsu a gidan yake zuwar mata kamar yanzu abin me faruwa tsoro da fargaba ya shiga yawo a cikin zuciyarta to yau karo na biyu da tazo gidan da zama wacce irin rayuwa zatayi kafin lokacin bikin nasu da Ahad yazo tasani ta bayance dai rayuwartasu zatayi koma ta linka ta bayan tunda kaddara tasa zata auri dan matarda take da cikakken iko da isa a gidan na Wan mahaifinnata.
Maganar Abba Bukar yasata dawowa daga dogon tunaninta inda yace
"Shiga cikin gidan kafin Dan-liti (mai gadi)ya shigo miki da kayan naki"
Da to ta bisa dan ta fara tafiya cikin sanyi ta is a kofar falon bata sami kowa a falonba dalilin daya sata jin dadi kenan harta isa kofar da zata sadata da bangaren da shine nasu dasuka zauna a gidan da har yanzu yake nasu da idan sunzo gidan shine gurin zamansu
A share bangaren yake kai kace wani na zama a cikinsa.
Sallamar Baba Dan-liti da Abba Bukar yayi masa izinin shiga ya kaiwa Rufaida kayanta yasashi shiga,don iyakacin aikinsa gate.
Amsa masa Rufaidan tayi ta gaishesa ya amsa ya aje mata kayan a falon ya fito.
Jakar dake zagale a kafadarta ta aje saman kujera tareda cire hijabin jikinta ta zauna tana maida gajiya tana mai cigaba da tunanin rayuwa ganin tunanin bazai mata ba yasa ta mike tayo alwala ta tada sallah ta dade tana addu'o'i kafin ta mike tabar dakin da nufar dakin matan gidan gaishesu
"Wawa sakarai dama don haka kace bakasan Rukayya don kawai kanason macen da banbanci dake tsakaninku mai girman da bansan adadinsa ba ne, Rufaida da take kokarin tura kofar dakin Hajiya Jamila tajiyo furucin nata da dama tasan fiye da haka saita faru bama ga Ahad dinba har gareta tunda zai aureta,gudun hakan yasa take tsoron auren Ra'uf dukda bawai sonsane itama batayi ba saidai wannan matsalar take hangowa,da ita kullum tunaninta sanin banbancin dake tsakaninsu dasu Ahad da har yau takasa fahimtar menene banbancin jin furucin Ahad ya katse mata tunaninta"
"Umma inasan Rufaida tunda tazo duniya banasan Rukayya da soyayyar aure, amma kifadamin banbancin mu ko zaisa ya zama silar hakurata da auren Rufaidan amma ni nasan Rufaida 'yace kamar kowa,bana haufi akan bazata cutar dani ba har ma daku"
"Dakata Malam ai banbancinku sananne ne da kowa ma ya sanshi sakarci da wauta ne yasa kaika manta dashi kuma tunda ka kafe sai ka aureni Rufaida to nima zan kafe a au.....
Bata tsaya jin karashen maganar Hajiya Jamilarba tabar kofar dakin nata tana kokarin hana hawayen idanunta fitowa,
Hajiya Jamila mutuniyar garin Nasarawa state ce acan Abba Bukar da yaje bautar kasarsa ya ganta ya Aurota acan
yaranta biyar Abdul-Ahad ne babba a gidanma gaba daya sai,AbdulMalik,Abdul-Jabbar,AbdusSalam,Wasila
Kai tsaye dakin Hajiya Kubra ta shiga cikin sakin fuska suka gaisa ta zubo mata abinci taci tana sake nusar da Rufaida yanayin rayuwa Hajiya Kubra mutuniyar kirkice auren zumunci sukayi da Abba Bukar 'yar cikin garin zariyace, kuma aurenso da kauna da ba hadasu akaiba Allah ne ya hadasu da take mutuwar son Abba Bukar dalilin dayasa takesan kowa nasa kenan dukda itada Abba Bukar din abu dayane,amma sonsa ne yake tasiri a zuciyarta dayake kara mata kaunar 'yan uwansa dukda itama din nata ne,amma bata banbanta wadannan sunfi kusanci gareta indai akan abinda ya shafi mai gidan nata ne
yaran Hajiya Kubra a lokacin Hassan,Hussaini,Aliyu,Umar,Usman.
cikin kwarin gwiwa Rufaida ta fito ta shiga 'dakin Aunty Amina suka gaisa da itama macace mai kirki saidai batada yawan surutu amma dai tanada kirki batada yawan magana bare harta fadawa 'yan uwan Abba Bukar din wata magana mara dadi rashin maganarta ne yasa wasu ke ganin batada kirki amma shi Abba Bukar sam baya ganin haka don ta fadamasa laifin da nasa suka mata to lallai za'a dade yaranta biyu a lokacin don itace amarya
Sadiq,Ubaidullah da take goyo
Tana fitowa ta shiga dakin Hajiya Jamila da ko sallamar da tayi bata amsa ba haka ma gaisuwarta haka ta gama zama ta fito da Hajiya Jamila ta biyo ta dajan tsaki.*❣️JININMU 'DAYA❣️*
BY SADIYA IBRAHIM KHALIL

*HAPPY SALLAH ALLAH YA MAIMAITAMANA AMIN*
Chapter 32 · 0% Book details