← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 163

Sashe 86

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amin, wani abun kulu ai sai na samu lafiya ma, da yardar Allah idan bukata ta biya zan kyautata miki, ta shi ki tafi kamin Yasir ya shigo”

“Toh Hajiya, amman zan bar leshin a nan saboda idon mutane, sai idan na ga sarari zan zo na karba”

“Dadina da ke wayo Kulu kin iya sirri”

“Gidan na mu ne Hajiya sai da haka, kamin a fara fadar ana ganina bangarenki ”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi. Ita kuma ta mike tsaye ta yi mata sallama.

“Mu kwana lafiya”

Kamin ta isa kofar dakin ta bude Yasir ya bude sai dai be shigo ba ya bata hanya ta fita yana amsa gaisuwar da take masa.

“Me ta zo yi nan?”

Hajiya ta nuna masa lace din dake kasa

“Nafisa ta aiko min da lace?”

“Ke kuma?”

Ya tambaya kamar mai shakku, Hajiya dai bata sake ce masa komai ba ta nufi gurin da ta tashi ta zauna da tafiyar nan nata kamar zata yi dingishi.

“A kafa kike jin ciwon ne?”

“Eh gurin da na taba jin ciwo kwanan baya, a nan na sake jin ciwo haka nan kawai sai na ji kamar an tureni na fadi kasa”

“Ko santsin gurinki ne ke janki”

Ya soma duba kafar da ta dan dago masa tana jin kamar ana yanka gurin sai sululi yake mata kamar an watsa ruwan zafi.

“Aa ba wani tsantsi shekara nawa ina gidan nan da can tsantsin be ja ni ba sai yanzu? Turo ni ake yi fa”

“To wa yake turoki Hajiya”

“Yo ina zan sani tun da abu ne na aljanu, amman tabbas ba faduwa ce zallar faduwa ba, turo ni aka yi”

Yasir yayi murmushi tare da kai hannu ya latsa gurin.

“Ban san me yasa ku mata kuke yarda da irin abubuwan nan ba, haka Last week Rukayya take ce min wai ance aljannu ne a jikin Amma, ku dai komai kun fi son ace aljannu ne, wani abun fa daga Allah yake kai tsaye idan ana na asibiti zaki ga an dace, ita kanta Amma da za a fitar da ita waje a dubata duba mai kyau za a gane Matsalarta”

Hajiya ta janye kafarta da sauri saboda lasa gurin da Yasir yake yi.

“Ku kuma ba ku yarda da aljannu ba ko?”

“Mun yarda da su mana, amman ba lallai komai ace su ba, kin ga kafar nan take da zaki iya daurewa mu bari sai da safe mu tafi asibitin, hoto za su miki su duba matsalar”

“Eh haka zan yi, mu hakura da tafiya asibitin nan sai gobe da safe”

“Ba sosai kafar take damunki ba”

“Yanzu dai ta min sauki ba kamaf dazun ba, kai Allah sarki na tausaya wa Iyami gaskiya, a kafa kawai ina jin ciwon nan kamar zan mutu balle ita da ta ke kwance bata iya komai shekara da shekaru, wai har yanzu bata iya tashi da kanta?”

“Rukayya ta ce min tana tashi da kanta yanzu, kuma da kanta take cin abinci, rayuwar Amma akwai ban tausayi sosai, gashi ba wani karfi yanzu sosai ”

‘Munafuka Hurriya wato kin iya kini bibi ko? Ni zaki yi ma karya?’

Ta fada a ranta tana wani kashe ido, a zahiri kuma sai ta ce.

“Allah ka raba mu da wahalar duniya, wato Yasir yanzu ka zama dan gidan ka san ciki da waje”

Murmushi yayi ya mike tsaye.

“Daman can ai dan gida ne ni, ba wai sai saboda Rukayya ba”

“Haka ne, Allah ya zaba abun da ya fi zama alheri amman dai ina son ka sani ba zan taba yarda ka dauko yar'uwar makiyiyata uwa daya uba daya ka kawo a gidanka ba da sunan mata”

“Hajiya Amma ce makiyiyar? Idan ma kuna kallon junanku da wannan ne ban isa na canja ba, amman matsalarku dabam be kamata ta shafe mu ba, musamman ma ita Rukayya meye nata a ciki?”

“Wai dan Allah duk matan garin Gusau ka rasa wanda zaka so sai ita? Me ta fi mata da shi ne?”

