← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 163

Sashe 16

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A jere suke suna tafiya Hamad ya tambayeta domin abun da ya tsaya masa a rai kenan tun a lokacin da ta boyewa Amma cewar sun yi fada.

“Idan ta ji zata ji ba dadi ba, baka ji tana cewa mu zauna lafiya ba? Idan kana yin fada ran Amma zai bace”

“Ni dai bana son Hajiya bana son Momy bana son kowa a gidan nan”

Yana fada yana wani cin magani kamar wani babban saurayi, Hurriya ta tsaya kallonsa da mamakin furunci, shi kam tuni ya juya ya fasa shiga bangaren Hajiya Kaltume ma ya nufi na su bangaren duk kuwa da ya san Amma bata gidan. Hurriya ta cigaba da tafiya har ta isa bakin kofar falom ta muda kofar ta shiga da sallama farin gilashin dake kara mata kyau yana fuskarta.

“Wa'alaikassalam”

Fadeel ya amsa mata yana zaune daga gefen kujera yana gwada kiran Hajiya Fatee.

“Ni yanzu hankalina ya tashi sosai, ace har karfe goma Hajiya bata dawo ba? Ga wayarta baya shiga, daman tun da Ruma ta dawo makaranta take ta damu na da ina Hajiya”

Cewar Maama tana gwada kiran Hajiya Kaltume.

“Amman fa ce mana ta yi gurin Hajiya Fatee zata je”

Fadeel ya ce

“Bata gidan, domin daga can na fito masu aikin suka ce min tare suka fita da Hajiya, shiyasa na zo nan ko tana nan domin wayarta har yanzu bata shiga”

Yasir ne ya shigo falon yana motsa keys din dake hannunsa.

“Hurriya ke da Hamad Appa yace na kira ku, Ina Hajiya?”

Ya karashe zancen yana kallon Maama da hankalinta ya tashi sosai kamin ya karasa ya mikawa Fadeel hannu su gaisa.

“Ita muke ta nema?”

“Ban gane ita kuke nema ba?”

Tambayar Fadeel dake fadar haka yake da mamaki.

“Dazu na shiga na gaishe da Hajiya aka ce sun fita tare da Hajiyarka, yanzu kuma na dawo masu aikin suka ce min bata nan, na gwada kiran wayarta kuma ba a samu shiyasa na zo nan ko zan sameta sai kuma na tarar nan din ma kanenka neman Hajiyarka suke”

“Wai tun fitar da ta yi da safe bata dawo ba? I thought ta dawo ba fa, yanzu ma Appa ne ya ce a kirata”

Maama da tuni ido ya raina fata ta fara kuka ta ce.

“Wallahi bata dawo ba har yanzu, ni hankalina ya tashi”

“Subhanallahi, to ina ta ce zata je?”

Maama da Salma suka amsa masa, duk abun da ake Hurriya da ido kawai take binsu, Fadeel kuma yana jefa mata kallo time to time, farar fatarsa sai daukar masa hankali take kasancewarsa baki, ba shi kadai ba har Yasir da duka yan matan Hajiya Kaltume babu fari ko daya, sai wanda ya dara wani baki, domin an yi gadon bakar fata ta uwa ta uba, kamar yadda shi ma yake baki sai dai nasa bakin mai kyau ne irin mai shaike da ya dace da fatarsa ya karawa hancinsa fa fararen hakoransa da idanuwa kyau. Hurriya ta mike tsaye ta nufi kofa domin amsa kiran mahaifinta Fadeel ya bita da ido yana kallonta kasa kasa har ta fice, ba wannan ne karon farko da ya fara ganinta ba, amman a yau ta tafi da shi, domin ta kure iyakar ganinsa ta cika idonsa.

*** *** ***

Wasa-wasa aka nemi Hajiya Kaltume aka rasa babu amo babu labari, duk inda ake saka ran za'a gane an bincika bata nan, haka ma Aminiyarta Hajiya Fatee ita ta bangaren danta Fadeel babu inda be bincika ba amman be same ta ba, gashi be san direban da ya daukesu ba balle ya neme su, wayoyinsu kuma idan an kira ba mai shiga, shi kansa Appa sai hankalinsa ya tashi balle kuma yayanta da bachi ma ya gagaresu, Hurriya ma da ba yarta ba sai da nata hankalin ya tashi domin bata son ta ji wani abu marar kyau ya same mutum.

Tun ana maganar kwana daya, biyu har aka yi sati, sai da Hajiya Kaltume da Kawarta Hajiya Fatee suka yi kwana goma cif sannan aka kira wayar Appa ana neman ya fada miliyan dari, domin sun tambayi Hajiya kuma ta fada musu waye mijinta, ta bangaren Hajiya Fatee ma haka suka nema gurin ďanta. A lokacin Appa ya zo musu da labarin yana mamaki su ma mamakin suka yi, ba su mamakin jin cewar tana hannun kidnappers ba daman sun saka tsammanin haka domin sun bincika ko'ina ba a same ta ba, kuma su kai report gurin police an saka addu'a amman duk shiru, kudin da suka bukata ne abun mamaki.

“Miliyan dari kuma? To a ina suka samu number ka Appa?”

Yasir ya tambaya cike da mamaki da kuma tashin hankali a lokaci daya.

“A gurinta suka samu, na yi magana da ita na ji murayarta?”

“How taya suka kama su? Wannan abun sai idan da na gida aka hada kai”

“Ban sani ba, amman dai mai maganar yace sun kama su a wani kauye dake kusa da gidan zalla nan kwatarkwashi”

“Ikon Allah, amman dai tana lafiya ko Appa”

Ruma ta tambaya tana kuka.

