← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 163

Sashe 97

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karasa yana magana da Namra da ke zaune a kasa tana rusar kuka har lokacin tana lalaba bayanta, gaba daya ta cire zip din rigar amman zabin da take ji sai take jin kamar kunamar tana nan bayanta, tun da ta zo duniya kunama bata taba cizonta ba, sai yau.

“Ya zan yi na ba su hakuri ya ake bada hakuri, dan Allah ku yi hakuri ku yafe min...”

Tana kuka tana rokonsa har da hade hannayenta guri daya. Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba sai ta yi saurin rufe bakinta ta juya baya. Kowa sai da ya kalleta Momy ta yi kamar ta yi mata fada saboda ta yi dariyar Namra, sai kuma ta tuna ta kalli twins din ta shanye maganarta. Captain ya sauke kansa kasa a hankali yana murmushi dariyarta is something else da ya daukeshi ya jefa shi wata duniyar ta nishadi, sautin giggles laugh dinta na ta maimaita kansa a kunnunsa.

“Shatu shiga ki dauko mata hijab dinta mu tafi asibiti”

Momy ta fada cikin bacin rai, ba dan tana gudun ran yaran ya kara baci wata Matsalar ta sake afkuwa ba da sai ta yi ma yaran duka kuma ta ci uban Hurriya saboda dariyar da ta yi. Tare da Shatu suka haura sama ita ta shiga dakinta ta dauko keys din mota Shatu kuma ta dauko Hijab din Namra, Momy ta sauka Shatu ta saka ma Namra Hijab din ta rikata ta mike tsaye tana kuka. Momy ta yi zaton Captain zai ce ya kai Namra Asibitin amman be yi wani unkurin ba har direbanta ya shigo ya karbi keys din suka fice. Inna Kulu da Shatu ma suka fice daga falon, aka bar Hurriya daga ita sai kanenta da Captain. Sai a lokacin Hurriya ta samu natsuwar kwashe abincin da twins suka zubar ta zuba a plate ta dauke komai ta nufi kitchen tana aje plate din ta kunna tap ta wanke hannunta, sai ta ji magana a bayanta.

“Kin iya dariyar keta ko?”

Me zata yi idan ba dariyar ba, ta sake kyalkyalewa da dariya irin dariyar nan da baka iya controlling, idan ta tuna yadda Namra ta yi a dazun sai ta kasa rike kanta, ta juyo tana fadar

“I wish ni ma twins ce da an bata min rai... ”

Ta kasa karasa a yayinda ta kalli fuskarsa, tunawa da shi din ba abokin hirarta ba ne kuma ba yayanta ba, hasalima bata da wata alaka da shi, sai dai kuma murmushin da ta yi arba da shi a fuskarsa ya saka ta dan ji sakewa fiye da yadda take ji idan ta kalleshi a baya.

‘I'm your twinned, duk wanda ya taba ki, will see my reaction Immediately, trust me Hurriya i hear the whole story, i know the pain behind this precious smile of yours’

Magana yake daga zuciyarsa zuwa ga Hurriya dake tsaye gabansa yayin da yake rike da murfin fridge.

“Zaki iya haihuwar twins ai, yawanci gadonsu ake, idan kika yi aure zaki iya haifawa mijinki twins ko Tripple, i love twins too”

Ta kara fadada light smile dake fuskarsa kamin ta sauke kanta kasa ta fice daga kitchen din, ba tare da ta sake cewa komai ba. Ya dan daga girarsa kadan ya kai hannunsa ya dauko lemun kwalba ya bude sannan ya rufe fridge din, ya dawo bakin kofar kitchen din ya tsaya shi baya cikin falon shi baya cikin kitchen din ya jingina yana kallon Hurriya dake haurawa stairs tare da twins dinta gwanin sha'awa. Sai da ta haye gaba daya sannan ta juyo ta kalli kofar kitchen din, daman jikinta ya raya mata akwai idon wani a akanta, lemun dake hannunsa ya daga mata yana murmushi, ita ma ta yi murmushi kadan sannan ta dauke kai ta karasa saman ta isa bakin kofar dakinta, ta nan kam baya iya hangota ita ma bata iya ganin wanda ke falon. Dakinta ta tura sai da yaran suka shiga sannan ta shiga ta rufe kofar, kan gadonta dayan ya fada, dayan kuma ya nufi gurin da madubinta yake ya fara yi mata tabe tabe.

“Hamid bari mana, zo ga chocolate”

Ta dauko ragowar chocolate dinta ta mikawa musu. Ko da su Momy suka dawo Captain ya bar gidan, a daren Namra bata yarda ta kwana dakinta ba dakin Momy ta kwana saboda tsoro, washe gari da safe Momy ta kira masu kula da fulawa suka bincike dakin na Namra babu kunama babu alamarta, dakin Momy ma da aka daga gadon ba a ga komai ba.

