← Book details Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 57

Sashe 47

Jininmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Ammi sannu da gida" Ra'uf yayi maganar yana karasa zama gefen kujerar da Ammin ke kai
Ammin ta dubesa ka'dan
"Yawwa Ra'uf,yanzu na tanbayi su Husna kana ina suka cemin kaje gidan Shureim"
"Eh wallahi Umma can naje naje dakinki na fada miki zan fita na tadda kina barci,a gajiye nake ma"
Harararsa Ammi tayi tace
" 'yar wannan tafiyar ace harka gaji,dafatan suna lafiya dai ko su Inteesar 'din?"
"Eh Ammi lafiyar.su kalau Irfan ne dai bayajin dadi shine naje na dubasa"
"Oh Allah ya bashi lafiya,dama yaro da yazo duniya zaka samu ya fara rashin lafiya"
"Wallahi kuwa Ammi"
"Au kako ji Samihan Ahmad ta haihu yau"
Cikin murna Ra'uf yace
"A'a Ammi wayata yau gaba daya a kashe take,mai aka samu"
"Nima dazu Ahmad ya fadamin yace min ya kira lambarta ka bai samu ba,Namiji aka samu"
"Kai Amma Ammi naji dadi mun samu aboki Allah ya raya mana shi"
"Amin ya rabb,kai yaushe zaka yi auren ne?"
Jin tanbayar da Ammi tayi masa da bai zace taba yasa shi kallonta
"Ammi aure kuma?"
Cikin karfin gwiwa tace
"Eh aure,ko haka kake so kayi ta zama,shekarunka kullum ja suke,amma kai naji ko maganarsa bakayi ga abokanan daga mai 'ya'ya biyu sai mai 'daya"
"Ammi ba nida budurwar ne har yau bansamu wacce tayi dai-dai da tsarina ba"
"Ai ba zaka samu ba kuwa,tunda ba nema kake ba,nida nayi ma sha'awar kaje kanemi auren Inteesar ba ki kayi ba,sai kaje ka nemawarwa abokinka soyayyarta,gashi nan ya aureta suna zamansu lafiya harda karuwa ma tsakaninsu"
"Ammi tayi maganar da nuna bacin rai
" amma Ammi na fada miki,Inteesar Shureim ya dade yana fadamin son da yake mata,kinga bai kamata naje na nemi soyayyarta ba"
"Amma ai tun a lokacin na fadama kaje ka samu wata ga 'yam mata nan a gari"
"Ammi bawai 'yam matanba samun ta gari a wannan zamanin shine aiki,kuma idan nasa mu banaso a sake kwatanta abinda ya faru a baya"
Sai yanzu Ammi ta soma fahimtar Ra'uf wato har yau dai bai manta da waccen yarinyar ba kenan bayan ta mayi aurenta ta dai kauda wannan tunanin tace
"Ra'uf kenan wato har yau ka kasa manta abunda ya riga da ya wuce,ya kamata ka manta da baya fa a yanzu ka tunkari gaba ka fahimta cewa bafa laifin su Yaya sule bane a waccen abun da ya faru,haka Allah ya kaddara tun fil'azal ita ba matarka bace"
"Hakane Ammi,amma na baki damar ki dubomin wata"
"To zamuyi magana da Dadynku Allah ya yima albarka"
"Amin Ammi na" shiru ne ya biyo baya
Shigowarsu Husna ya katse shirunsu
"Husna ce ta karasa wajen Tv tana cewa
" Ammi sai kace gidan makoki Tv a kashe bari na kunna"
Ammi tace
"Tunda kinzo sai ki kunna ai uwar iya"
Safiyya ta karasa kujerar dake saitin tasu Ammi ta zauna tana cewa da yaran indiyanci da shine yaran da sukeji sosai
"Ammi sannu da hutawa,yaya sannu da zuwa"
Cikin hadin baki suka ce yawwa
Sophie ta karaso tana cewa
"Yaya welcome"
Da murmushi kan fuskarsa Yace ur welcome Ammi na"
Daga haka ta zauna da murmushi kan fuskarta tace
"Yaya munfayi 'da"
Yace "Eh Ammi ta fadamin"
Safiyya tace "amma zamuje wannan karanma ko yaya?"
Yace"Anya kuwa Sophie"
"Kai Yaya don Allah muje munjema haihuwar Rufaida bare wannan aboki fa kayi"fadin Safiyya
Ammi ta harari Safiyya tace
" to sarkin da'din baki,karatun fa,kunsan zaku shiga first semester level 400"
Husna tace
"Kai Ammi kwana biyu fa zamu yi"
Harararta Ammin tayi tace
"Ba zaku ba fa,karatun zaku bari"
Ra'uf yace
"Ammi daina wahalar da bakinki nima ba zuwa zanyi ba bare su sa rai"
Safiyya ta fara magana kamar zatayi kuka tace
"Kai Yaya don Allah kayi hakuri"
Dady Jabir da ya karasa falon kowa da upstairs ya karaso falon yana kokarin fita jin hakurin da Safiyya ke bayarwa ya sashi saurin karasowa gurin da suke yace
"Ra'uf bazaka kiyayarmin Auta ta kuma kanwata ba mai tayi mana ne"
Ra'uf ya harari Safiyya yace
"Dady don ance fa bazasu UK ba gurin sunan matar Ahmad shine take ta'bara,kamar ita ka'dai aka hana zuwa"
"Kunga ku je ku shirya mu fita mu qyale su"
Da sauri suka mike ba sukayi Upstairs
Dady ya zauna a kujera yana murmushi ya kalli Ra'uf yace
"Ra'u har yau baka sami wacce kake so bane,ga kannenka nan su Husna da sun kammala degree dinsu aure zan musu ga babban wansu a gida ya zama gwauro?"
Ammi tace
"Wallahi Abban Safiyya nima maganar dana gama masa kenan"
Ra'uf yace
"Dady zan nemo insha Allah"
"Yawwa kayi kokarin hakan kaga Husna tanada saurayinta tsayayye Bello,yanzu saura Safiyya itace bata fito da miji ba,idan kuma kana santa sai ayi 'yar gida"fadin Dady Jabir
Ra'uf ya dan bata rai jin maganar Dady yace
" kai Dady,badai Safiyya ba zan nemo dai"
"To meye aibun Safiyya ne" Ammi tayi maganar tana tsare Ra'uf da ido
"Ammi kinsan dai wacece Safiyya kuma kinsan Hajiya bazata yarda ba kuma ma kinsan ko Baff...." Jin sallamrsu Husna yasa shi yin shiru da maganar Dady mikewa yayi ya kalli su Ammi yace
"Mu zamu fita"
Suka hada baki gurin cewa
"Allah ya kiyaye hanya" suka fice
Su Ra'uf suka cigaba da firarsu.
Chapter 47 · 0% Book details