“Ba mu sani ba dai, ba mu gama magana ba suka yanke wayar kuma na kira bata shiga”

“Kamata yayi a sanar da police tun wuri”

“Zan kira yanzu na sanar musu”

Appa ya juya ya fice, cikin wani karin tashin hankali sa be gama warkewar daga na Amma ba an kara masa wani.

HURRIYA POV.

Hurriya na zaune falon Momy plate din shimkafa a gabanta tana cin abincinta na dare, Namra zaune saman kujera tana duba dogayen rigunan dake zube gefenta kan kujera. Momy ta shigo daga bangaren Appa. Namra ta mike tsaye da sauri tana nuna mata rigar da ta zaba.

“Momy wannan nake so, Hurriya ta dauki bakar”

Momy ta tsaya kallonta.

“Idan ta dauka ke zaki biya? Ka ji min wani rainin hankali”

“Momy toh ai na ga na shagonki ne”

“Idan na shago ne mutuwa na yi balle ki ci gado har ki dauka riga mai tsada ki ce abawa Hurriyya?”

Namra ta juya ta kalli Hurriya sannan ta juyo ta kalli Momy tana mana alama da zata iya ji.

“Ta ji mana, tsoronta nake? Ke ce baki san ciwon kanki ba har kika hada kanki da ita, kina kallo a gidan nan duk kudin da mahaifinsu zai bada na siyen abu sai na ciya na siyo muku wanda ya fi na sauran yan'uwa, amman yanzu har kika maganar ki saka riga Hurriya ta saka irinta”

Da kamar mamaki Namra ta ce.

“Ubanmu daya da ita fa, kudin da Appa zai bata su zai ba ni duk daya ne”

“Eh amman ai ina kara miki? Tufafin da kuke sakawa wake sska su a gidan nan? Karki sake min wani abu makamancin wannan, rai na a bace yake kin kara min wani”

“Me ya faru Momy”

“Kaltume ce wai kidnappers sun kamata suna neman milyan dari”

Momy ta fada tana kiran sunanta domin ita kadaice a gidan bata sakawa Hajiya Kaltume ta ce Hajiya sai dai ta ce Kaltume kawai. Hurriya ta juyo da sauri jin abun da Momy take fada, Namra kuma ta zaro ido.

“Innalillahi daman sai da na fada tana ina yanzu?”

“Ke kin yarda? Ai talaka babu abub da ba zai iya ba, wannan Kaltume zata iya kidnapping din kanta da ta karbi wannan kudin gurin Alhaji, balle tana ganin yadda nake tafiyar da kasuwanci ai abun yana tsone mata ido”

“Haba Momy taya? Kuma har wannan kwanakin bata fito ba?”

“Ke makira ce wannna matar fa, ni na san yadda na zauna da ita, kin ji ta a waya sai kukan munafurci take wai wani idan ta kara sati a gurin mutuwa zata yi, tana cikin bala'i da masifa a Alhaji ya taimaka ya kawo kudin da wuri hmmm”

Momy har wani kwaikwayon muryarta take tana nufar hanyar Kitchen Namra ta rufa mata baya dan kara jin labari, ita sam bata yarda an sace Hajiya Kaltume ba ta fi yardar Hajiya Kaltume ce ta sace kanta. Hurriya mamakin ya hana ta cigaba da cin abinci mamakin jin cewar an sace Hajiya Kaltume take, da dayan bangaren kuma tana mamakin yadda Momy take ganin kamar ita da Namra suna da banbanci bayan uba daya ya haife su, tana mamakin yadda Momy take duban Hajiya Kaltume ma dake da tarin rufe asiri a gidan tana ganinta talaka. Da sauri Hurriya ta cire hannunta a abinci ta fice daga falon zuwa bangaren su Khairi.
[10/18, 5:35 PM] Nana 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲 1: ☆❁ 𝗛𝗨𝗥𝗜𝗬𝗬𝗔 ❁☆

𝐁𝐲 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲

Hello Habibaties 😍🥰
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy

𝗣𝗮𝗴𝗲 9️⃣

Hurriya na shiga falon Hajiya Kaltume ta fara rabon ido ganin yadda kowa yayi jigun, wasu daga yayanta kuma suna amsa waya suna kuka. Gurin da ta tafi wayo ta nufa wato gurin yayanta ta tsaya kusa da shi tana kallonsa har ya gama wayar sannan ta ce.

“Yaya wai garkuwa aka yi da Hajiya?”

Kamin ya bata amsa Khairi ta watsa mata harara.

“Tsohuwar munafuka, hala dadi kika ji?”

“Dadi dai? Me ye abun jindadi a ciki da har zata ji dadin? Wace irin magana ce wannan?”

“Toh Yaya idan ba haka ba, me yasa take tambaya?”

“Bata da hakkin sani ne? Ni kuna bani mamaki a gidan nan Wallahi, miye laifi a ciki idan ta tambaya? Karki bata min rai yanzu na fara dukanki”

Yasir ya karashe maganar yana nunata da yatsa, sai ta dauke kai domin ta sani sarai zai iya, ba wani jutuwa suke da juna ba. Ya dubi Hurriya dake gefensa tsaye.

“Eh sace ta aka yi, mu ma yanzu Appa ya zo mana da maganar sun ce za a ba su miliyan dari”

A take hankalinta ya tashi, tana son ta sake cewa wani abu tana tsoron kar Khairi ko Salma su kwatseta, dan haka ta ja bakinta ta yi shiru tana cigaba da sauran yadda ake ta kiran yan'uwa ana fada musu.

****       ****         ****
Chapter 16 · 0% Book details