Misalin karfe goma sha biyu na rana Maryam da wata yar'uwarta suka sauka airport din sokoto, Appa ya aika da mota a sirrance aka daukosu tun daga sokoto har garin Gusau, bata samu isowa gidan sai karfe biyu da rabi, saboda yanayin tafiya. Ko da ta shigo gidan yana cike da mutane kamar jiya, masu zuwa gaisuwa da gaske da kuma masu zuwa cin abinci, ta fito motar tana sanye da mask sai doguwar rigar Abaya da ta rufe jikinta kovina ruf. Cousin dinta ta ma ta fito motar kowacensu tana rike da jaka, suka shiga bangaren na Hajiya Kaltume, tun a waje suka gaisawa da mutane suna musu ya hakuri har suka shiga can ciki gurin Hajiya Kaltume dake kwance a kan gado zazzabin na dawainiya da ita. Sosai Maryam ta yaba halin kawarta na kirki tana kukan rashinta, ita kanta mutuwar ta taba ba kuma ta zo mata bagatatan a lokacin da ba ta yi tsammani ba, na ita kadai ba mutuwar Salma ta bawa kowa mamaki, ko da yake ba a mamakin ikon Allah, sai dai jin cewar tana lafiya kalau gashi bata dade da gama karatu ba, ya saka kowa tausaya mata. Bayan Maryam ta yi gaisuwa sai kuma ta yi kuskuren gabatar da kanta a gurin Hajiya Kaltume saboda ta san wacece ita, ba dan tana son auren mijinta ba sai dan abotar dake tsakaninsu da Salma.

Hajiya Kaltume dake kwance ta tashi zaune ta gyara hijabinta tana kallon fuskar Maryam.

‘“Daman ke ce yarinyar?”’

Maryam ta dago ta kalleta, ba ta yi zaton Appa ya fada ma Hajiya komai a game da maganar aurensu ba, domin shi da kansa ya bukaci su bar maganar a sirrance har sai idan an daura aure sannan kowa ya ji, ta dayan bangaren kuma bata zaton Salma zata boyewa mahaifiyarta wacece ita saboda ta gargade tun a ranar da suka yi bankwana a airport.

“Ke ce yarinyar da kika haddasa mata bakinciki?”

Maryam ta maida kanta kansa tana jin kunya na rufeta. Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana jin kamar da wuka a kusa da cakawa Maryam ta kasheta.

“Ke ce fitsarriyar yarinyar da kika hakikance sai kin auri ubanta? Duk saboda ku yata ta mutu, ke da Iyami ba za ku gama da duniya lafiya ba, Allah ya tsine muku albarka”

Maryam ta san wacece Iyami domin tana labarin yadda gidan Appa yake ciki da waje, ba ta gurinsa ta ji ba ta gurin bincikar yadda rayuwar gidansa take ta ji.

“Shi ne saboda baki da kunya kika dauko kafa kika zo yin murna ko?”

Maryam ta dago da sauri.

“Subhanallahi wake murnar mutuwa? Ni kawar Salma ce ba makiyiyarta ba”

“Kawarta ba zata ce zata auri ubanta ba, mugun kwadayi da dogon buri ya saka zaki auri ubanta tsohon da ya isa haihuwarki, kin ji kunya yarinyar kin ji kunya rayuwarki zata lalace nan gaba, na rantse da Allah sai kin wulakanta”

Fada sosai Hajiya Kaltume take yi, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ana riketa ana rufe mata baki amman ta kasa daina saboda zafin mutuwar yarta da take ji, ga kuma silar komai a gabanta tana gani ita tana raye. Hajiya Fatee dake waje ta taso ta shigo cikin dakin ta ita da mutanen dake waje ciki har da Hajiya Binta. A fusace Maryam ta mike tsaye cikin masifa ta ce

“Miye laifina dan na zo gaisuwar yarki? Tun daga garin Naija na taso na zo garin nan saboda gaisuwar Salma, akan wane dalili zaki tara min mutane, to bari jiki na fada miki kanki kika tonawa asiri, domin wanda be san mijinki zai kara aure ba yau ya sani, kin kunyata kanki da mijinki”

Tana aje aya Maama ta dauke ta mari, ta kai hannu zata rama Khairy ta rike suka fara dukanta, cikin karfin hali ta fara ramawa ita da cousin dinta aka hau rabasu daker aka kwaci Maryam hannun Maama da Khairy. Hajiya Binta ta dakawa Hajiya Kaltume tsawa

“Wai ke kan kanki farau aure? Wane irin mugun kishi ne yake damunki? Kina babba amman baki san ki tsawatarwa yayanki ba sai dai ki bude musu kofa?”

“Hajiya Karki kara min bacin rai, daman kullum goyon bayan dakinki kike baki tana ganin farina ba, ai ni ba wani abun na yi miki ba amman kika dauki tsana da kiyayar duniya kika dora min, ko wani abun na tare miki?”

“Magana kike ta rashin hankali da tunani Kaltume, ashe mutuwar Salma bata isheki ishara ba? Girma kike kina cin kasa? Jiya ma danki sai da ya kuka min akan abun da kika yi ma Rukayya, yaro yana son yarinya amman kina neman shiga tsakaninsu saboda bakin kishi da ba zai haifar miki da komai ba? Yanzu kuma kin zo gaban mutane kina kunyata mijinki akan abun da baki da tabbaci? Kuma ko da kina da tabbaci ya kamata ki ci mutuncin yarinyar da ta dauko kafa daga nesa ta zo miki gaisuwa? Kim kunyata kanki kin kunyata mijinki. Shiyasa kullum nake yabon Iyami kun fita shekaru amman ta fi ku hankali, wannan abun da kike yi hauka ne?”

“Hauka ne Hajiya, idan kina da magani sai ki ba ni, na gaji da abun da kike min, ba ba ku san me nake ji a zuciyata ba, ba kussn yadda yata ta rasa rayuwarta kun saka ni gaba kuna kunna min wata wutar, na yi kishin kishin halak ne, ni na auri Haruna tun ba shi da komai har ya zama komai, ni nasan fadi tashin da muka yi na rayuwa”

Hajiya Binta ta nunata da tsaya rai a bace.
Chapter 97 · 0% Book details