← Book details Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 163

Sashe 3

Huriyya Part 1 And 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Da kyau ni ma ya fada min haka, kuma yace wannan gasar ma mai tsoka ce, suna kyautata zaton idan kika yi ta daya za su dauki nauyin karatunki domin haka suke yi ma duk wadda yayi na daya, ni kuma na kara musu da cewa ko da ba su fitar da ke ba, zarar kin kallama makarantar da kike yanzu zan fitar da ke waje ki yi karatu mai kyau, duk kuwa da bana sha'awar fitar da ƴaƴa mata waje yin karatu amman ke zan fara akanki”

Ba shiri Hurriya ta bude baki tana mamakin jin furucin mahaifinta.

“Appa da gaske?”

“Da girmana zan yi karya?”

Ta saki chocolate din da hollandia ta rufe baki tana zaro ido kamar zai fado. Sai kuma ta daka tsalle ta dire.

“Appa i love you i can't wait”

“Ki dage da karatu Allah ya taimaka ina alfahari da ke, Allah ya miki albarka”

Ya fada yana murmushi yana nuna mata alamar lokaci a hannunsa da babu agogo, sai ta duka ta dauki abun da ta zubar ta.

“Ameen ina sonka Appana, na tafi sai na dawo”

“Allah ya kiyaye,”

Ta amsa da Ameen already ta sauka entrance din tana hadawa da gudu domin yan'uwanta sun kusa isa gurin bus din dake kaisu makaranta ta maido su. Tana daf da isa ta ji an fisge chocolate din dake hannunta kamin ta juyo aka fisge madarar hollandia din dake dayan hannunta. Suna hada ido ta bata fuska ta buga kafa kasa, shi kuma ya saka dariya yana kokarin bude ledar chocolate din.

“Yaya Yassar dan Allah ka ba ni”

“Wallahi ba zan baki ba”

Ya fada kai tsaye yana mata dariyar keta, juyawa ta yi cikin yanayin damuwa ta koma bangaren Appanta wannan karon bata tsaya gurin windows din ba ta murda kofar falonsa ta shiga, sanin talkamin makaranta ne daure a kafarta sai ta fadi kasa tana rarrafe dan kar ta taka masa carpet.

“Appa Appa Appa”

Alhaji Haruna ya fito daga dakinsa da sauri jin yarsa na kiransa.

“Hurriya baki wuce ba?”

“Appa YaYa Yassar ya kwace min abun da ka ba ni, na kowa yana nan ni ya karbe nawa”

Appa yayi murmushi ya juya ya koma ciki, be dade ba ya fito rike da wani chocolate din da hollandia ya mika mata.

“Appa dan Allah ka kora Yaya Yassar daga gidanka ka ce ya tafi ya bar maka gidanka, Wallahi takura min yake yi da yawa”

Tana fada tana saka hannu biyu ta karba.

“Idan kin hadu da shi a yanzu ki fada masa na ce ya hada kayansa ya bar min gidana, saboda ya cika takuraki ke da gidan Appanki”

“Appana na gode, zan fada masa haka a yanzu kuwa”

Cikin shagwaba da jindadi ta fadi haka sannan ta mike tsaye shi kuma ya kai hannu ya shafa kanta dake cikin hijab domin ya fahimci a bakin gaskiyarta take fadar Yassar ya bar gidan. Tana kokarin juyawa Amma ta shigo falon dauke da tray, bata yi mamakin ganin Hurriya a sitting room din mijinta ba, daman ta fi kowa yin latti zuwa makaranta ko fita unguwa. Musamman idan mahaifinta yana gari, a dole sai ta ganshi sannan zata fita, idan kuma bata zuwa ko'ina to tana zaune tare da shi a bangarensa babu ruwanta da ranar girkin Amma ne ko na Hajiya Kaltume ko Momy, ko da bata shiga har inda yake ba indai ta san yana nan zata zauna a part dinsa ne, hakan ya haifar da shakuwa sosai a tsakaninsu.

“Daman ai duk wanda yayi shiririta a garin Gusau a bayanki yake, ke kam Allah ya shiryar da ke Hurriya”

Dariya kawai ta yi ta fice tana fadin.

“Appa ka fada mata abun da Yaya Yassar yayi min. . .”

Daga mahaifiyarta har mahaifinta binta suka yi da kallo jindadi da farinciki har ta fice, sannan Amma ta girgiza kai ta maida dubanta ga Appa.

“Bismillah Appan Hurriyya muje ka karya”

Kamar wanda aka jefo a wata duniyar haka yanayin fuskarsa ya sauya daga murmushi da jindadi zuwa bakinciki da bacin rai da be san dalilinsa ba, ba dan komai ba sai dan jin muryar Amma a bayansa.

“Zan shigo”

Ya amsa ba tare da ya jiyo ba, domin baya son kallonta a yanzu, fuskar dake masa kyau da kwarjini, mace da yake gani yana jin kamar shi da ita sa'anin juna ne, a yau ita yake kyamar gani, muryar da ta fi kowace murya yi masa dadi a duniya yau muryar ce yake jin kamar tana sanar masa mutuwa. Cikin hikima da kokarin danne damuwa ta sauke ajiyar zuciya domin ta san shekaru da aka fito da watanni mijinta ba haka yake ba, a da idan ta kawo masa abinci jiki na rawa yake tarbarta ya fara zuba santi tun kamin ya ci, ba zai ma bari ta fara isa bedroom dinsa ita kadai ba sai ya rika mata tray ko ya dauki wani abun yana zolayarta, amman a yan kwanakin da idan aka a hada su aka kirga zai bada wata daya ya sauya mata gaba daya.

