← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 57

Sashe 44

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wahid da yake tsaye jikin kofar dakin Rufaida da hankalinta nakan wayar da take da Samiha batasan ma ya shigo ba yana kallon yadda yanayin matarsa ya koma bayan ta kammala wayar murmushi yayi ya karaso inda take ya karbe kayan da take kokarin sakawa cikin drower ya riqe hannunta ya zauna gefenta kallon mamaki ta bisa dashi don batasan ya dawo ba, fuskarta ya kalla yace
"Waye ya batamin ran mata ta"
Sai a yanzu ta iya magana tayi saurin cewa
"Babu kowa,mai ka gani"
Ya danyi murmushi tukun yace
"Ban yadda ba Samiha ta bata ranki saboda tayi miki maganar Ra'uf ko saboda kinason ki manta shi a yanzu haka"
Ido ta zaro tace
"Yaya waye ya fadama munyi maganar Ra'uf da Samiha?"
Ya danyi murmushi yace
"Nina jiyewa kunnena babu wanda ya fadamin,na dade tsaye anan,ina jin duk wayarku da Samiha,Rufaida a kullum ina godiya ga Allah dana samu mace ta gari kamarki"
"Hmm Yaya kenan maiyasa kace haka"
Rufaida tayi wannan maganar"
Ya dan kalleta yace
"Saboda kin hakura da zabina da Allah yayi miki wato ni baki kasance mai bibiyar tsohon saurayin da kaunarsa nasan ita ta fara linkaya a ruhinki,gashi sai kikayi rashin sa'ar mijinki bai iya soyayya ba,bare lokaci guda ya fitar miki da son Ra'uf a ranki,amma ke din sai kika bada gudunmawar hakan,kinga dole nace nasamu mace ta gari"
Murmushi tayi tace
"Shikenan ya isa haka mu manta da baya mu tunkari gaba"
Yayi saurin ce mata
"Hakane mata ta,yanzu mai kika tanadarmin yaufa yunwa nakeji sosai,Kabir ya cinye abincin da kika kawomin office"
Ta dan yi masa hararar wasa tace
"Duka fa abincin na zubo muku dana girka azo muje dai kitchen kayi girkinka dai,wai shi Yaya Kabir Luba bata iya girki bane?"
Yace"Am sorry my wife ki girkamin ko indomie ne,kinsan dai Kabir bayan abincin matarsa bayason cin na kowa saike,Kabir yace abincinki dadinsa daya dana matar Uncle dinsa da take porthacourt,yace gani yake idan yaci abincinki kamar nata yaci"
Murmushi Rufaida tayi tace
"Kasan dai halin Yaya Kabir kila ma ba haka bane,nidai muje na tayaka kazo nima ka karasa shiryamin kayana"
Wahid ya kalleta bayan ta mike yace
"Nufinki dai abokina karya garesa ko,ba ruwa na keda luba wallahi,dama yace min yau zata zo, kinga saina fadamata"
Zama tayi kokarin yi tare da cewa
"OK jeka ka fadamata ni kuma naki tayaka girkin"
Wahid da yake kokarin fita yace
"Sorry,my wife,wasa nake miki"
Da haka ta mike tabi bayansa zuwa kitchen

*Bayan wata biyu*

A wannan lokacin abubuwa da dama sun faru na farin ciki da akasinsa abun farin cikin harda haihuwar Rufaida ta haifi yaronta kyakkyawa da yaci suna Yasir da yake kama da mahaifansa,Samiha da aka tura mata hoton yaron ba karamin farin ciki tayi ba,kamar ita aka yiwa haihuwar ta kuma turo masa da kaya masu kyau da tsada ba karamin soyayya ake nunawa yaron ba,a gidansu ta haifesa Kano da taje goyon ciki har saida akayi arba'in ta dawo wannan zuwan bakaramin farin ciki Ummi Hauwa'u tayi ba na zuwan 'yarta ta koba komai ta rage jin bacin ran irin auren da akayiwa Rufaidan,ta kuma dora so akan Yasir,da itama Ummi Hauwa'u ta kara wata haihuwar ta haifi 'yarta mace mai suna Amina suna ce mata Rahima a lokacin akayi bikin Nasiba shehu kawa ga Rufaida da duk ta hadu da class mate dinsu da hakan ya tuna musu da rayuwar makaranta Samiha ce kadai bata samu zuwa ba kasancewar Ahmad yace sai ya kammala karatunsa zasu dawo tare,duk yadda taso zuwa haka ta hakura Abdul-Rahman ma yazo bikin dukda baya kasar yana Cyprus saida yazo daurin auren Aisha kasancewar ita ce ta hannun damarsa,haka nan ya dinga tsokanar Rufaida Yasir ya fi ta kyau,Hajiya Jamila badan taso ba tazo ganin da saboda matsawar da Abba Bukar yayi tazo ba tare da ta kawo ko tsinke ba,tana ganin Yasir kuma taji kiyayyarsa ta shiga ranta,da habaice habaice da bakaken maganganu ta baro Kano,wata 1 tayi cur a Kano daganan ta koma Abuja da Luba taje gidan ta gyara mata shi itama a lokacin ta haifi dan ta Yusuf a kwantagora da nanne garinsu Kabir din aiki shima ya maidoshi Abujar da yake matsayin Kwararren likita

