Sashe 163
Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Amaryar Musib ta tare a garin da mijinta yake wato a Zamfara, Ruma kuma ta tare a gidan nata mijin dake Kano. Duk da rashin lokaci da takurarwa aiki da Captain yake samu haka ya cije ya zo daurin auren na dan'uwansa da kuma yar'uwar matarsa. Sai da Hurriya ta yi da gaske sannan ya barta ta fi kai Amarya Kano, daga can yayi mata booking flight zuwa garin da yake aiki a yanzu. Sai bayan biki da kwana biyu sannan Hamad ya shirya ya kai musu Manal da aka bari a gurin Amma, yayi kwana biyu a garin sannan ya dawo gida.
*** *** ***
Manal na ganin Daddynta a kwance ta zo da gudu ta fada a faffadan kirjinsa ta kwanta.
“Dada baka da lafiya”
Ya daga idonsa kadan ya kalleta.
“Yes Manal”
Hurriya ta kai hannu ta taba wuyansa.
“Jikinka yayi zafi, bari na kawo maka magani”
Ta mike tsaye ta fara tafiya kenan ta ji yayi mata wata magana da ta saka ta juyowa da sauri tana tofar da yawu.
“Wata kila dai ba a banza nake fever nan ba, duk a karkare daga karshe ba zai wuce ace akwai ajiya a cikinki ba”
“Allah ya kiyaye, yaushe aka haifi Haidar din ma to, yaron da yanzu yake koyon zama”
“It doesn't matter, ni dai na san irin wannan fever dake sani kyamar abinci da zafin jiki sosai bana yinta sai da dalili”
“Wallahi aa Allah ya tsare Malaria ce kawai, ko kuma gajiyar aiki”
“Zamu gani ai sai a gane mai gaskiya, ni na san yanayin da nake ji ba irin na rashin lafiyar mutane ne ba ne”
Ta daga kafadunsa tana murde baki.
“To wata kila aljannu suka shafe ka”
Ya kyalkyale da dariya sosai kamar ba shi ba ya daga Manal daga jikinsa ya zauna ya zaunar da ita. Hurriya kuma ta shiga ciki ta dauko masa magani da ruwa ta balla ta ba shi ya sha.
“Thank You Allah ya miki albarka”
“Ameen Allah ya baka lafiya”
“Dada Allah ya baka lafiya”
Manal ma ta fada sai ya amsa da Ameen yana murmushi.
“My Ammy rabin raina”
Hurriya ta tabe baki.
“Hamad na yi aure zan bada ita”
Manal ta lake kafada kamar ta san abun da ake fada, Captain kuma yayi dariya mai sauti.
“Da kin jawa janki wahala ko ya dauki yarana ai sai ya dawo da su zai samu salama, ko da Nigeria ne kuwa balle wata kasar”
“Ni ma dai bana son zaman shi a can”
“To ya za'ayi tun da ya zabi cigaba da masters dinsa a can”
“Wallahi duk saboda yarinyar nan ne, ni bana son ma ya aureta saboda Salim”
“Ina ruwan Salim da soyayyarsu? Ita dai tace Hamad take so, shi ma kuma yana sonta sai kawai a musu fatan alheri”
“Ai Amma ba zata bari ayi auren yanzu ba sai ya gama masters dinsa”
“Kamin lokacin ita ma ta gama makaranta ai, sai ayi daidai a dauko muku yar Ethiopian amman al'adunsu daban da na mu”
“Wai Salim yana duniyar nan ma?”
“Yana nan mana, kin san an watsar da lamurransa shiyasa ba ni da labarinsa yanzu, yayi ta kamun kafa a kamin yayi aure yana son dawowa gurin Namra ya nuna masa ba ma bawa marar tunani da mutumci auren zuri'armu, yaje can ya samu daidai shi”
“Amman baka kyauta ba, ka sani ko tana sonshi har lokacin?”
“Ko tana son shi be cancanci aurenta ba, kuma ita ma bana jin zata iya aurensa gaskiya, ke ce dai take ta kishi har yanzu ta bari shedan ya shiga gabanta”
“Ai na gani, shiyasa yanzu ni ma bake kama jikina, Momy ma bata nuna min komai yanzu amman ita ta saka daina nuna min kyama”
“Zata daina with time, nan gaba zata gane kuskuren abun da take ta daina”
“Allah yasa”
“Ameen”
Ya mike tsaye.
“Ammyna Dada will take a little nap okay?”
“Okay Dada get well soon...”
“Ba dai Soon ba Ammyna, Mamanki ta riga ta shafa min ni ban san yadda aka yi ma muke raba pain din nan ba”
Hurriya ta saka masa dariya sai ya kai mata rankwashi a kai ya nufi dakinsa. Tashi ta yi ta bi bayansa sai ta samu har ya hau gado, remote ta dauka ta rage ac sannan ta lullube shi sai ya saka hannunsa da karfinsa ya janyota ta fado kansa.
“Come here ni kike yi ma dariya dazun dan kin ga gaban Ammyna ne ko?”
Ya fara kokarin tsikararta yana hada mata da mitsika sai ihu take data dariya.
“Na bari Allah na bari Captain”
“Oh Really Captain kai tsaye?”
Ya ma tashi zaune gaba daya yana chakularta.
“Yayana haba Dada Manal, My Noor na bari Allah na daina kuwa, haba Sojana”
Ya sumbance ta ta daga blanket din ya saka ta ciki shi ma ya lulluba ya rumgume a dolenta ta yi bachin da bata tashi yi ba har da su numshari.
*** *** *** **** ****
Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah. Godiya ta tabbata ga Allah da ya ba ni ikon rubuta wannan littafin. Inda na yi kuskure Allah ya yafe min, darasin dake ciki kuma Allah yasa ni da ku mu amfana da shi.
Haka kuma ina rokon yafiyar wadda duk na batawa rai cikin rashin sani ko ganganci a yafe min da Allah, idan mu ne yau ba mu ne gobe ba. 🤲
Ba zan aje alkalamin ba har sai na yi godiya ga duk wanda ya siye littafin Hurriya ma'ana yan paid group na Hurriya, da kuma yan Arewabooks. Na gode na gode na gode, na san kauna ce sila. Allah ya bar min ku.😍❤️
And to those that read my book without paying da wadanda suka yi forwarding, na bar ku da Rabbi 🙌
Malam Mai Tawakkali ina godiya Allah ya kara budi ya karo wasu customers masu yawa 🙏
Daga Marubuciyar.
ZAKI
FULANI
GOBENA
HAFSATU MANGA
RAI BIYU
DEENAH
BABBAN GORO
SALEENA
CIWON SO
BAKAR WASIKA
ZAGON KASA
ZABIN RAI
WANI GARI
HURRIYA
Ta ku har kullum🥰
KHADEEJA CANDY
(Oum Namra)
08036126660