← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 57

Sashe 2

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bugun Zuciyar Rufaida ne ya karu dole ta bar kitchen din taje falo ta kwanta hakanan yanzu take jin bugun zuciyar batasan daliliba anbatan Allah ta fara yi a cikin zuciyarta,wayarta ta lalubo ta danna tasa a kunne,a daya bangaren murmushi Ahad yayi ganin sunan mai kiran My wife ya daga ya gabatar da sallama ta amsa tana cewa Yaya Ya hanya yace Alhamdulillah nakusa zuwa Kaduna wayar ta ka tse tana masa addu'ar Allah ykiyaye hanya yayi murmushi yana kara jin kaunar matarsa a ransa da haka ya cigaba da tukinsa
Wahid bayan barinsa cikin Kaduna yana gaf da shiga Zariya,duk yadda yaso kaucewa motar sai da tazo ta bugi da motarsa nan motar tasa ta dinga mirginawa yanata salati motar man da tayi gefe ta kama da wuta abinka da cikin jama'a yasa dan dan nan gurin ya cika AbdulWahid ake kokarin ceto aka tsaida motar da ta fara shigewa rami kuma mai zurfi dakyar aka fiddoshi daga cikin motar jini yayi kaca kaca da jikinsa bazaka taba shaida cewa wannan fuskar AbdulWahid ne matashi mai kuruciya kyakkyawa lallai duniya ba abakin komai take ba,wayar dake cikin motar da duk ta ragargace police suka dauko suka aka saka sim din a wayar wani daga cikin yan sandan bayan anyi kokarin sasa a motar police din aka bar wasu suna bincika motar tasa nan aka fara kokarin kiran danginsa amma yawanci duk bata shiga ta Rufaida ce kawai ba'a kira ba
A abuja
Rufaida lafiyarki kalau kuwa kin kasa cin alalan nan kuma bayan nasan kinasan alala Luba ta fada tana dafata damai da fuskarta ga Rufaidan Rufaida tace wallahi Luba wayar Yaya Wahid nake takira naji ko yaje zariyan to da tana shiga baya dagawa yanzu kuma taki shiga gaba daya kuma nasan yaya Ahad baya kin daga wayar Luba tace ki sake kira kiji to yanzu,wayar Rufaidan ta dauka tasake kiran sa anan tayi sa'ata shiga daya daga cikin dan sandan da yake a farfajiyar General hospital na Zaria din ya dubi abokin aikinsa yace yallabai ana kira wancen mai hatsarin naga an rubuta My wife yace,daga kila matarsa ce tunda an kira iyayennasa basu daga ba da ya rubuta hakan da sallama dan sandan ya amsa wayar jin bashine ya amsa wayarba nan Rufaida bugun zuciyarta ya karu dan sandan yace wacece ke a gurinsa tace matarsa dan danan dan sandan ya katse wayar zuciyarsa a raunane domin bazai iya fadama Rufaidan halin da mijinta yake cikiba nan Luba ta kalli Rufaida tace ya akeyi Rufaida tace cikin karayar zuciya tace Luba bana tunanin Yaya lafiyarsa kalau kuwa nan ta labartawa Luba abinda ya faru a wayar da sukayi Luba tace bara na kira baba yusuf nafadamasa ki kwantar da hankalinki ita dai to tace kawai kira daya Luba tayiwa Kabir ya daga yace yana kofar shigowa falon bata aje wayarba ya shigo falon yana riqe da hannunsu Yusuf da Yasir gurin mamarsa ya nufa ya kwanta a cinyarta Rufaida batasan sanda hawaye ya zubo mata ba ta fashe da kuka tana shafa kan Yasir Kabir ya kalli Luba yace Wife mai aka yima Rufaidan ta dan dubesa tace Wallahi abokin nakane Baban Yasir ake ta kiransa yaqi dagawa karshe ma wanine ya daga Kabir yace haba to shine abin kukan bari na kirasa naji yanzu namaga missed call dinsa badamar na daga ina tuki wayar tasa yasa a kunne maganar da yaji anfadamasa a wayar ita ta girgizasa ya dan saki murmushi bayan gama wayar yace,to meye abin damuwar ki shirya yanzu m tafi gidanku ashe aprilfun ya miki ko zariyanma baije ba ita dai Rufaida cikin kasala ta mike tana tunani kala kala to ita tunda take da AbdulWahid baitaba mata wani April fun ba bare kuma yau yayi mata yanzu asalima shi bayasan wannan April fun din tunda ba shi a musulunci shiru tayi ta mike tasa hijibinta tace ta shirya Kabir yace kema wife kije ki dauko hijabinki tace Abban Yusuf kaje kaci abinci mana kafin mu tafi yace kibarshi ni na koshi munje shoprite da Nazir,Luba dai ba tace komai ba dan tasan mijinta baya cin abinci ako ina ba sai gida