Share plz kuma kuyi manage
*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Ibrahim Khalil
(Sadiya Khalil)

45.
Ayi manage please ba yawa

*Bayan shekara biyu*

Wahid ya dago jajayen idanunsa ya kalli Hajiya Jamila da take zaune saman kujera Wahid yana gefenta kan carpet zaune ya soma magana cikin raunin murya
"Mama nifa bana qi auren Ruqayya bane,illa ni dai kawai,bata daga cikin tsarin matan da na keso na aura"
Hajiya Jamila cikin zafin zuciya ta kalli Wahid ta soma magana
"Na fahimceka Wahid,'yar karuwa wadda banbancinku yafi gaban kwatance har ta fiye ma Ruqayya,to wannan karon muddin baka auri Ruqayya ba sai dai ka saki waccen yarinyar don ba zan bari irin karuwa ta cigaba da haifamin jikoki ba,dan shi kansa wancen 'dan ban yarda naka ne ba ne"
Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa yace
"Haba Umma mai yasa zaki ce haka,dan Allah Umma mu daina tuna baya mu tunkari gaba kawai...
Abba bukar da ya dade a tsaye a kofar dakin da yakejin duk abinda suke tattaunawa wanda babu wanda yaji motsinsa a cikinsu yace
"Barta ta tuna duk abinda ke ranta Wahid"
Muryar Abba Bukar din ce ta katse karashen maganar da yakeson yi
Abba Bukar din ya dora da cewa
"Jamila tunda har Wahid yace bazai auri Ruqayya ba da bakinsa to nima,bazan amince ba kai koda ma ya amince din,saboda koda ban hada iri da Rufaida ba wallahi ta fiye min ke da yan uwanki"
Wata shewa Hajiya Jamila tayi kafin tace
"Bari na tuna ma idan ka manta ni din da kake fadar hakan akaina ko makaho ya shinshina yasan cewa nafi wancan dan iskan kanin naka,wanda saboda abun kunya saurayin 'yar da iyayensa suka fasa,sai danni nawa 'dan ya taimaka musu zakayi min maganar banza,me ake da zuriya irin taku
Abba Bukar ya tunkaro Hajiya Jamila cikin zafin zuciya zai kai mata duka da take zaune kujera ba tare da tayi koda motsi ba Wahid ya mike ya rike hannun mahaifinnasa yana cewa
"Abba kayi hakuri"
Abba Bukar da idonsa ya soma ja yace
"Wahid yanzu ni Jamila ta ke fadawa wadannan maganganun,ita ta manta abunda ya faru da tata 'yar uwar ranar da ranar aurenta mijin ya fasa ta manta kuma abunda dan uwanta ya aikata da..."
Hajiya Jamila sai yanzu ta mike daga kujerar da take ta katse maganar Abba Bukar da cewa
"Bukar wallahi karka kusa,ka fadi wata magana akaina idan ba haka wallahi saikayi dana sani mara iyaka"
Cikin bacin rai ya kalli Hajiya Jamila yace
Wanne dana sani zanyi daya wuce ke wanda zakiyi"
Murmushi Hajiya Jamila tayi kafin tace
"Aini banida wani danasani,kune kukayi shi,tuntuni bama yanzu ba saboda kuskuren shigowar karuwa kazama cikin.....
Wahid ne ya yayi kokarin jan Abba Bukar ganin Ummantasu bazata fasa maganar da take,suka fito daga daki saida suka fito wahid ya dubi Abba Bukar yace
"Abba dan Allah kayi hakuri,da abinda Umma tayi yanzu"
Abba Bukar dafa kafadar Wahid yayi yace
"To ya zanyi Wahid kullum cikin hakuri nake yi,dawowar dana yi mata na dauka abun zaiyi sauki amma abun yafi nada ma,saboda don kawai na hadaka aure Rufaida"
Wahid cikin ba ya dubi ABBA Bukar yace
"amma Abba menene laifin Rufaida,bata aikata musu komai ba,haka ma ummansu Abba"
Abba Bukar yace
"To dama mai zata aikata musu Wahid kasan shi makiyi ba ya jira kayi masa laifi yake ba,yanzu ka wuce ku tafi karkuyi dare a hanya"
Jiki ba kwari su Wahid suka fito harabar gidan shida Abba Bukar gurin motarsu da Rufaida da sauran matan gidan suke jikin motar sun fito rakiyarsu
Haka suka shiga Wahid ya tada motar Rufaida ta shiga tare da Yasir da yayi girma ya fito a kyakkyawan Hausa Fulani da ya debi kamanni mahaifinsa sak
Har suka fara tafiya a motar babu wanda cikin Rufaida da Wahid sukayi wa juna magana saidai takan ji firarsu jefi jefi da Yasir don bataji akwai abinda zata iya cewa dashi shi din ma haka ne saboda bayason ta fahimci abinda ya faru shida mahaifiyar tasa a yanayin maganarsa ita dinma bata damu da hakan ba ta bude gidan gaba ta shiga jikinta babu kwari don tasan tabbas akwai abinda ya faru,a shigarsa sa dakin mahaifiyartasa,da niyyarsa tayi mata sallama sai kuma ga wadancen maganganun sun biyo baya
Chapter 44 · 0% Book details