“Hajiya ni dai ita nake so kuma ita zan aura da yardar Allah”

Hajiya ta daure fuska sosai tana watsa masa danta da be kishinta harara.

“Ina fada maka bana bukatarta a matsayin suruka kana karanta min ita zaka aura, saboda kai ne uba ni ce ya ko? To mu zuba ni da kai shege ka fasa, ko saboda ka ga wacan karon ka min magana na maka sanyi? Ina duba gudun ruwanka ne? Amman Wallahi ko Rukayya ita kadai ta rage a duniya ba zaka aureta ba”

Gudun sa'insa da ita ya saka shi ficewa daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, sai dai kana kallon fuskarsa zaka san kalaman na Hajiya Kaltume ba su masa dadi ba.

“Wallahi ba zaka aureta ba, ni gaba daya ma kamar an canja min kai, kai kenan namiji Allah ya ba ni amman baka min biyaya, idan ina kiyayya da mutum kai sai ka dauke shi masoyi, haka kake rawar jiki akan Hurriya sai ka ce ni na haifi yarinyar nan”

Ta yi ƙwafa, kamin ta juyar da fadan gurin Hurriya da bata san tana yi ba.

“Ita kuma tsohuwar makira wai ita nan har ta iya canja labari ta fada min Iyami bata ji sauki ba, wannan yarinyar da wata babbar mace ce da ni zata yi kishi nan gaba, amman zan maganinku duka”

Ta mike tsaye tana daga kafar ta nufi bandakinta.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
28
Ita ke da girki yau, amman sai ta saka Khairy ta kai ma Appa komai a bangarensa, saboda ba zata iya zirga zirga da kafar ba, daman kuma tana jin wani abu mai kamar haushin Appa a ranta yanzu. Dan haka bata leka bangaren ba sai after goma da wani abu, sannan ta saka kayan bachinta ta dora bakar abaya a sama, yau kam bata damu da yi ma mijinta ado ba, daman kuma ba wani yabawa hake idan ta yi ba, bata sani ba ko dan bata da kyau ne ko kuma saboda an dade tare da juna, amman ta tabbatar idan Iyami ce ba zai kyale ba, tun asali can Appa irin mutunen nan ne dake da rayuwar da, wani abun zuwan Amma ne ta canja shi, wani kuma Momy ce ta yi sauya mata ta karfi da yaji.

Bata bar annuri da fuskarta ba saboda damuwa ta mata yawa yanzu, har ta rasa ina zata kama, haka ta shiga barayar mijinta ba tare da sallama ba, Appa ya aje wayar dake hannunta yana kallonta da yanayinta, a gaban gadon ta zauna cikin wata muryar dake kara bayyana fushinta ta ce.

“Sannu da zuwa?”

“Yauwa, amman yau lafiya kike kuwa?”

“Me ka gani?”

Ya gyara zamansa yana kallonta irin kallon nan na mazan da suka kwashe shekaru a duniya kuma suka fahimci rayuwa.

“Na ga yau Ummul Khairi ce ta kawo abinci, kuma kin shigo babu wani walwala a tare da ke, kayan bachi da kika saba sakawa a nan ma yau can kika saka kika zo da su?”

Ta dan tabe baki.

“Ashe kana lura da al'amurrana”

Appa yayi dariya irin ta can cikin makoshin nan ya dubeta a natse ya ce

“Shekara nawa ana tare Kaltume? Uwargida ran gida? Uwargida sarautar mata? Kuma sai ace ban lura da yanayinki ba? Ai shi miji kamar....”

Ya ja zaren furucin yana sosa gafen idonsa tare da aje wayar hannunsa.

“....Uba yake wani lokacin duk wani abun da mace take yi yana lura da shi, ita kuma mace kamar gidan uba take a karkashin miji, wani ikon ma har ya fi na uba, shiyasa Allah yake cewa ku tsiratarta iyalanku daga wuta, wanda makamashinta su ne Mutane  duwatsu, ku ai kuyo ne a gurinmu, dole sai muna kiyayewa, kuma kuna taya mu idan ba haka ba abubuwan sai su mana, a duk lokacin da na tuna cewa zan tsaya a gaban Allah amsa tambayarsa sai hankalina ya tashi matuka”

Ta juyo ta kalleshi a tsanake.

“Saboda me?”
Chapter 86 · 0% Book details