Hanyar Zaria ya nufa dasu ya hada rai domin karsu tanbayesa ma Rufaida kuwa kukan zuci kawai takeyi dan tariga data yanke tsammani

Wani dattijone da zaiyi shekara sittin ne ya shigo babban falon gidan da waya a hannunsa yanasa sallama duk atare suka amsa masa kallon mutanan daake falon yayi kowa yana harkokin gabansa wasu suna kwance wasu suna kallon tashar sunnahTv din da ake karatun alqur'ani wasu suna bin karatun wasu sunacin abinci babu wanda yake surutu dai saboda karatun ina Hajiya Jamila batakai ga cewa gani ba yace lafiyar AbdulWahid kuwa tun dazu yaketa kirana kinsan muna meeting banma shiga da wayarba na barta tana caji a mota sai yanzu dana shigo gida na dauko wayar na duba nagani hajiya jamila tace,ai ina tunanin yau zaizo shine dalilin kiran nima ta yiyu ya kirani nasata a caji wayartawa,dattijon yace bara to na kirasa naji kiran yayi yawa wajen 10 da kira wannan dan sandan ya daga nan ya labartawa masa komi cikin rashin kwarin gwiwa Abba ya katse wayar daya daga cikin matasan yace Abba mai ya faru Abban bai sauraresa ba yace k sameni a waje yayi kofar fita matashin maisuna Abdulmalik da shima ya kidime dan shima ankirasa amma bai daga ba tana dakinsu shikuma yana falo,Hajiya Jamila babu ko mayafi ta fito don ta tabbatar ba lafiya batasan mummunan labarin da zaizo mata ba,Hajiya Kubra ce tayi kokarin mikomata hijabin jikinta Abdulmalik ne yaja ya kaisu asibiti tundaganan Hajiya Jamila ta fara salati tana shikenan na rasa dana motar da Abba yace yaja Emergency da aka kwantar da AbdulWahid suna isa dakin da aka kwantar dashi aka kaisu da taimakon yan sandan da Abba ya kara kiransu babu wanda zaiso kara kalan AbdulAhad rai yana hannun Allah sau daya Abba ya kallesa,Hajiya Jamila kuwa jikinsa ta fada tana kuka mai sauti Abdulmalik ne ya janyeta yayi waje da ita yana lallabata akan zai tashi cuta ba mutuwa bace,Abba shikansa dauriya yake ya kara ga dan nasa mafi kyautatamasa duk a cikin yaran nasa, hannunsa ya kama ya maida dubensa ga fuskar dan nasa yana cewa AbdulAhad kayi addu'a zaka tashi da izinin Allah kaidai ka riqa salati da kalmarshahada yana jin bakinsa alamun magana amma bayaji yaji dai motsi inda ya sa kunnensa a saitin bakin AbdulWahid din yaji dai yana Rufaida Abba,daganan baisake jin komaiba sai motsin da bakinshi yake Abba yana nanatamasa Kalmar Shahada yana ganidai yana motsa bakinsa baisan maizai ceba yadai fi tunanin kalmarshahadar da yake shima yanayi ganin bakin AbduWahid ya daina motsi shine ya tabbatar da cewa AbdulWahid ya rigamu gidan gaskiya dukkan mai rai mamacine koda rasuwar tazo wa kunnen hajiya Jamila sumewa tayi a take anan,saida aka bata taimakon gaggawa ta hanyar fesamata ruwa Abdulmalik gawar dan uwansa ya kama yana kuka shima mai tsuma zuciya,yayi babban rashin da zai wuya yasamu irinsa tun suna yara AbdulWahid yana hakuri da abinsa yabawa Abdulmalik,anan aka gama komai akabasu gawarshi
Isarsu cikin asibitin Zariya yayi dai-dai da fitowa da gawar AbdulWahid a motar asibitin ganin motar Abba Bukar na binsu a baya yasa Kabir fasa shiga asibitin don sosai Kabir yasan mortar Abba Bukar kuma yasan Abba Bukar din,dauriya kawai yake yana bin motar har zuwa gidansu AbdulWahid unguwar su dake sabongari Zariya sautin kukan Rufaidah ne ta cika motar domin ta riga ta sadakar da cewa AbdulAhad yayenta yayi tafiya mai nisan da babu waiwaye bayan tafiyar,Yasir ma kukan yake ya makale cinyar mamarsa Luba ma zuciyarta ta karaya itama kukan ta fara Kabir shi kansa kukan yake shirin yi sai dai yakasa yi kukan zuci kawai yake tabbas yasan yarasa aminin aboki shine kadai yake fadawa damuwarsa ya samu sauki bayan iyayensa AbdulWahid mutumin kirki ne yaso ace yazo ya samesa bai rasu ba da zai iya sadaukar da komai don ya rayu muddin zai iya sai dai ina mutuwa bata shawara kuma Idan anyi ba'a dawowa baisan ya karaso gate din gidanba don tukin kawai yake ba tareda yana gane komaiba saida yaji karar bude gate ya tabbatar sunzo Rufaida bata jira yagama parking ba ta fito a lokacin da mutane ke kokarin fito da gawar AbdulWahid daga mota jikin gawar ta ruga ta fada da take haryau da jini tana kuka din tana Ku ajemin miji wallahi bashine ya mutuwa karya ake Ku aje shi mijina bai mutuba yaye fuskarsa tayi shima Yasir da yake abayanta jikin gawar babannasa ya fada da aka a jiyeta a harabar gidan basu kara jin motsinta ba sai kukan Yasir inda Hajiya Kubra tazo tajanyeta amma bata ko motsi anan ta zube ta yi kasa luu alamun suma tayi Yasir kuwa Kabir ne ya janyesa shima Kabir din kukan yake