Sai da ya tabbatar ta shige sannan ya juyo ya kalli kofar dakin, hannu ya saka a kirjinsa ya danne tashin hankalin da yake jin yana kusantoshi. Cikin wani yanayi mai kama da nauyin jiki da na zuciya ya cira kafarsa ya fara takawa tare da maida hannayensa baya ya rumgume yana tafiya a hankali. Yana shigowa cikin dakin Amma ta juyo ta kalleshi da damuwar da ta gagara boyuwa a fuskarta.

“Ranka ya dede waya canja Bedsheet din nan?”

Tsaye yayi yana kallonta kamar mai tunanin kalar amsar da zai bata, kana kallon idinsa zaka karanci damuwar dake tare da shi. Can kuma ya kawar da fuskarsa ya dawo da hannayensa dake rumgume a bayansa ya zuba su cikin aljihu.

“Kaltume ce ta canja”

Da matukar mamaki Amma take kallonsa, domin al'adarsu ce duk wanda ke da girki ita zata gyara bangaren mijinta kuma zata tafi da Bedsheets dinta ta shimfida, idan wata zata karbi girki sai ta kwashe kayanta wadda ta karba ta shimfida nata ta kula da bangaren, hakan ya saka ko wace mace da kalar kamshin turaren dake fita a part dinsa idan girkinsu ya zo.

“Ban gane ta canja ba? Jiya na shimfida shi fa, kuma jiya da yau girkina ne, ai ta jira har sai girkinta ya zagayo tukuna ta canja”

“Ni na saka ta canja kuma na karya zaki iya dauke abincinki”

Kamar an watsa mata ruwa sanyi a jiki haka ta ji duk wata kusurwa da logo dake jikinta ya saki, lakkar jikinta ta yi kasa.

“Gaba daya na daina gane maka a yanzu Appan Hurriyya ka canja min”

Ta matsa inda yake tsaye ta risina kasan guiwowiyinta ta hade hannayenta kamar mai rokon gafara.

“Wannan shi ne karo na biyar da zan sake rokonka idan wani laifi na yi maka ka fada min na nemi yafiyarka, ka dubi girman Allah ka yafe min, ka daina hukunta ni da wasu dabi'u da halayya da ban sanka da su ba, kuma baka saba yi min ba”

“Baki min laifin komai ba Iyami, Wallahi ban rike ki da wani abu ba a zuciyata ba”

Ta daga kai ya kalleshi.

“Toh me yasa kake min haka? Akan wani dalili zaka saka Hajiya ta canja zanen gado kuma ta kawo maka abun karyawa bayan ni ce da girki?”

“Saboda zata karbi girki a yau”

Kamar an tsinke wutar cikin jikinta haka ta ji, sai ta mike tsaye tana kallonsa ta kasa sake furta komai.

Hannayensa ya cire aljihu zuba ya nufi kusa da inda ta aje masa tray ya zauna gefen gadonsa sannan yayi mata alama da ta zo ta zauna.
Ta kalli gurin da ya nuna mata amman ta kasa cira kafata ta isa gurin.

“Zo ki zauna Iyami”

Sai a lokacin ta ji kuzari ta cira kafarta ta taka har ta isa gurin ta zauna jiki a sanyeye tana kallonsa. Ajiyar zuciya ya sauke kusan sai uku sannan ya kai hannunsa ya bude bedside drawer ya dauko wata yar karamar jaka ya bude ya dauko wasu takardu ya mika mata.

“Wannan takardun gidana ne da yake a Samaru, na saka lawyer na ya canja komai daga sunana zuwa naki, na kafa shaida da lawyer na kuma ta bangarenki na yi magana da Bappa shi ma ne shaida domin a gabansa aka yi komai, sai dai na bukaci kar ya fada miki saboda ina son ya zama ni zan fara sanar da ke, saboda haka yanzu gidana dake Samaru mallakinki ne halak malak...”

Ta mika hannu biyu ta karba cikin yanayin mamaki da faduwar gaba, ta kasa godiya haka kuma ta kasa jin farinciki ko kishiyarsa. Wata karamar Envelop ya dauko a cikin jakar ya mika mata.

“Wannan Cheque ne na Naira miliyan Ashiri, ina son ki yi amfani da kudin ta hanyar da ya dace ki yi kasuwanci ki rike kanka dan Allah”

Ta karba idonta na cika da hawaye.

“Wannan duk na minene?”

Yayi shiru ya kasa ce mata komai, sai ya sake saka hannunsa ya dauko wani envelop din ya mika mata.

“Ki yi hakuri Iyami, ina jin rashin natsuwa da faduwar gaba da tashin hankali a duk lokacin da girkinki ya zagayo, idan na tuna kina a cikin gidana karkashin kulawata sai na ji kamar zan mutu, na yi ta daurewa ina ganin kamar abun nan zai wuce amman ban ga alamar haka ba, a kullum sai kara yin gaba abun yake, akan hakan na yanke hukuncin yin abun da zai zame mana mafita gudun kar na cutar da ke, domin idan muka daure a haka ban san a gaba yadda zama zai kasance ba”

Kasa mika hannu ta yi ta karba kuma ta kasa ta kasa cewa komai, ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa, hawaye kuma suka ce mata ga rabarsu. Ganin haka ya saka ya aje mata takardar a saman takardun da ya mika mata.
Chapter 3 · 0% Book details