Cikin kankanin lokaci labarin mutuwar AbdulWahid Bukar Bukar (ABB) ya fara zuwa kunnuwan 'yan uwa da abokan arziki da 'yan Unguwa abokansa na cikin unguwa,sukaji mutuwar AbdulWahid din sosai,matashi mai son jama'a bai da abokin fada lallai duniya ba'a bakin komai take ba wanda yayi damara dan ita ya kwance,daganan mutane suka fara tururuwar zuwa jana'iza

Wannan zuriyar tabbas sunyi babban rashi kowa kagani a gidan kuka yake wasu idonsu yayi ja jawur a haka aka shirya AbduWahid Hajiya Jamila kasa addu'a tayi bayan gama shiryasa sai kuka itako Rufaidah haryau bata farfadoba sai wasu daga cikin kannensa mata da yan uwansa ne sukayi suma suna kuka suna addu'ar koda aka budesa fuskarsa kai kace zaiyi magana da murmushi akan fuskarsa sai dai har yau jinin dake fitowa a jikinsa bai daina zuba ba daga gefen fuskarsa yake zubowa ba,dukda yadda aka wanke gurin, da haka daukesa aka masa sallah yayi jama'a sosai nan aka dawo aka dan Zauna daga baya duk aka watse domin ka'idar Abba Bukar bayasan wannan zaman na gulma abarsuma da rashin da sukayi yaron sa yataso da son kyautatamusu amma Allah ya karbi abinsa dukda dai akwai wasu yaran amma dai bakamar AbdulWahid din a cikinsu.
[4/27, 11:49 PM] Sadiya IB Khali*JININMU 'DAYA*
NA
Sadiya Ibrahim Khali

2
Chapter 2 · 0% Book details